Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi
Published: 19th, October 2025 GMT
Ofishin Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar a ranar Asabar cewa “Mashigar Rafah a Gaza za ta kasance a rufe har sai abin da hali ya yi a nan gaba.”
Ofishin Netanyahu ya kara da cewa, bude mashigar ya dogara ne bisa ga yadda Hamas ta aiwatar da tsarin yarjjeniyar da aka cimmawa wajen mika gawawwakin Isra’ilawa da ke hannunta.
Wannan bayanin ya zo ne jim kadan bayan da ofishin jakadancin Falasdinu a Masar ya sanar da cewa za a sake bude mashigar Rafah da ke kudancin zirin Gaza a ranar Litinin mai zuwa.
A nata bangaren, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin da Netanyahu ya dauka yana a matsayin keta sharuddan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da kuma karya alkawuran da ya dauka ga masu shiga tsakani da masu bayar da lamuni ga yarjejeniyar.
Kungiyar ta yi bayanin cewa, ci gaba da rufe mashigar Rafah, da hana fitar da wadanda suka jikkata da marasa lafiya, da hana shigar da kayan aiki na musamman da ake bukata domin neman wadanda suka bace a karkashin baraguzan gine-gine, hakan zai haifar da jinkirin dawo da gawarwakin Isra’lawan.
Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da masu bayar da lamuni ga yarjejeniyar da su dauki matakin gaggawa don matsa lamba a kan Isra’ila domin bude mashigar Rafah cikin gaggawa, tare da tilasta mata yin aiki da dukkanin sharuddan da ke cikin yarjejeniyar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Bayyana Cewa: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya October 18, 2025 Joseph Kabila Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa October 18, 2025 Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa October 18, 2025 Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025 Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mashigar Rafah
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar.
Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa.
Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai da kashi kashi 71 ga manyan ayyukan ci gaba, yayin da sama da naira biliyan dubu dari biyu da tamanin da shida daidai da kashi 29 za su tafi ga al’amuran yau da kullum.
Ya ce kaso mafi tsoka na ayyukan ci gaba ya mayar da hankali ne kan gina manyan muhimman ababen more rayuwa masu dorewa.
Rabe-raben kason sune: Ilimi ya samu kashi 25 bisa dari, sai Ayyukan Gine-gine da Cigaban KarKarkashi ma kashi 25 bisa 100, Lafiya kashi 15 bisa 100; Noma da Samar da Abinci kashi 11 bisa 100; Tsaro kashi 6 bisa 100; Ci gaban Zamantakewa kashi 5 bisa 100; Muhalli da Matakan Sauyin Yanayi kashi 4 bisa 100; sai Mulki da Gudanarwa kashi 5 bisa 100.
A nashi jawabin, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya ce kasafin kuɗin 2026 ya nuna sahihiyar manufa wadda ta ƙunshi faɗaɗa ababen more rayuwa a yankunan karkara, da habbaka kwazon ma’aikata da tabbatar da ganin dukkan al’ummomi suna cin gajiyar ci gaba mai ɗorewa da ya haɗa kowa.
Rt. Hon. Liman ya jinjina ga Gwamna Uba Sani da tawagarsa a bisa gabatar da kasafin da ya dace da hangen nesan gwamnatin da ke ƙoƙarin gina Jihar Kaduna mai yalwar arziki.
Ya kuma gode wa gwamnan bisa samar da zaman lafiya, haɗin kai da sabunta kudurori a fadin jihar, tare da yabawa gwamnan bisa rashin yin katsalandan cikin harkokin majalisar wanda hakan alama ce dake nuna cikakken tsarin rabon iko da ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingantaccen sa ido da daidaito tsakanin bangarorin gwamnati.