An dawo da malamai 103 da aka kora daga aiki a Zamfara
Published: 20th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Zamfara ta dawo da wasu malamai 103 da aka kora a baya sakamakon binciken tantance ma’aikata tare da biyan su bashin albashin watanni bakwai.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Malam Wadatau Madawaki, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon sake nazarin tantance malaman da ma’aikatars ta gudanar.
Madawaki ya ce an cire sunayen waɗannan malamai ne bisa kuskure “ko kuma ta mantuwa” a lokacin gudanar da tantancewar.
“Bayan an kammala tantancewar, mun gano cewa malamai 103 cikin waɗanda aka cire sunayensu an yi kuskure. Sun cancanci kasancewa cikin jerin malamai da aka tabbatar da su,” in ji shi.
Juyin mulki: Ana zargin tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin sojojin Najeriya NAJERIYA A YAU: Shin Ya Kamata A Saki Shugaban IPOB Nnamdi Kanu?Kwamishinan ya ce bayan gano kuskuren, ma’aikatar ta rubuta wa Gwamna Dauda Lawal takarda tana neman amincewarsa a dawo da su da kuma a biya su albashin da aka dakatar.
“Daga watan Janairu zuwa Yuli 2025, Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta rubuta wa Mai Girma Gwamna tana neman ya amince a dawo da waɗannan malamai 103.
“Alhamdulillah, Mai Girma Gwamna ya amince a dawo da su tare da biyan su bashin albashin watan Janairu zuwa Yuli 2025,” in ji Madawaki.
Kwamishinan ya ƙara da cewa gyare-gyaren da ake yi a ɓangaren ilimi na cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na tsaftace tsarin aiki da tabbatar da inganci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun rasu, 13 sun jikkata a hatsarin mota a Kogi
Aƙalla mutum shida ne suka rasu, yayin da wasu 13 suka jikkata, bayan wata bas ɗauke da nakasassu ta yi hatsari a kan hanyar Lokoja zuwa Okene.
Waɗanda abin ya shafa suna komawa Okene ne bayan halartar bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta 2025 a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Lokoja.
Jirgin fadar shugaban ƙasa ya ƙi sayuwa wata 5 bayan saka shi a kasuwa ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a YobeAn garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci daban-daban a jihar, inda suke ci gaba da samun kulawa.
Kwamishinan Harkokin Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya ce wannan hatsari abun baƙin ciki ne ga gwamnati da jama’a.
Ya ce Gwamna Ahmed Usman Ododo ya umarci gwamnatin jihar da ta biya dukkanin kuɗin maganin waɗanda suka jikkata kuma ta tura jami’ai zuwa asibitoci don tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Fanwo ya ce: “Gwamnatin Jihar Kogi tana jimami sosai tare da iyalan waɗanda suka rasu guda shida, kuma za ta tallafa musu.”