Tinubu Ya Amince A Fara Aikin Tashoshin Jiragen Ruwa Na Apapa Da Kalaba Da Fatakwal Da Warri — NPA
Published: 17th, October 2025 GMT
Shugaban ya kara da cewa, aana sa ran aikin za a fara gudanar da shi ne, a zangon farko na shekarar 2026.
Ya ci gaba da cewa, aikin na yiwa wadannan Tashoshin garanbawul, na daga cikin kudurorin Gwamnatin Tarayya na zamantar da Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa, musamman ta hanyar samar da kayan aiki na zamia da kuma ci gaba da janyo hankalin masu son zuba hannun jari zuwa ga fannin, wanda hakan zai kuma kara sanya gasa a cikin wadanda suke a cikin fannin.
Ya bayyana cewa, masu son zuba hannun jari a fannin suna ci gaba da nuna shawarsau, musamman saboda sauye-sauyen da Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinbu ta kirkiro da su, a fannin kara habaka tattalin arzkin kasar.
Kazalika, Shugaban ya kuma jinjinawa Ministan Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa na kan Teku Adegboyega Oyetola, musamman kan goyon bayan da yake ci gaba da bayarwa ga fannin.
Ya yi nuni da aiki irin wannan mai mahimmancin gaske, abu da ke bukatar isassehen lokaci domin a samu damar gudanar da ciakken shiri, duba da cewa, aiki ne, da ya kunshi bangaren injiniyoyi gudanar da bincike da sauransu.
Hakazalika, Dantsoho, wanda kuma shi ne, Masu Kula da Harkar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Afrika ta Yamma wato IAPH, ya jaddda cewa, tattalin arzikin kasar nan zai kara samun dimbin masu son zuba hannun jari a fannin, musamman biyo bayan sauye-sauyen da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiro da su.
A cewarsa, Hukumar ta NPA ta yi hadaka da sauran masu ruwa da tsaki a fanin, wanda ya sanar da cewa, hadar za ta taimaka wajen janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari a fannin.
Ya yi nuni da cewa, a bayanan da wasu daga cikin masu ruwa da tsaki suka bayyana a wajen taron shi ne, yadda a shekarun baya, fannin ya fuskanci rashin nuna yarda da kuma iya gudanar da shugabanci na gari, inda ya kara da cewa, a yanzu mu muna bukatar ganin cewa, an yi hadaka domin a kara ciyar da fanning aba.
“Zamu yi wannan hadakar ne, ta hanyar nuna amincewa domin a cimma burin da aka sanya a gaba, na yin hadakar, “ Inji Dantsoho.
Shugaban ya kuma sanar da cewa, wani Kamfani da ke a kasar Singapore ya bai wa Hukumar NPA kwangila wadda za a gudanar da ita, a karkashin shirin NSW na kasar nan.
“Kamfanin da kayan aiki da kudade da za aiwatar da kwangilar, A cewar Shugaban.”
Shugaban ya kara da cewa, aikin bunkasa ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa, aiki ne da ke bukatar a kashe kudade masu yawa, wanda kuma masu zuba hannaun jari daga kasar waje ne kawai za su iya yin hakan.
Dantsoho ya ci gaba da cewa, duba da yadda a yau ake yin amfani da kayan aiki na zamani dajen tafiyar da ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwa a fadin duniya, dole ita ma Nijeriyata shiga cikin wannna sahun a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwa da a kasar.
“A yau duniya ta sauya wajen daina yin amfani da tsohon tsari wanda mutane suke gudanar da abu daya kadai,” A cewar Shugaban.
A cewar Shugaban Nijeriya ba ta wadatatun kudaden da za iya aiwatar da wadannan manyan ayyukan, amma muna kan ci gaba da kokarim janyo ra’ayin masu son zuba hannun jari a fannin.
“Akwai matukar bukatar mu yi hadaka da sauran jama’a, domin kamar yadda na bayyana a shekarar 2006, cewa ya zama wajibi Hukumar ta NPA ta daina doharo kan bangaren ggwamnati, amma ta mayar da hanjali a bangaren kamfanonin masu zaman kansu.
“A yanzu muna son mayar da hankali wajen zuba hannun jari ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, kuma wannan abu ne, da ke bukatar kudade masu yawa, muna kuma kara kokari domin kulla wannan hadakar, Inji Dantsoho.
“A yayin da muka hallara a nan, za mu kuma kara hallara wasu taruka na da ban kuma suna yi mana kallon cewa, tabbas mu abokan yin hadaka ne,” Acewar Shugaban.
“Muna a cikin kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na PMAWCA, muna kuma a cikin kungiyar IAPH da kuma ta masu kula da masu tafiya cinari ta kasa da kasa wato IMO za mu kuma ci gaba da tattaunawa wadda muke da yakin za a samu sakamako mai kyau,” Inji Dantsoho.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: masu son zuba hannun jari a fannin Tashoshin Jiragen Ruwa Shugaban ya
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Aikin Tsaftace Unguwar Kwankwasiyya Mataki Na biyu
Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane.
Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya.
A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli.
Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da Amana kwarin guiwa da su taka rawar gani wajen kiyaye tsafta a tsakanin al’ummarsu.
Ya kuma kara jaddada cewa shirin zai taimaka wajen rage cututtuka masu alaka da tsaftar muhalli ta hanyar sarrafa sharar gida da inganta ayyukan tsafta.
Mukaddashin Manajan Daraktan ya kuma bayyana cewa, aikin tsaftar muhalli ya yi daidai da tsarin sabunta biranen gwamnatin jihar, wanda ya ba da fifiko ga ci gaba da farfado da manyan biranen uku na Kwankwasiyya da Bandirawo da kuma Amana.
Ya tuna cewa Birnin Kwankwasiyya, wani bangare ne na aikin raya birane da aka fara a zamanin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, an tsara shi ne domin magance matsalolin da suka hada da karancin gidaje, da rage cinkoson birane da dorewar muhalli.
A karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, an sake yin kokarin farfado da wadannan garuruwa, da warware batutuwan da suka hada da biyan kudaden fansho, da tabbatar da gudanar da ingantaccen albarkatun kasa.
Engr. Kwa ya kara da cewa ayyukan tsaftar muhallin da ake ci gaba da yi sune muhimman matakai na cimma wadannan manufofin raya birane da inganta rayuwa da tabbatar da dorewar muhalli a fadin sabbin biranen Kano.
Rel/Khadijah Aliyu