Dantsoho ya sanar da haka ne, bayan kaddamar dashi a matsayin Mataimakin Shugaban Kungiyar a kwanan baya a wani taro kan harkokin Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya da aka gudanar.

 

Kazalika, Dantsoho ya ci gaba da cewa, zai mayar da hankali ne, kan wanzar da tsarin da NPA, ta sanya a gaba da kara karfafa hadaka, musaman domin a habaka samar da sauki a fannin gudanar da hada-hadar Tashohin Jiragen Ruwa da ke a Afrika ta Yamma.

 

Idan za a iya tunawa, harkar gudanar da Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika ta Yamma na fuskantar kalubale da suka hada da, yin aiki da kayan da suka dade da rashin samar da dawamammen tsari da kuma rashin rungumar yin aiki da  kayan aiki na zamani.

 

Sai dai, ya sanar da cewa, ta hanyarin amfani da kayan aikin zamani, hakan zai bai wa Hukumarsa damar kara samun masu zuba hannun jari a fannin.

 

“Wannan nuyin da aka dora min, zai kara bani wata damar ta kara yin aiki tukuru wajen daukar matakan kara saita ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa da a yankin na Afirka ta Yamma tare da kuma kara habaka tattalin arziki, “Inji Shugaban.

 

Ya kuma nanata cewa, zai tattabatar da ya joranci ganin ana yin amfani da fasahar zamani, musamman domin a kawar duk wani shinge na hada-hadar kasuwanci da zai haifar da wani jinkiri.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tattalin Arziki Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida October 11, 2025 Tattalin Arziki Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho October 10, 2025 Tattalin Arziki An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi  October 10, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Tashoshin Jiragen Ruwa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma

A baya- bayan nan ‘yan ta’addan wadanda suka daura damarar hanawa al’umma kwanciyar hankali sun kashe daruruwan mutane, kona gidaje tare da garkuwa da mutane ciki har da mata da kananan yara.

Rahotanni daga yankunan sun tabbatar da yadda al’umma suka gaji suka kosa da jin alkawura marasa adadi daga gwamnati wadda ke kasa cikawa a yayin da hare-hare ke karuwa a duk shekara duk da karin kudaden tsaro da ake warewa..

A Sakkwato, kauyuka da dama kamar Giyawa, Kurawa, da Unguwar Lalle a gabascin Sakkwato hedikwatar gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji sun fuskanci hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a baya- bayan nan.

A Karamar Hukumar Sabon- Birni, wasu mazauna yankin sun tsere domin tsira da rai zuwa cikin dazuka bayan wani mummunan hari da ‘yan ta’addan suka kai a daren Lahadi.

A Zamfara, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a Kauran- Namoda, Maradun da Dansadau da Shinkafi inda suka kashe manoma, aka dauki mutane fiye da 40, yayin da a Katsina, kauyuka kamar Batsari, Jibia da Kankara suka sake fuskantar luguden wuta, lamarin da ya tilasta mazauna barin gidajensu.

A cikin kasafin kudin 2025, gwamnatin tarayya ta ware fiye da Naira tiriliyan 3.2 domin yaki da matsalar tsaro, mafi girman kaso a cikin dukkan bangarorin gwamnati. Duk da haka, hare-haren suna karuwa, musamman a yankunan karkara da ba su da cikakken kariya.

Ba ya ga asarar rayuka, hare-haren sun durƙusar da tattalin arzikin yankunan. Gonaki sun lalace, sana’o’i sun tsaya, haka ma yawancin matasa sun fice daga kauyuka zuwa birane don neman mafaka.

A watannin da suka gabata daruruwan mutane ne suka kauracewa garuruwa da gidajen su tare da neman mafaka a wasu garuruwan domin tsira da rayukan su a yayin da garuwawan su suka zama lahira kusa.

A bayyane yake yadda barayin daji suka kassara ayyukan noma a Arewacin kasar nan ta hanyar tilastawa manoma biyan harajin amfanin gona, hana masu shuka da ma kone gonakin bakidaya lamarin da ya yi wa Arewa da kasa bakidaya mummunar illa wajen samar da wadataccen abinci.

A makon nan al’ummar jihar Zamfara sun fito fili sun bayyana yadda ‘yan ta’adda suka hana masu girbe amfanin gona a gonakin su. Mamoman sun bayyana cewar suna cikin fargabar yadda za su girbe tare da kwashe amfanin gonar su a yayin da damana ta kawo karshe.

Mamoman a karamar hukumar Shinkafi, sun bayyana cewar suna cikin zullumin ne a sakamakon hare- haren ‘yan bindiga a garuruwan su wanda ya sa suke cikin kunchi saboda rashin mafita.

A yayin da al’ummar ke neman agajin gaggawa daga wadanda lamarin ya shafa, gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewar ta na sane da halin da al’ummar Shinkafi ke ciki kuma za ta dauki matakan da suka kamata domin shawo kan matsalar wadda gwamnatin ta ce an samu nasara sosai kan barazanar barayin daji ga manoma a jihar.

Da yawa daga cikin mazauna yankunan da ‘yan ta’adda ke aika- aikarsu na ganin dabarun da hukumomin tsaro ke amfani da su ba su da inganci saboda rashin amfani da bayanan sirri daga al’umma da kuma jinkirin amsawa bayan kai hari.

Malam Aliyu Garba, wani manomi daga Giyawa, ya bayyana cewar “Ko da an ce gwamnati ta kara kudin tsaro, to ba mu ga bambanci ba. Idan har kudi ake kashewa haka, to ina sakamakon?”

Haka kuma, Lami Umar, wadda ta rasa danta a harin Maradun, ta ce “Mun gaji da alkawuran da ake yi mana na kawo karshen barayin daji ba tare da ganin sakamako ba.”

A kodayaushe Gwamnatocin Katisna, Sakkwato, Zamfara da Kebbi kan jaddada cewar suna aiki kafada da kafada da gwamnatin tarayya wajen yaki da ta’addanci da samar da zaman lafiya .

A wata sanarwa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya bayyana cewar “Mun fara amfani da fasahar zamani wajen bibiyar hanyoyin ‘yan ta’adda, da kafa cibiyar bayanan sirri ta jiha wanda hakan zai taimaka wajen hana kai hare-hare.”

Sai dai masana na da ra’ayin karin kudin da ake kashewa a bangaren tsaro ba ya zama mafita idan ba a tabbatar da gaskiya, ingantaccen tsari da bin diddigin ayyukan hukumomin tsaro yadda ya kamata ba.

A kwanan nan al’ummar karamar hukumar Kebbe a jihar Sakkwato suka kokawa gwamnatin jiha da ta tarayya kan su kawo masu agajin gaggawa kan karuwar kisan gilla da ya shafi akalla garuruwa 12.

A jawabinsa a taron manema labarai, jagoran tawagar, Adamu Haruna Kebbe ya ce abin damuwa ne yawaitar karuwar hare- haren ta’addanci da ‘yan ta’addan ke yi masu wanda ya tilastawa daruruwan al’umma gudun hijira.

“Daruwan al’ummar mu sun bar garuruwan su, gidajen su, dukiyoynsu da gonakin su domin tsira da rai saboda jama’a na cikin fargaba saboda yanayin ya kazanta sosai, duk da hukumomi sun san abin da ke faruwa amma kisan gillar bai yi sauki ba.”

A kan wannan ya yi kira ga gwamnatin jihar Sakkwato da gwamnatin tarayya da su karfafawa hukumomin tsaro da kayan aiki domin shawo kan matsalar da ke hana masu bacci da idanu biyu.

Kebbe ya bayyana cewar al’ummar yankin sun yi gudun hijira daga mafi yawan garuruwan da lamarin ya shafa, ya ce rashin kawo agajin gaggawa zai sa matsalar tsaron ta kara tabarbarewa.

A kan wannan gagarumar matsalar tsaron, majalisar wakilai ta yi kira ga hukumomin tsaro da a matakin gaggawa su tura jami’an tsaro a mazabar tarayya ta Kebbe/Tambuwal domin shawo kan karuwar ayyukan ta’addanci a yankin.

Matakin majalisar ya biyo bayan amincewa da kudirin bukatar gaggawa da Honarabul Abdussamad Dasuki da ke wakiltar mazabar ya gabatar a zaman majalisar a ranar da ta gabata Talata kan yadda ‘yan ta’adda ke hanawa al’umma bacci da idanu biyu.

An samu yawaitar hare- haren ayyukan ta’addanci a Kebbe da Tambuwal, kisan al’umma da garkuwa da mutane da tarwatsa garuruwa da dama.

Al’ummar yankin sun bayyana cewar matsalar tsaron ta gurgunta tattalin arzikin yankin musamman ayyukan noma wanda ya sa daruruwan mutane da dama neman mafaka a sansanin gudun hijira a Sakkwato da makwabtan jihohi.

Dasuki ya bayyana cewar a ranar 12 ga Augusta 2025, ‘yan ta’adda sun shiga mazabar Fakku a karamar hukumar Kebbe tare da kashe mutane biyar da garkuwa da mutane 28 da satar shanu 37.

“Haka ma a ranar 15 ga Agusta barayin daji sun kai farmaki a mazabar Sangi tare da tilastawa jama’a neman mafaka a Kuchi da Koko a jihar Kebbi. Bugu da kari a ranar 18 ga Agusta ‘yan ta’adda sun afkawa mazabar Ungushi tare da kisan mutane biyu da garkuwa da mutane bakwai tare da asarar dabbobi.”

Dasuki ya kuma bayyana cewar, mazabar Jabo a karamar hukumar Tambuwal da mazabar Tambuwal/Shimfiri suna fuskantar kalubalen tsaro da ke bukatar agajin gaggawa.

Dan majalisar ya bayyana halin kuncin da al’ummar yankin ke ciki, ya ce munanan hare- haren sun tarwatsa kwanciyar hankalin al’umma, jama’a sun kauracewa garuruwa, haka ma yara sun daina zuwa makaranta, a yayin da manoma sun dakatar da zuwa gona a bisa ga tsoron ta’addancin.

A bisa ga amincewa da kudirin, majalisar ta bukaci rundunar sojin Nijeriya da rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro domin karfafa kai hare- hare a yankin Kuchi a karamar hukumar Kebbe da yankunan karamar hukumar Tambuwal domin kare rayuka, dukiyoyi da gonaki.

Wani mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum Aliyu Daure Tambuwal ya bayyana cewar “Kasafin kudin sha’anin tsaro na karuwa a kowane kasafi, amma babu daidaito tsakanin abin da ake kashewa da sakamakon da ake gani. Ya ce sai an tunkari tushen matsalar, talauci, rashin aiki da cin hanci, sa’annan za a ga canji.”

Duk da karin kudin sha’anin tsaro da gwamnati ke warewa a kowace shekara, Arewa maso Yamma na ci- gaba da zama cibiyar ta’addanci ba kakkautawa ta yadda jama’a ke rayuwa a cikin tsoro, lamarin da ba za a ga canji ba matukar ba a tashi tsaye an yaki ta’addancin da zuciya daya ba.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Labarai Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara October 16, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
  • Jihar Jigawa Ta Dukufa Wajen Gina Magudanan Ruwa Domin Kaucewa Ambaliya
  • Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma
  • Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
  • Alkaluman Jin Ra’ayi na CGTN Sun Shaida Amincewar Al’umma Da Karfin Tattalin Arzikin Kasar Sin
  • Matakin Da Kasashen Yamma Su Ka yi Na Maidowa Da Iran Takunkumi Ya Sabawa Doka.
  • Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan
  • An kama mata da miji suna safarar makamai a Kaduna
  • Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa