Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151
Published: 19th, October 2025 GMT
151-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda Imam Ali (a) ya daga murya yana cewa {Na rantse da Ubangijin Kaaba na rabauta} a lokacinda ya ji sarar Abdurrahman dan Muljam ya shiga cikin kansa, sai ya fadi a kasa a wurin sallarsa.
Daga nan sai mutane suka yi ta fitowa daga gidajensu zuwa masallaci, daga inda suka ji sautin Amirul muminina (a). Yana daga cikin mutane na farko da suka isa kansa, yayansa da danginsa, daga ciki akwai Ja’adatu dan Hubairah Almkhzumi, mahaifiyarsa yar’uwan Amirul muminina wacce ake kira Ummu Hani yar Abutalib, sannan mun ji yadda Imam (a) ya fada masu cewa an kama Ibnu Muljam a kofar Kinda kamar yadda amirulmuminina ya fada masu, kuma Mughira dan Naufal dan Haritha ne ya kama shi ya daka shi da kasa sannan suka daure shi suka kawo gaban Imam Alhassan (a).
Har’ila yau mun ji yadda Imam (a) ya bukaci Imam Alhassan (a) ya ji tausayin Ibn Muljam a lokacinda yake tsare da shi, ya ciyar da shi abinda yake ci ya kuma sahayar da shi abinda yake sha.
Sannan idan ya yi masa kisasi, kada yayi Muthla da shi, dan manzon All..(s) ya hana a yi muthla ko da da kare mai cizo ko cutarwa ne ne. Mun ji yadda aka maida shi gida, ya gamu da yayansa mata da matansa suna kuka, sannan a lokacinda aka kawo jama’ar likitoci mafi kwarewa daga cikinsu watu Atheer dan Amru Assakuni ya bukaci a kawo masa jijiyar akuya mai zabi, aka kawo ya shigar da shi cikin raunin da takobin ya ji masa ciwa sai ga shi jijiyar ta fito da farifarin kwakwalwar Imam (a).
Sai Atheer assakuni ya ce masa ya yi wasiyansa don ba zai rayu ba. Sannan mun ji yadda guban da ke jikin takobin ya shiga jininsa (a) sannan ya canza launin fuskarsa zuwa fatsi-fasti ko yello.
Daga nan Imam (a) ya runkumi dansa Imam Alhassan (a) yana bashi hukuri yana fada masa cewa, daga yau kuma babu bakinciki ko fargaba ga babanka, a yau zai hadu da kakansa Muhammadul Mustafah, a yau zai hadu da kakakansa Khadijatul Kubra a yau zai hadu da mahaifiyarsa Fatimah Azzaha(a).
Sannan ya ci gaba da yin zikri da addu’o’i, daga ciki yana cewa: {Ya Ubangiji ka hada ni da annabawa da wasiyai, ka bani mafi daukakar darajojin Aljanna.}
Ana cikin wannan halin sai Imam (a) ya suma, sai Imam Al-Hassan (a) yana ta kuka a kansa, sai hawayensa suka diga a kan fuskansa, sai ya ya farfado. Ya ganshi a kansa yana kuka. Sai yace masa: {Ya dana! Menene wannan kokar,? Babu tsoro babu fargaba ga mahaifinka daga yau. Ya da na! kada ka yi kuka, za’a kasheka da guba, sannan za’a kashe dan’uwanka Alhusain da takobi}.
Daga nan sai Imam Amirulmuminina (a) y afara yin wasiyya ga yayansa da halaye masu kyau, yana basu misalai masu kyau, yana basu darussa na halaye masu kyau, da farko ya fara yin wasiyya da nasihohi ga yayansa Al-Hasan da Al-Husain(a). sannan ga sauran yayansa sai kuma sauran Musulmi.
Daga cikin wasiyyansa garesu yana cewa:
{Ina maku wasiyya (ku biyu) da tsoron Allah da kuma kada ku nemi duniya ko ta nemeku, kuma kada ku yi bakinciki da wani abu da ya kubuce maku daga gareta, Kuma ku fadi gaskiya, kuma ku yi aiki don samun lada, kuma ku kasashen mai husuma ga azzalumi, kuma mataimaki ga wanda aka zalunta.
Ina maku wasiyya, da dukkan yaya na da iyalai na da duk wannan wasiyar ta kai gareshi, da tsoron All…da tsara al-amarinku, da kyautata tsakaninsu, To, Lalle naji kakanku manzon Allah (s) yana cewa: Kyautata tsakanin (musulmi) ya dukkan salloli da azumi.
Ina hadaku da Allah, ina hadaku da Allah cikin kula da marayu ! Kada ku hanasu kyaututtukanku, kada ku yarda su wahala a gabanku.
Inan hadaku da Allah ina hadaku da Allah dangane da makobtanku, su wasiyyan annabinku ne, bai gushe bay ana wasiya da a kula da su, har muka zaci cewa Lalle sai gadar da su.
Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah dangane da Alkur’ani ! Kada waninku ya rikaku aiki da shi. Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah dangane da Sallah ! don ita ginshikin addininku ne.
Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah dangane dakin Ubangijinku. Kada ya wofinta daga gareku matukar kuna raye, don idan an barshi to ba za’a Allah ba zai dubeku da karamcinsa da kuma rahama ba.
Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah dangane jihadi da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku a kan tafarkin Allah.!
Inan horonku da da sada zumunci da musanyar kyaututtuka, kuma ina gargadinku da bada baya a tsakaninkug da kuma katse zumunci a tsakaninku, kada ku daina umurni da kekyawar ayyuka da kuma hana daga munanan ayyuka, (idan baku yi haka ba) sai a dora munanan mutane daga cikinku a kanku, ko da zababbu daga cikinku sun roki Allah ba za’a amsa adda’arku ba}.
.Sannan sai ya juya zuwa iyalan gidansa yana cewa:
{Ya ku yayan Abdulmuttalib, kada in sameku, kuna kutsawa cikin jinanen mutane musulmi ..kuma cewa: An kashe Amirulmuminina. Ku saurara, kada ku kashe saboda ni , sai wanda ya kashe ni.
Ku jira ku gani, idan na mutu sanadiyyar wannan duka da ya yi mani. Ku kashe shi da doka guda, da duka guda da yayi mani. Kada ku yi muthla da mutumin, Don lalle ni na ji manzon All..(s) yana cewa: Ina gargadinku da yin muthla ko da da kare mai cizo ne)}…
Daga nan sai ya fara yin wasiyya dangane da addini ga dansa Imam Alhassan(a), shi kadai, inda yake cewa:
{Ya da na! Ina maka wasiyya da tsoron Allah, da tsaida Sallah a cikin lokacinta, da bayar da zakka a lokacin bada shi, da kyautata Alwala don lalle babu sallah sai da tsarki, kuma ba’a karbi sallar wanda yake hana zakka, ina maka wasiyya da gafarwa wanda ya cutar da kai, da hadiye fushi, da sada zumunci, da hakuri ga wanda ya jahilceka, da karatun addini, da tabbata a cikin al-amarin addini, da sabo da karatun Alkur’ani mai girma, da kyautata makobtaka, da umurnin da kyawawan ayyuka, da hani daga munkari, da kauracewa zunubbai gaba daya, a cikin duk inda aka sabawa Allah cikinsa}…
Sannan a ranar 20 ga watan Ramadan, mutane sun yi cincirindo a kofar gidan Imam (a) suna neman izinin ziyartassa. Sai aka yi wa kowa da kowa izinin shiga. A lokacinda suka shigo suka zauna, sai ya juya wajensu yana cewa:
{Ku tambayeni kafin ku rasa ni, kuma ku sassauta tambayoyinku don abinda ya sami limaminku} Sai mutanen sun ji tausayinsa a yawan tambayoyi saboda halin da yake ciki na zafin Rauni da yake fama da shi.
Daga nan sai ya gabatar da dansa Imam Al-Hassan (a) a matsayin magajinsa, a lokacinda ya ga cewa tafirasa ko mutuwarsa ta karatu, Ko kuma saduwarsa da Ubangijinsa ta karato, sai ya gabatar da Imam Hassan (a) a matsayin Khalifansa a bayansa, don al-umma ta koma gareshi a bayansa, a cikin dukkan al-amuranta.
Malaman shi’a basu yi sabani kan hakan ya faru ba. Thiqatul Islam Alkulaini, daga daga cikin manya-manyan malaman Imamiyyah, a cikin karni na biyu bayan hijira. Kan cewa Amirulmuminina (a) ya yi wasiya wasiyya ga dansa Imam Alhassan (a) kuma ya kafa shaidar hakan da Imam Al-Hussain (a) da Muhammad (dan hanafiyya) da dukkan yayansa, da shuwagabannin shi’a a lokacin, da iyalan gidansa. Sannan ya mika masa littafain da makamai, sannan ya ce masa:
{Ya da na! Manzon Allah (s) ya umurce ni, da in yi wasiyya gareka, kuma in baka littafaina da makamaina, Kumar yadda manzon Allah (s) ya yi sanya ni wasiyyinsa, ya mika mani littafansa, da makamansa, kuma ya umurce ni da in umrceka kan cewa idan mutuwa ta zo maka ka mika su ga dan’uwanka Husain(a)}
A wani hadisin yana cewa {Ya dana! kai ne waliyyin jinina, idan ka yi afwa, gareka, idan kuma zaka kashe to duka guda a matsayin duka guda}.
Amma wasu daga cikin malaman sunnan sun tafi a kan cewa Amirulmuminin (a) bai yi wasiyya ga dansa Imam Alhassan(a) ba, suna kafa hujja da hadisin da Shu’aibu dan Maimuna Alwasity ya ruwaito na cewa Aliyu(a), an ce masa , ba zaka Sanya khalifa ba? Sai yace: idan Allah yana son Alkhairi ga al-umma zai hana kansu a kan mafi alkhairinsu.
Wannan hadisin yana daga cikin hadisan da Shu’aibu ya kirkiro, kuma yana daga cikin “Manakirinsa” wato hadisan daga aka ki karba daga gare shi kamar yadda ibn Hajar Al-Askalani ya yake fada.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156
156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.
Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.
Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).
A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.
Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ® ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.
Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).
Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.
Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.
:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..
Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.
Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farillu ba da sonsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci