Aminiya:
2025-12-03@14:24:50 GMT

HOTUNA: Al’ummar Jihar Neja sun yi addu’o’in neman zaman lafiya

Published: 18th, October 2025 GMT

Al’ummomin ƙananan hukumomin da ke yankin Arewacin Jihar Neja sun gudanar taron Sallah da addu’o’i na musamman domin neman Allah Ya kawo musu zaman lafiya, sakamakon matsalar ’yan bindiga da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.

Hare-haren ’yan bindiga ya yi ajalin dubban mutane tare da raba su da muhallnasu da hanyoyin samun arziki a sassan Jihar Neja da wasu sassan Najeriya.

Ga hotunan;

Dubban jama’a daga yankin ƙananan hukumomi shida da ke Arewacin Jihar Neja sun gudanar da addu’a ta musamman domin samun tsaro da aminci. Manta da ƙananan yara sun fito Filin Idi na Kontagora domin halartar taron addu’o’in da aka gudanar a ranar Asabar. Mutane daga ƙananan hukumomin Magama, Borgu, Rijau Mashegu da Kontagora na daga cikin yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka fi addaba a Jihar Neja. ’Yan ta’adda sun kashe mutane sun sace wasu da dama tare da dabbobi, baya ga ƙona gidaje da dukiyoyi, tare da tilasta wa dangin waɗanda aka sace biyan kuɗaɗen fansa. An sace dubban mutane, yawancinsu mata da magidanta a sassan Jihar Neja wadda ke fama da matsalar ’yan bindiga kamar maƙwabtansa jihohin Kwara, Kaduna, Kebbi, Zamfara da Katsina da Kogi da da Babban Birnin Tarayya

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Zaman lafiya yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta

Daga Aliyu Muraki

Hukumar Ilimi Matakin Farko ta Jihar Nasarawa (NSUBEB) ta yi barazanar kamawa tare da gurfanar da iyayen da  ‘ya’yansu ba sa zuwa makaranta a jihar.

Shugaban Hukumar, Dr. Kasim Mohammed Kasim ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a matsayin wani bangare na ayyukan babban  taron inganta ilimi da hukumar ta shirya.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce, ilimin boko matakin farko haƙƙin kowanne yaro ne, ba gata ba, kuma ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani yaro a baya ba.

Shugaban Hukumar ya bayyana cewa hukumar ta yanke shawarar gudanar da gagarumin wayar da kan jama’a ta hanyar tarurrukan jin ra’ayoyin jama’a, da kafofin watsa labarai domin jaddada muhimmancin ilimin boko na a matakin farko ga kowane yaro a jihar.

Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce sun sayi motocin bas guda bakwai da za a gudanar da wayar da kan jama’a a dukkan sassan kananan hukumomi 13 na jihar, domin fadakar da iyaye  muhimmancin kai ‘ya’yansu makaranta.

Game da babban taron, Dr. Kasim Mohammed Kasim ya ce wannan taro zai hada manyan masu ruwa da tsaki ciki har da masana ilimi, jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, masu tsara manufofi, iyaye, malamai da sauransu.

Ya ce, mahalarta taron za su tattauna hanyoyin magance matsalolin ilimi, musayar kwarewa da sabbin dabaru domin kara inganta koyarwa da koyo a jihar.

Ya lissafo wasu daga cikin matsalolin da suka hada da ginin makarantu marasa inganci, karancin kujeru, karancin malamai, yawan rashin zuwa aiki daga ma’aikata, da rashin daidaitaccen tsarin tura malamai, da sauransu.

Ya ce hukumar ta maida malamai 1,900 wadanda a da ke aiki a ofis-ofis zuwa azuzuwa domin koyarwa, kuma nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin malamai 1,000 domin cike gibi a makarantun jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta
  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gurfanar da Iyayen Yaran da Ba Sa Zuwa Makaranta
  • Shugaba Pizishkiyan:  Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • Baqaei: Amurka Ce Babbar Barazana Ga Zaman Lafiya Da Tsaro A Duniya
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Garin Eruka Na Jihar Kwara
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • ’Yan bindiga sun sace amarya da ƙawenta 14 a Sakkwato