Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)
Published: 19th, October 2025 GMT
Maganar mace tana iya gina aure ko rusa shi. Idan kika yi amfani da harshenki wajen zagi, tsinuwa, da cin zarafi, kin riga kin fara gina bango tsakaninki da mijinki. Kuma wannan kuskure ne da ake yin kuka a kai daga baya.
7. Barin kanki ba kula da kanki
Mace da ta daina kula da tsafta, kamshi, da kwalliya a cikin gida tana sa mijinta ya fara daina ganin armashinta, ki kula, mijinki zai iya samun abin da ke burge shi a waje, amma bai kamata ya rasa hakan a wurinki ba.
8. Rashin zama mai hakuri
Aure ba kyakkyawa ba ne kadai, akwai gwaji, akwai jarabawa. Idan mace ba ta da hakuri, tana iya ruguza gidan aurenta da kanta. Hakuri shi ne kashin bayan nasarar kowanne aure.
9. Kin sanin darajar mijin ki
Idan kika daina nuna masa cewa ke kina godiya da shi, kina ganin komai ya zama dole, to kin fara ruguzawa. Miji yana bukatar a yaba masa, a nuna masa daraja. Idan kika yi sakaci, sai ya fara neman inda zai sami hakan.
10. Kin guje wa shawarar Allah
Dukkan kuskuren da aka ambata a sama ya samo asali daga barin koyarwar addini. Idan mace ta tsaya da gaskiya, ta kiyaye umarnin Allah da na Manzonsa, ba za ta aikata wadannan kurakurai ba. Amma idan ta bar su, aure na zama cike da nadama da bakin ciki.
Karshen magana:
Kuskure a aure na iya zama karami a idon mace, amma yana iya zama babban abu da zai rusa ginin da ta dauki shekaru tana ginawa. Kada ki bari wata rana ki ce “Da na sani.” Saboda lokacin da kalmar nan ta fito, lallai nadama ta riga ta mamaye zuciyarki.
Ki tsaya, ki gyara, ki kasance mace ta daban mace mai daraja a idon mijinta.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An Fara Yi Wa Yara Miliyan 1.6 Rigakafi A Taraba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ƴansanda Sun Kama Gungun Masu Sojan Gona Suna Aikata Laifuka A Kano October 18, 2025
Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna October 18, 2025
Labarai Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro October 18, 2025