Aminiya:
2025-12-03@23:36:12 GMT

’Yan sanda sun tsare ɗan jarida kan zargin ɓata sunan hadimin gwamnan Kano

Published: 19th, October 2025 GMT

’Yan sanda sun kama ɗan jarida Ibrahim Ishaq Dan’uwa Rano, kan zargin ɓata sunan Babban Hadimin Gwamnan Kano kan Al’amuran Fadar Gwamnati, Abdullahi Ibrahim Rogo.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an ’yan sanda daga Hedikwata ta Ɗaya ne suka kama Dan’uwa Rano a ranar Asabar yayin da yake aiki a ofishinsa da ke Kano.

Magidanci na neman shawarar ’yan sanda kan ƙara aure a Kano Gwamnati ta ɗauki matakin rage shan gishiri a Nijeriya

Shaidu sun ce an kama shi ba tare da gabatar da takardar izinin kama shi ba.

Ana tsare da ɗan jaridar ne bisa zargin ɓata sunan hadimin cikin wani shirin barkwanci mai suna ‘Imalu’ da yake wallafawa a shafinsa na YouTube mai suna ‘Dan’uwa TV‘.

An ce ɗan jaridar ya yi shaguɓe a cikin shirin inda ya yi magana a kan hadimin tare da zarginsa da karɓar cin hanci don bai wa mutane damar ganawa da gwamnan.

Ko da yake bai ambaci suna ba a cikin shirin ba, Rogo, ya kai wa ’yan sanda ƙara, inda ya ce ana amfani da shirin wajen ɓata masa suna.

Dan’uwa Rano, ya tabbatar cewa ana yi masa tambayoyi kan shirin da kuma zargin gudanar da tasha a in5tanet ba tare da lasisin Hukumar NBC ba.

“‘Yan sanda sun ce ba mu da lasisi daga NBC, kuma kamfaninmu bai yi rijista ba,” in ji shi.

Kakakin ’yan sanda na Shiyya ta Ɗaya, CSP Bashir Muhammad, ya tabbatar da kama ɗan jaridar, inda ya ce an kama shi ne bayan ƙorafin ɓata suna da aka shigar a kansa.

Ya ce: “Babban Sufeton ’Yan Sanda na Shiyya ta Ɗaya, AIG Ahmed Garba, ya bayar da umarnin a gayyaci ɗan jaridar don yi. bincike. Bayan bincike, idan an same shi da laifi, za a gurfanar da shi a kotu.”

AIG Garba, ya kuma shawarci ’yan jarida da su tabbatar da adalci a cikin rahotanninsu tare da tuntuɓar ofishin hulɗa da jama’a na ’yan sanda kafin wallafa labarai.

Ya kuma nemi su bari ana gudanar da bincike ba tare da yin katsalandan ba.

’Yan sanda sun tabbatar da cewa za su yi bincike cikin gaskiya da adalci, kuma za a sanar da jama’a sakamakon abin da suka samu.

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito EFCC da ICPC na binciken Abdullahi Rogo bisa zargin almundahanar kuɗi Naira biliyan 6.5.

Ana zargin ya karkatar da kuɗaɗen gwamnati ta amfani da wasu abokan hulɗarsa tsakanin watan Nuwamban 2023 da Fabrairun 2025.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Jarida Ɗan Jarida Ɗan Uwa Rano Yan sanda sun ɗan jaridar

এছাড়াও পড়ুন:

Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara

Daga Ali Muhammad Rabi’u

An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa  dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri.

An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin.

A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.

Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma su rika kai rahoton duk wani abin da suke zargin zai iya haddasa fitina ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a  makarantar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai
  • ’Yan sanda sun kama mutum 28 kan zargin lalata mata da yara a Yobe
  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • An tsare tsohuwar shugabar kula da manufofin ketare ta EU Mogherini bisa badakalar cin hanci
  • DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
  • An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
  • ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar