Chen Xiaoguang ya bayyana cewa, dabarun da aka saba amfani da su na yaki da sauro suna da tasgaro. Ya ce tarko da gidan sauro na kama sauro ne marasa shan jini, yayin da tsarin kama sauro cikin mazubi da ruwa, ke kama sauro masu jan jini da yin kwai.

 

Ya kara da cewa, abun da suka kirkiro na’ura ce dake gudanar da ayyuka biyu a lokacin da ake ciki, kuma tana da matukar inganci wajen sa ido da bibiyar sauro.

(Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko.

A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13.

Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana.

Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar ’yan sanda, jami’an DSS, da kuma sojoji.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa suna matuƙar farin ciki da wannan nasara, musamman ganin cewa mutanen sun kwashe watanni a hannun ’yan bindiga cikin tsananin wahala.

Hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere, tare da inganta matakan tsaro a yankin don kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.

“Za mu ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi don tabbatar da cewa babu wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da za ta samu mafaka a Kaduna,” in ji DSP Mansir Hassan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22
  • Neman Kudi Ne Ya Kawo Ni Masana’antar Kannywood Ba Fadakarwa Ba – Khadija Muhammad 
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho