Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi – Masari
Published: 17th, October 2025 GMT
Shin menene makasudin shirya irin wannan taro na masu ruwa da tsaki akan sha’anin ilimi da aka gudanar a yau?
Makasudin wannan taro shi ne a fadakar da mutane ayyukan wannan hukuma ta TETFUND da take yi, sannan kuma a yi magana da wadanda suka fi amfana da shi wannan tsari na TETFUND. Kamar jami’ai da makarantu da kuma dalibai sannan kuma a karbi shawarwari ga jama’a akan yadda za a bunkasa wannan aikin na hukumar tallafawa manyan makarantu na gaba da Sakandire a Nijeriya.
Wannan shi ne makasudi kuma na farko da ake san a jawo al’umma a ciki su dan abinda ake yi da yadda ake kashe kudaden da kuma yadda ake tarawa da makasudin tara su da makarantun da ake ba kudaden da kuma su makarantu yadda suke amfani da kudin
Shin kamar bangarori nawa ne suka halarci wannan taro na masu ruwa da tsaki a wannan hukuma ta asusun TETFUND?
Aminu Bello Masari: Na farko akwai bangarorin makarantu da Dalibai da ‘yan jarida da masu bukata ta musamman da kungiyoyin Malaman jami’o’i wata ASUU da da COUSU da duk masu ruwa da tsaki akan harkar ilmin gaba da Sakandire da kungiyoyin farar hula duk sun halarci wannan taro, bayan jami’an gwamnati wadanda suka zo daga fanni-fanni da tsofaffin shugabanni da majalisar tarayya da suke da hakkin kudaden da ake kashewa baki daya.
Jama’a da dama sun yi magana akan zama wasu sun mika kokon barar su akan ilmin gaba da Sakandire wani mataki zaku dauka a kan haka?
Daman ma’anar wancan zama shi ne domin a samu karin shawarwari daga al’umma da masana ta yadda za a cigaba da lissafin kasafin kudi na shekarar 2026, samun wadannan shawarwari za mu zauna mu kalle su, mu duba wadanda za su iya yiyuwa bana, wasu kuma sai an tura gaba, amma dai za a yi wani abu akan shawarwarin da aka samu insha’Allahu.
Masu bukata ta musamman sun samu wakilci kuma har sun mika bukatun su, me zaka ce game da haka?
To, na farko dai su masu bukata ta musamman darkatan da ke kula da gine-gine ya ce to yanzu dole ne duk ginin da za a yi dai an tabbatar da yana da tsari na kula da masu bukata ta musamman. Kuma sun kawo bukatar suna san a yi masu wani gurbi a ofishin shi sakatare na hukumar tallafawa manyan makarantun gaba da Sakandire, wannan kuma wani abu ne da sai mun zauna wajen taro zamu kalli abubuwan sannan abinda ke yiyuwa kuma shi za a yi.
A takaice me kake son cimmawa na ganin an ciyar da wannan hukuma ta TETFUND gaba?
Ai babban al’amari shi ne, a sanya mutane a cikin hidimar su san abinda ake yi, kuma su ba da shawarwari yadda za a kara bunkasa abin da ita wannan ma’aikata take yi, kudi ake amsa masu yawa kuma wajibi ne a gayawa jama’a yadda ake sarrafa wadannan kudaden a dukkan jami’o’in gwamnatin tarayya kusan 250 banda kwalejojin da sauran su ba wanda bai amfana da wadannan kudadai duk shekara.
Zuwa yanzu an kashe nawa a wannan hukuma mai tallafa wa manyan makarantun gaba da Sakandire a Nijeriya?
Yanzu abin da za mu iya cewa shi ne mun yi kasafin kudi, wanda zuwa yanzu an baiwa su makarantun daunin su na kaso hamsin (%50) bisa dari wanda yanzu lissafin da aka yi ya wuce biliyan 500 wanda aka ba su Makarantun a hannun su, to kuma za su kawo yadda za su kashe kudaden, sannan sauran an yi aikin lafiya da su wanda yanzu haka an fada a wajen taron da kuma aikin wuta da aikin tsaro duk wadannan wurare ne da aka sanya kudi da ayyuka na musamman.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba
Kwamandan rundunar ta 6, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yabawa sojojin bisa nuna kwarewa da juriya, inda ya bukace su da su ci gaba da sharar daji har sai an kakkaɓe duk wasu masu aikata laifuka gaba daya a jihar Taraba.
Ya bayyana ci gaba da jajircewar rundunar sojin Nijeriya wajen tabbatar da tsaro da tsaron duk ‘yan kasa masu bin doka da oda, yana mai ba da tabbacin cewa, sojojin za su ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da al’ummomin yankin domin samun dawwamammen zaman lafiya a jihar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA