Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza

Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar.

A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu kira ga mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da wannan gurguwar tunaninsu maras kan gado.

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawan Tekun Pasha Jasim Muhammad Al-Badaiwi ya jaddada cewa; matakin da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka na mamaye Zirin Gaza, yana wakiltar wani babban kalubale ga muradun kasashen duniya kuma lamari ne da ya saba wa dukkanin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, yana mai jaddada cewa, wannan mataki mai hatsarin gaske yana gurgunta duk wani yunkurin da ake yi na samar da zaman lafiya mai cike da adalci.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Da Iraki Sun Jaddada Goyon Bayan Kungiyoyin ‘Yan Gwagwarmaya August 9, 2025 Kwamitin Sulhu na MDD na Shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun Gaza August 9, 2025 Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza August 9, 2025 Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi tsokaci kan yadda bangaren shari’a na Turkiyya ya bayar da sammacin kama Netanyahu fira ministan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yaba da fitar da sammacin neman kama jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila 37, ciki har da shugaban gwamnatin mamayar, Netanyahu mai aikata laifukan yaki, da ministocin tsaro Gallant da Katz.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Juma’a, kungiyar ta ce wannan matakin “ya tabbatar da matsayin al’ummar Turkiyya da shugabancinsu, wadanda suka jajirce kan kyawawan dabi’un adalci da dan Adam, da kuma ‘yan uwantaka da ke tsakaninsu da al’ummar Falasdinawa da ake zalunta.”

Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: “Al’ummar Falasdinawa na ci gaba da fuskantar mummunan yakin kawar da mutane a tarihin zamani a hannun masu aikata laifukan yaki tsakanin shugabannin mulkin kama-karya,” kamar yadda ta bayyana su.

Hamas ta kuma yi kira ga dukkan kasashen duniya da hukumomin shari’arsu da su bi sahun kasar Turkiyya wajen bayar da sammacin kama mutane masu aikata muggan laifuka da kuma bin diddigin shugabannin mamayar Sahayoniyya a ko’ina, da kuma yin aiki don kawo su gaban shari’ar kasa da kasa da kuma hukunta su kan laifukan da suka aikata kan bil’adama.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025  Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Tarayyar Turai: Ana Fuskantar Matsananciyar Wahalar Isar Da Kayan Agaji Zuwa Al-Fashar Na Sudan November 7, 2025 Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon November 7, 2025 Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza November 7, 2025 Falasdinawa Miliyan 1.5 Ne Ke Cikin Mawuyacin Hali November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail
  • Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila
  • Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
  • Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma
  • Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon
  • Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza
  • Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jin Isra’ila .
  • Kwamitin Tsaron Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza
  • An Kama ‘Yan Jarida 3 A Nijar Bi Sa Tuhumar  Fitar Da Bayanai Na Hukuma