Yayin da aka ce jam’iyyun siyasa a jamhuriya ta farko, sun fi karkata kan yanki, an yi yunkurin kafa jam’iyyun kasa a jamhuriya ta biyu da gangan.

A wancan jamhuriyar (1979–1983), manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su ne GNPP, NPN, NAP,NPP, PRP, da kuma UPN.

Duk da cewa, jam’iyyun sun banbanta a akida; amma ana ganin jam’iyyun UPN da PRP, a matsayin na masu fafutuka da kuma jajircewa, domin kuwa jam’iyyar UPN ta tsaya tsayin-daka wajen aiwatar da manufofinta.

An gina tsarin jam’iyyar bisa manyan manufofi hudu kamar haka: ilimi kyauta tun daga makarantar reno har zuwa manyan makarantu, harkar kiwon lafiya kyauta, hadin gwiwar karkara da ci gabanta da kuma samar da cikakkun ayyukan yi masu dorewa. Wadannan alkawura, an bi su ne bisa tsari na addini a jihohin da suka yi mulki, wato Jihar Legas, Oyo, Ogun, Ondo, da kuma Bendel.

A halin da ake ciki yanzu, yunkurin daidaita daidaito wajen aiwatar da tsarin ya samu matsala, a cewar rahoton LEADERSHIP.

LEADERSHIP ta tuna cewa, yunkurin da gwamnonin jihohi suka yi a baya na aiwatar da tsarin duba takwarorinsu a karkashin kungiyar gwamnonin Nijeriya, yanzu abin bah aka yake ba.

Yayin da jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta PDP ke ci gaba da gudanar da taron gwamnoninsu, an nuna damuwa kan rashin aiwatar da muhimman tsare-tsaren jam’iyyar da kuma ci gaba da shirye-shiryen jam’iyyar ta hanyar gwamnatocin jam’iyyar daya da suka gaje su, wanda hakan ke haifar da manufofin jam’iyyar.

Wannan lamari dai ya kara yin tsamari sakamakon ficewar gwamnoni daga jam’iyyunsu.

Tun daga 1999, jam’iyyu sun zama tamkar wasu motoci ne da ake yin amfani da su, domin cin zabe;

 

Ba Za Mu Sake Bari Haka Ta Faru Ba – ADC

Sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa; rikicin da ke tattare rashin aiwatar da tsarin jam’iyyya na bai-daya a jihohin da jam’iyya daya ke mulki, na nuna cewa wata babbar matsala ce.

Ya ce, tun daga farkon jamhuriya ta hudu, jam’iyyu suka zama masu matukar rauni a cikin al’umma tare da kasancewa a matsayin wani dandali na ‘yan siyasa na tsayawa takara.

“Saboda haka, ba kamar jam’iyyun jamhuriya ta biyu ba, wadanda suka ginu a kan akidu, manufofi da kuma tsare-tsare. Jam’iyyun a wancan jamhuriyar, sun kasance tamkar wasu motoci na musamman, domin gudanar da zabe; saboda haka, don ba su da karfi; ba za su iya dora ikonsu ko akidunsu a kan daidaikun ‘yan siyasa ba.

“Don haka, idan kuna da jihohi shida a karkashin jam’iyya, sannan kuma kowannensu ya fitar da nasa tsarin ba tare da an ga akida daga jam’iyyar ba, to sai a ga irin wannan rashin jituwa, rabuwar kai ko kuma rashin jituwar ta yi yawa.

Ya kara da cewa, a jamhuriya ta biyu mutane sun zabi jam’iyyu ne saboda abin da za su samu.

“Shi yasa mutane irin su marigayi Chinua Achebe, sun shiga jam’iyyar PRP, saboda imani da ya yi da akidu da kuma manufofinta.”

“Amma ida za a iya tunawa, shugaban jam’iyyar ADC na kasa Sanata Dabid Mark ya ce; muna gina wannan jam’iyya ne, wanda ba za ta bar duk wanda aka zaba a ADC ya yi abin da ya ga dama ba bayan samun mulki. Daga rana ta farko, za mu mika wa zababbu manufofin da ke kunshe da wannan jam’iyya,” in ji shi.

Ya ce, idan har jam’iyyu za su iya bunkasa tsarin tafiyar da harkoki da manufofinsu na al’umma, duk wanda ya samu mukami dole ne ya aiwatar da manufofin jam’iyya, kamar yadda aka gani a jamhuriya ta biyu a karkashin jam’iyyar UPN.

Ya yi nuni da cewa, babbar mafita ita ce karfafa jam’iyyun siyasa tare da tabbatar da cewa; ba za su bison zuciyar mutane ba.

 

Dalilin Da Ya Sa Jam’iyyun Siyasa Suka Kasa Aiwatar Da Manufa Iri Daya- IPAC

Majalisar bayar da shawara kan jam’iyyu (IPAC), ta bayar da haske kan dalilan da suka haifar da wannan gazawa ta demokuradiyya tare da samar da hanya mai bullewa.

A wata tattaunawa da LEADERSHIP, shugaban IPAC na kasa, Dakta Yusuf Mamman Dantalle ya bayyana cewa; manufofin jam’iyya, wadanda ke tattare da akidu da manufofin da ke tsakanin jam’iyyun siyasa da masu zabe, sun zama tamkar wadansu takardu da ake yin watsi da su bayan kammala zabe.

Duk da haka, shugaban na IPAC ya lura cewa; fassarar alkawuran da aka yi a sakamakon gudanar da mulki, ya zama mai matukar wahala; saboda dalilai da dama, ciki har da inganta yanayin zamantakewa da tattalin arziki, banbancin da ke tsakanin jihohi da kuma na kananan hukumomi.

 

Akwai Bukatar Sauya Fasalin Tsarin Cikin Gaggawa – CISLAC

Da yake zantawa da LEADERSHIP kan wannan batu, babban jami’in tsare-tsare a cibiyar CISLAC, Suleiman Gimba ya nuna cewa; demokuradiyyar Nijeriya na fama da matsananciyar matsala, rashin daidaito, musamman wajen aiwatar da manufofin jam’iyya.

Ya bayyana yadda a baya aka taba kafa tsarin mulkin siyasa a karkashin jam’iyyu irin su UPN, wanda a halin yanzu abubuwan ba haka ake gudanar da su ba.

“Gwamnonin da aka zaba a jam’iyya guda, suna bin wasu manufofi daban-daban, wasu jihohin sun tafi a bangaren samar da ababen more rayuwa, wasu sun tafi a kan wasu abubuwa da ban, wasu kuma ma babu ruwansu da akidar da jam’iyyar tasu ta kafu a kai,” in ji Gimba.

“Dalili kuwa shi ne, saboda a yau; jam’iyyun suna aiki ne tamkar wasu na’urorin lashe zabe fiye da gwamnati.”

Gimba ya dora alhakin hakan a kan wasu muhimman abubuwa guda uku: raunin tsarin jam’iyya na cikin gida, rashin tushen akida da kuma rashin tsarin samar da kudade ga jam’iyyun siyasa.

A cewar tasa, idan ba tare da tallafin jama’a ko samar da wata hanyar shigowar kudade mai dorewa ba, jam’iyyu za su ci gaba da yin garguwa da masu hannu da shuni da kuma masu rike da madafun iko ne, wadanda ke bankado ayyukansu.

Gimba ya kara kwatanta shugabannin Nijeriya da alakarsu da jam’iyyun siyasa.

Ya ce, Obasanjo ya nuna karfi tare da juya jam’iyyarsa yadda yake so a lokacin mulkinsa, inda su ma shugabannin da suka biyo bayansa ke ci gaba da kwatanta hakan.

Kazalika, ya kawo misali da ajandar Tinubu ta ‘Renewed Hope Agenda’, wanda ya bayyana shirin a matsayin nasa na kashin kansa, maimakon na tsarin jam’iyyar APC.

“Babu shakka, wannan sauyi ya ci gaba da raunana jam’iyyun siyasa, yanzu haka muna da shugabannin zartarwa da ke mulki ta hanyar ka’idojin kashin kansu tare da kawar da akidun jam’iyya baki-daya, in ji shi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasa manufofin jam iyya jamhuriya ta biyu jam iyyun siyasa a jamhuriya ta a karkashin

এছাড়াও পড়ুন:

An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia

Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.

Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.

Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina