Aminiya:
2025-09-17@20:29:54 GMT

Taron PDP: Akwai yiwuwar NEC ta yanke hukunci kan Wike da Ortom

Published: 25th, August 2025 GMT

A yau ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da zama na 102 na Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), inda ake sa ran ta yanke hukunci kan wasu jiga-jiganta da ake zargi da cin dunduniyarta, ciki har da Ministan Abuja Nyesom Wike da tsohon Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom.

Majiyoyi a jam’iyyar sun ce a yayin taron, za a gabatar da rahoton kwamitin ladabtarwa ƙarƙashin jagorancin Tom Ikimi, wanda ya ba da shawarar ɗaukar mataki a kan waɗanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zangon ƙasa.

Har ila yau, taron zai tattauna shirin gudanar da babban taron jam’iyya na ƙasa a Ibadan a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, inda za a zaɓi sababbin shugabanni.

Kazalika rahoton Kwamitin Rabon Mukamai na daga cikin abubuwan da za a tattauna.

Mataimakin Jami’in Yaɗa Labarai na PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya ce an kammala duk shirye-shirye, kuma taron zai gudana lafiya ba tare da wata rigima ba, yana mai cewa za a sake tabbatar da matsayar jam’iyyar kafin zaben 2027.

Dambarwar Mike

Sai dai saɓani ya ƙi ƙarewa a babbar jam’iyyar adawar, musamman kan matsayin Wike, wanda ke adawa da wurin taron, yana mai cewa dole ne jam’iyya ta fara amincewa da taron Kudu maso Kudu da masu goyon bayansa suka gudanar wanda NEC ta yi watsi da shi.

Wasu jiga-jigan PDP na zargin ministan da lalata jam’iyya, yayin da wasu ke ganin a bi a hankali don kada a ƙara rura rikici.

Shugabannin matasa da wasu shugabannin jihohi sun nuna goyon baya ga taron na Ibadan da tsarin rabon muƙamai, suna kira ga mambobi da su fifita haɗin kan Jam’iyyar.

Masana sun ce wannan zama na NEC zai taka muhimmiyar rawa wajen ganin ko PDP za ta tsira daga rikicin cikin gida kafin zaben 2027.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Babban taro Jam iyyar PDP

এছাড়াও পড়ুন:

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu

Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki Guda 5 A Wajen Taron Kolin kere-kere .
  • Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
  • An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Runduwar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar