Jakadan Iran a Saudiyya: Kasashen biyu na tuntubar juna a kan muhimman batutuwa na yankin
Published: 17th, August 2025 GMT
Jakadan Iran a Saudiyya Alireza Enayati ya tabbatar da ci gaba da tuntubar juna tsakanin babban hafsan hafsoshin sojin Iran da ministan tsaron Saudiyya.
A wata hira da kamfanin dillancin labarai na IRNA Alireza Enayati ya yi nuni da cewa, Saudiyya na kallon alakar ta da Iran a matsayin alaka mai matukar muhimamnci, kamar yadda ita ma Iran din take Kallon wannan alaka tsakaninta da Saudiyya.
Inda ya kara da cewa “Mun ga irin goyon bayan da Saudiyya ta bayar kan shawarwarin nukiliyar da aka yi a baya-bayan nan, wanda hakan abin yabawa ne.”
Har ila yau, ya yi ishara da cewa, magance da kuma kula da al’amurran da suka shafi yankin gabas ta tsakiya abu ne mai yiyuwa idan Iran da Saudiyya suka hadin gwiwa suka yi aiki tare kafada da kafada, yana mai cewa “sake dawo da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakanin Iran da Saudiyya wani lamari ne mai matukar muhimmanci.”
Jakadan na Iran ya ce kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta mai cikakken iko, na iya zama wani abin da zai fi muhimmanci da kuma mayar da hankali a kansa a cikin ayyukan hadin gwiwa tsakanin Iran da Saudiyya.
Kimanin wata guda da ya gabata kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya bayyana cewa, tattaunawar da aka yi tsakanin minista Abbas Araqchi da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ta yi armashi matuka, kuma za ta amfani dukkanin kasashen biyu da ma sauran kasashen yanin gabas ta tsakiya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: A cikin sa’o’i 24 Mutane da dama sun yi shahada daruruwa sun jikkata a hare-haren Isra’ila August 17, 2025 An kashe mutane 17 a harin da dakarun RSF suka kai a El Fasher, Sudan August 17, 2025 Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Yi Allah Wadai Da Kalaman Netanyahu Kan Mamaye Yankunan Kasashe August 16, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Furucin Jami’ar Kotun ICJ Na Goyon Bayan Isra’ila August 16, 2025 Araqchi Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een August 16, 2025 Hamas Ta Yi Allah Wadai Da Sanya Ta Cikin Jerin Sunayen Bakin Littafin MDD August 16, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Tafka Muggan Ayyukansu A Yankin Zirin Gaza August 16, 2025 Mataimakiyar Shugaban Kotun ICJ Ta Ce Tana Goyon Bayan HKI August 16, 2025 Burtaniya Zata Gurfanar Da mutane 60 Saboda Goyon Bayan Falasdinawa August 16, 2025 Qalibof: Dole Ne Musulmi Su Hada kai Don Matsin Lamba Ga HKI August 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi tir da matakin Australiya na alakanta IRGC, da mai tallafawa ta’addanci
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,”
“Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis.
Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah wadai da ita da kuma rashin adalci.
“Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki wannan matakin a matsayin haramtacciyar hanya.”
“Wannan matakin rashin da’a da babban kuskure da gwamnatin Australiya ta aikata bisa zargin da ba shi da tushe da hukumomin tsaro na gwamnatin Saihoyoniya suka kirkira,” in ji ta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ramaphosa ya soki kalaman Trump na cewa ba zai gayyaci shi a taron G20 November 27, 2025 ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau November 27, 2025 Faransa, Jamus, Italiya, da Burtaniya sun yi tir da “karuwar rikici” a yammacin kogon jodan November 27, 2025 Rasha A Shirye Take Ta Taimaka Wa Najeriya A Fada Da Ta’addanci November 27, 2025 Palasdinawa Sun Karbi Gawawwakin Shahidai 15 Daga ‘Yan Mamaya November 27, 2025 Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon Dake Takawa Makiya Birki November 27, 2025 Najeriya: Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini Shehu Dahiru Bauchi Rasuwa November 27, 2025 An Zabi Iran A Cikin Majalisar Zartarwa Ta Hukumar Yaki Da Makamai Masu Guba Ta Duniya CWC November 27, 2025 HKI Tana Amfani Da Tsagaita Wuta A Gaza Don Sake Shata Kan Iyakokin Yankin November 27, 2025 Yawan Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Na Karuwa Saboka Keta Yarjeniyar Tsagaita Wuta November 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci