Gwamnatin Jigawa Ta Jinjinawa UNICEF Da EU Bisa Gudunmawarsu A Fannin Ilimi
Published: 18th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba wa Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Tarayyar Turai (EU) bisa gudunmawar su wajen inganta harkar ilimi a fadin jihar.
Shugaban Hukumar Ilimin Firamare (SUBEB) na jihar, Farfesa Haruna Musa, ne ya bayyana hakan a lokacin bude taron bitar kwana uku na karkashin Shirin Ayyukan Sashen Ilimi na a Jihar, wato Local Education Sector Operations Plan (LESOP) da aka gudanar a Dutse.
Ya bayyana cewa UNICEF da Tarayyar Turai na tallafa wa gwamnatin jihar ta hanyar Shirin Inganta Ilimi da Karfafa Matasa da Shirin Ayyukan Sashen Ilimi na jihar Jigawa inda ake sake dubawa da tsara sabbin tsare-tsaren aiki da za su zama jagora wajen inganta harkar ilimi a jihar.
A cewarsa, wannan shiri zai mai da hankali kan magance matsalolin da suka addabi tsarin ilimi, musamman matsalar karancin sakamako mai kyau a fannin koyo da kuma yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta.
A nasa jawabin, Manajan Ilimi na ofishin UNICEF na Kano, Mista Michael Banda, ya sake jaddada kudirin UNICEF din na ci gaba da hada kai da gwamnatin Jigawa wajen farfado da fannin ilimin firamare. Ya ce bitar LESOP muhimmin mataki ne wajen karfafa tsarin shiryawa da aiwatar da manufofin ilimi a jihar.
Mista Banda ya ce sake duba LESOP na nuna cewa gwamnatin jihar tana da niyyar bin sahihin tsarin yanke shawara bisa hujja, gaskiya da kuma hada al’umma, wadanda su ne muhimman ginshikan sauya tsarin ilimi a matakin ƙananan hukumomi.
Sai dai ya nuna damuwa cewa duk da ci gaban da aka samu, har yanzu yara da dama a Jigawa na fuskantar matsaloli wajen samun ingantaccen ilimi saboda talauci, aikatau, aurar da kananan yara ko kuma nisan makaranta daga gida. Ya ce tsarin LESOP zai ba da damar gano wadannan matsaloli a kowane yanki da kuma tsara mafita da suka dace da al’ummar yankin.
Ya kuma bayyana cewa rashin isassun kudade na daga cikin manyan kalubalen da ke hana cimma burin ilimi, tare da bukatar tabbatar da gaskiya wajen amfani da kudaden da aka ware. Ya bukaci gwamnati da ta nemi hanyoyin kirkire-kirkire wajen samar da kudade da kuma tabbatar da cewa kudaden da aka ware don ilimi sun isa makarantu akan lokaci.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa UNICEF
এছাড়াও পড়ুন:
Yajin Aikin ASUU: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki, Za Ta Gana Da Ministan Ilimi
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn October 17, 2025
Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025
Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025