Leadership News Hausa:
2025-10-19@20:03:36 GMT

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Published: 19th, October 2025 GMT

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

Kazalika, ana bukatar da namiji ya sha ruwa akalla kimanin lita 3.7 a kullum, mata kuma su sha lita 2.7 a kowace rana. A nan, ana auna yawan ruwan da mutum yake sha ne, wanda ya hada da shayi ko lemo ko kuma jus da sauran makamantansu.

 

Idan kuma zallan ruwan mutum zai sha kamar ‘Pure Water’, ana so namiji ya sha kamar leda bakwai da rabi, mace ita kuma ta sha kamar leda biyar da rabi.

 

Amma a nan, ana magana ne a kan lafiyayyu, wadanda kuma ba su da cikakkiyar lafiya, kamar masu ciwon zuciya ko koda, bai kamata su sha wannan adadi ba.

 

Har ila yau, rashin yawan shan ruwa yadda ya kamata; zai iya jawo wa mutum illoli daban daban. Na farko, rashin shan ruwa a-kai-a-kai zai iya haddasa wa mutum kamuwa da cutar sanyin fitsari (Urinary track infection).

 

Na biyu kuma, zai iya haddasa wa mutum cutar tsakuwar koda (Kidney stones), a nan wasu abubuwa ne ke dunkulewa su ki fita, sai su zama kamar dutse, wanda hakan ke sanya wa mutum ya rika yin ciwon ciki mai zafi tare da yin fitsarin jini da sauran makamatantan wasu matsaloli da dama.

 

Na uku kuma, rashin yawan shan ruwa na iya jawo rashin iya yin bayan gida, wanda hakan kan kawo matsalar basir da sauran makamantansu, sakamakon sakaci da yawan shan ruwa.

 

Don haka, ya zama wajibi mu kula da shan shan ruwa a-kai-a-kai yadda kuma ya kamata, domin kaucewa haduwa da ire-iren wadannan cututtuka, kamar yadda a koda-yaushe likitoci suke kokarin fadakarwa tare da jan hankalinmu.

 

Lafiya uwar jiki, babu mai fushi da ke, sannan idan kunne ya ji; Hausawa suka ce, wai gangar jiki ta tsira. Don haka, a daure a kula sosai da shan ruwa, saboda irin matukar amfanin da yake da shi.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kiwon Lafiya Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa October 11, 2025 Kiwon Lafiya Ko Kin San… Amfanin Sabaya Ga Mace? October 5, 2025 Kiwon Lafiya Matsalar Tasgadewar Kashin Baya September 27, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yawan shan ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa

 

Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.

 

Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.

 

Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen yaki da rashin tsaro, talauci da rarrabuwa. Ya gargaɗi malamai da al’umma da su guji amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ƙarya da haifar da fitina.

 

Sarkin Musulmi ya jaddada cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata ne kawai idan aka samu haɗin kai na gaskiya tsakanin sassa daban-daban na al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.

 

A jawabinsu na haɗin gwiwa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi sun bayyana cewa son kai, rarrabuwa, da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo rashin tsaro a Arewa. Sun ce lokaci ya yi da shugabannin addini, gargajiya da siyasa za su buɗe tattaunawa mai fa’ida tare da yin aiki tare domin kawo ƙarshen rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki.

 

Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar na Jihar Zamfara, Sanata Shehu Buba na Jihar Bauchi, da Honourable Alhassan Ado Doguwa na Jihar Kano, sun yaba da wannan taro suna mai cewa lokaci yayi da za a ɗauki mataki na haɗin kai domin ceto yankin Arewa daga ƙalubale.

 

Sanata Yari ya ce rashin tsaro na ci gaba da ƙaruwa ne saboda rashin daidaito da ƙarancin damar tattalin arziki, yayin da Sanata Buba ya jaddada muhimmancin ƙarfafa matasa da aiwatar da gyare-gyaren zamantakewa bisa ka’idojin Musulunci.

 

Honourable Doguwa, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai na Arewa (Northern Caucus), ya tabbatar da goyon bayan majalisa ga sakamakon taron, tare da alkawarin haɗa hannu da hukumomi da shugabanni domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.

 

A ƙarshen taron, mahalarta sun amince da kafa Cibiyar Jagorancin Addinin Musulunci ta Ƙasa (National Islamic Leadership Forum), domin haɗa malamai, shugabanni da masu tsara manufofi a ƙarƙashin dandalin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.

 

COV: Shettima Abdullahi

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Talauci ne babban maƙiyin ɗan Adam — Atiku
  • Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?
  • Gwamnati ta ɗauki matakin rage shan gishiri a Nijeriya
  • Yadda Ake Alkaki
  • Mahukunta sun kai samame wani gidan shan Shisha a Kano
  • Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
  • Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho
  • Jihar Jigawa Ta Dukufa Wajen Gina Magudanan Ruwa Domin Kaucewa Ambaliya
  • Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa