Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Masana Iran da suka yi shahada a lokacin yaki babu laifin da suka aikata ban da hidima ga al’ummarsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka kan shirun da masu da’awar kare hakkin bil’adama da zaman lafiya da tsaro suka yi dangane da laifukan gwamnatin ‘yan sahayoniyya, yana mai cewa: Masana kimiyyar Iran da suka yi shahada ba su aikata komai ba face hidimar al’ummar Iran a fadin duniya, amma gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe su.

Masoud Pezeshkian ya halarci bikin karrama masana kimiyya da suka yi shahada a tsangayar koyar da fasahar nukiliya ta jami’ar Shahid Beheshti a safiyar ranar Talata, inda ya jinjinawa hotunan malaman kimiyya da suka yi shahada a cikin jami’ar tare da sanya hannu kan littafin bakin da suka halarta.

Pezeshkian ya kara da cewa: “Shi da kansa ya yi hulda da wadannan masoya saboda matsayinsu da kuma nauyin da ke wuyansu, ba su aikata wani laifi ba face sani da kuma iya yanke shawarar samarwa kasarsu fasahar zamani.”

Shugaban ya soki lamirin masu ikirarin kare dimokuradiyya, ‘yancin dan Adam, zaman lafiya da tsaro, yana mai cewa: “Wannan da’awar ba komai ba ce illa karya, wadanda aka rataye hotunansu a nan ba su yi komai ba illa hidimar al’ummar Iran da kokarin kare kasar daga cin zarafi na zalunci a duniya, amma gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe su.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: A Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe August 13, 2025 Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe August 13, 2025 Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin August 13, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida  August 13, 2025 Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya kawo ziyara Tehran bayan yakin kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa JMI.

Gwamnatin JMI dai tana shakkan ma’amatar da hukumar, inda take ganin babu gaskiya a cikin mu’amalarta da ita, da farko saboda tabbacin cewa hukumar tana bawa makiyanta, musamman HKI wasu bayanai wadanda ta karba a wajenta dangane da shirinta na makamashin nukliya, inda HKI ta sami damar kashe masana fasahar nukliyar kasar da dama a cikin shekarun da suka gabata.

Banda haka hukumar ta IAEA ta tara gwamnoninta suka kada kuri’ar rashin amincewa da shirin makamashin nukliya da rana guda sai HKI ta kawowa Iran hari. Wannan ya nuna kamar akwai aiki tare tsakanin hukumar da HKI.

Wannan matsalolin da kuma debe kauna kan cewa hukumar zata yiwa Iran adalaci majalisar dokokin kasar Iran ta fidda doka wacce ta jingine mu’amala da hukumar.

A wannan ziyarar dai bangarorin biyu zasu fidda sabbin hanyoyin mu’amala da hukumar tare da lura da korafe-korafen JMI a ayyukan hukumar a yanzu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tehran: Kasar Lebanon Tana Da yencin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 A Mali An Kama Sojoji Fiye da 40 Saboda Zargi da Kokarin Juyin Mulki August 11, 2025 Larijani Ya Gana Da Firai ministan Kasar Iraki A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza August 11, 2025 Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza August 11, 2025 Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza August 11, 2025 Iran: Ba a yanke wani abu game da tattaunawa da Washington ba August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: A Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
  • Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe
  • Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka
  • Larijani Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace
  • Babban Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Ce: ‘Yan Gwagwarmaya Sun San Abubuwan Da Suka Dace
  • Iran ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa ‘yan jarida a Gaza
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza
  • Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza