Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
Published: 17th, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, a ofishinta da ke Gusau.
Haruna ya ce shirin ya yi dai-dai da hangen nesan babban kwamandan hukumar gyaran hali ta Najeriya da nufin inganta jin dadin fursunonin da ke gidajen yari.
Kwantirolan ya kuma jaddada bukatar inganta asibitin hukumar da ke cibiyar tsaro ta matsakaita, Gusau, da samar da isassun kayan aikin likita da magunguna masu mahimmanci don biyan bukatun kiwon lafiyar fursunoni.
Murtala Mohammed Haruna ya lura da cewa, matakin ya dace da ajandar sabunta bege na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya mayar da hankali kan inganta jin dadin daukacin ‘yan Najeriya, ciki har da wadanda ke tsare.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Mustapha Abubakar ya fitar, ya ce sun kai ziyarar ne da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumar gyaran hali da ma’aikatar lafiya ta jihar domin inganta harkokin kiwon lafiya ga fursunonin dake fadin jihar ta Zamfara.
Da take mayar da jawabi, Dakta Nafisat Muhammad Maradun ta yabawa hukumar gidan yari bisa jajircewar da take yi na kula da fursunonin da kuma kare lafiyar jama’a.
Ta bayyana cewa tuni Gwamna Dauda Lawal ya siyo kayayyakin jinya da kayan aikin da ya yi alkawari a ziyarar da ya kai gidan gyaran hali na Gusau.
A cewarta, nan ba da jimawa ba za a mika magungunan da aka sayo ga hukumar, yayin da za a sanya kayan aikin da zarar an kammala inganta asibitin.
Kwamishinan ta ba da tabbacin cewa Konturola na ma’aikatar a shirye yake a karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, don yin hadin gwiwa da Hukumar Kula da Lafiya don inganta harkar kiwon lafiya.
Ta kara da cewa hadin gwiwar za ta hada da tallafin fasaha don gyare-gyare, inganta kayan aiki, da tsarin shiga NHIS.
REL/AMINU DALHATU