Cibiyar Tsare-tsaren Harkokin Ilimi da Gudanarwa ta Kasa (NIEPA) ta yaba da kokarin Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) wajen kare hakkokin yara na samun ilimi a Najeriya.

Darakta Janar na Cibiyar, Dakta David Shofoyeke ne ya bayyana hakan yayin bude taron horaswa na kwanaki uku ga masu gudanar da shirye-shiryen ilimin yankuna (LESOP) a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Dakta Shofoyeke, wanda Dakta Grace Omiyale Babbar Malamar Horaswa da Bincike a Cibiyar ta wakilta, ya tabbatar da cewa cibiyar tana da cikakken kudiri na sauya tsarin ilimi a Najeriya.

Ya bayyana cewa, samar da cikakken tsarin ilimi na jiha da kuma tsarin aiwatar da shirye-shiryen ilimi na jihohi yana taimakawa jihohi wajen tsara burinsu a fannin ilimi.

Ya ce, ta wannan hanya ce jihohi za su iya aiwatar da shirye-shiryen ilimi da suka dace da manufofi da albarkatun da ake da su.

Dakta David ya kara da cewa UNICEF tana bayar da taimakon fasaha wajen shirya wadannan takardu a jihohi takwas.

A cewar NIEPA, UNICEF ta shimfida tubalin shirye-shiryen ilimi bisa hujja, masu daidaito tsakanin jinsi, da fama da nakasassu, tare da karfin jurewa rikice-rikice da sauyin yanayi a Najeriya.

Dakta David ya yaba wa Gwamnatin Jihar Jigawa bisa jajircewarta wajen sauya tsarin ilimi ta hanyar amfani da bayanai wajen yanke shawara.

 

Shi ma babban  sakatare na ma’aikatar ilimin gaba da sakandare, da fasaha da kimiyya ta jihar, Alhaji Muhammad Dahiru, ya yaba wa abokan hulɗa bisa shawarwarin  da suke bayarwa.

A cewarsa, Gwamnatin Jihar Jigawa tana da cikakken kudiri na yin aiki tare da abokan hulda domin samar da ingancin ilimi a jihar.

Dahiru ya ce daya daga cikin ginshikan gwamnatin Namadi shi ne sauya tsarin ilimi.

Hukumar UNICEF tare da hadin gwiwar Tarayyar Turai (EU), suna tallafa wa Jihar Jigawa wajen nazarin sabon tsarin dabarun ilimin jihar.

Wannan aikin yana gudana ne karkashin shirin hadin gwiwa na UNICEF da EU kan ilimi da karfafa matasa.

 

Usman Mohammed Zaria

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa shirye shiryen ilimi Jihar Jigawa tsarin ilimi

এছাড়াও পড়ুন:

Kudurorin Kafa Hukumomi 3 Sun Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dokokin Jihar Jigawa

Wasu kudurori guda 3 da ke dauke da bukatun kafa wasu hukumomi 3 sun samu karatu na biyu a zauren majalaisar dokokin jihar Jigawa.

Kudurorin guda 3 sun hada da na kafa Hukumar Samar da Hanyoyin Mota a yankunan karkara, da na kafa Hukumar Samar da Kudade Domin Ayyukan Hanyoyin Mota a yankunan karkara da Kuma na Hukumar Bunkasa Kwazon Malamai ta jihar Jigawa.

A lokacin ya ke gabatar da kudurorin domin neman goyon baya kan bukatar kafa hukumar bunkasa kwazon malamai, mataimakin shugaban masu rinjaye na majlaisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce gwamnatin jihar na da nufin inganta aikin koyarwa ta hanyar kafa hukumar da za ta rinka horas da malamai akai akai.

Da su ke tattaunawa kan wannan batu, wakilan mazabar Kanya Babba da na Fagam da na Sule Tankarar da na Guri, sun lura cewa kafa wannan hukumar zai maye gurbin ayyukan kwalejin horas da malamai da aka rushe a can baya, abin da zai kawo ingancin harkonin koyo da koyarwa a halin yanzu.

Kazalika da ya ke gabatar da kudurin neman goyon baya kan batun kafa hukuma da kuma asusun samar da hanyoyin mota a yankunan karkara, mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhaji Sani Sale Zaburan ya ce daukar wannan mataki zai karfafa yunkurin gwamnatin jihar na inganta harkokin sufuri ga jama’ar karkara.

Da su ke bada gudummawa kan wannan batu, wakilin mazabar Gwaram da na Kiri Kasamma da na Guri da kuma wakilin mazabar Fagam sun bayyana kudurorin biyu a matsayin wata alama da ke nuni da kyakkyawan kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen samar da hanyoyin mota ga yankunan karkara, inda fiye da kaso 60 na jama’ar jihar ke zaune.

Bayan samun goyon baya da gagarumin rinjaye sai aka yiwa kudurorin 3 karatu na 2, daga nan kuma shugaban majalisar dokokin jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya mika kudurori 2 na hanyoyin mota a yankunan karkara ga kwamatin muhalli, yayin da kudurin kafa hukumar inganta kwazon malamai ya je ga kwamatin ilimi mai zurfi da na ilimi matakin farko, wanda dukkan su aka bai wa makonni 4 domin mika rahotannin su.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Gombe ya ƙaddamar da shirin tallafa wa karatun yara mata
  • Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 6 Don Bunkasa Noma, Ilimi Da Kasuwanci
  • Jihar Jigawa Ta Dukufa Wajen Gina Magudanan Ruwa Domin Kaucewa Ambaliya
  • Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF
  • Kaso 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF
  • Ministan Yada Labarai Ya Bayyana Jihar Borno A Matsayin Mafi Juriya A Najeriya
  • Kaso 92 cikin 100 na ’yan Najeriya ba su iya wanke hannu ba — UNICEF
  • An Bukaci An Bukaci Asusun JICHIMA Ya Fadada Hanyoyin Samun Kudade Baya Ga Gwamnatin Jigawa
  • Kudurorin Kafa Hukumomi 3 Sun Tsallake Karatu Na 2 A Majalisar Dokokin Jihar Jigawa