HausaTv:
2025-12-03@23:36:10 GMT

Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159

Published: 19th, October 2025 GMT

159-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun kawo maku wasikar da Imam Al-Hassan(a) ya rubutawa Mu’awiya dan Abu Sufyan wanda yayi tawaye wa mahaifinsa imam Ali(a) bayan an masa ba’a a madina da sunan neman jinin Khalifa uthman. Don haka Imam Alhassan ya gaji mahaifi a wannan jayayyar, ya bukaci Mu’awiya ya dawo ya mika kai ya hada kan musulmi.

Kafin haka Imam Al-hassan ya tunatar da shi abubuwan da suka faru bayan wafatin manzon Allah (s) ta yadda musulmi larabawa suka fara jayayya a tsakaninsu kan wanda zai karbi shugabancin Muhammad (s) a bayansa. Bayan jayayya mai yawa sai mutanen ansar suka barwa muhajirun wadanda kuma kuraishawa ne. suka yi bai’a wa Khalifa na farko.

Ya kuma tabbatar da cewa kuraishawa sun zalunci ahlulbaiti a lokacinda suka ki mayar masu da hakkinsu bayan sun bukaci hakan. 

Sannan munji yadda kafin Imam Al-Hassan (a) mahaifinsa Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya kawo wannan batun a cikin wasikar da ya rubutawa mutanen kasar Masar bayan ya karbi khalifanci inda, yad aga bayyana wannan al-amarin, kan cewa kuraishawa sun kwace hakkinsa, na shugabanci, duk da cewa kafin wafatin manzon All..(s) bai tsamman zasu yi haka. Amma da suka yi kuma shi yaki ya bisu, amma da ya ga cewa abinda suka yi yasa larabawa suka ridda su fice daga addinin musulunci, suna ma kira ga rusa addinin Mohammad (s), sai ya ga cewa dolene ya taimakawa musulunci da musulmi don kada musibun su yi masa yawa, idan musulunci ya rushe ko ya sami tawaya.

A cikin shirimmu nay au zamu fara kawo maku wasikar Mu’awiya dan Abu Sufyan bayan ya karbi ta Imam Alhassan ya kuma karantata. Inda yake cewa

(Bayan haka. Hakiki na fahinda abinda ka fada dangane da manzon Allah (s) shi ne ya fi cancanta falala gaba daya daga na farko zuwa na karshe, sannan ka ambaci jayayyar musulmi kan shugabanci a bayansa, ka kuma bayyana tuhumarka ga Abubakar Assidiku da Umar, da kuma Abu Ubaida dan Jarrah amintacce, da salihan bayi cikin wadanda suka yi hijira, ban ji dan kayi haka ba. Don lalle a lokacinda al-umma ta yi jayayya kan shugabanci a tsakaninta, ta ga cewa kuraishawa ne suka fi cancanta da lamarin, sai kuraishawa da Ansar da masu falala a cikin addini daga cikin musulmi suka ga cewa zasu shugabantar da wanda ya fisu ilmi a cikinsu, kuma basu yi kuskure ba, don da sun san wani mutum wanda ba Abubakar ba, wanda zai kare hurumin addinin musulunci, da basu barshi suka zabi Abubakar ba.

Sannan a yau indan mun dawo Tsakani na da kai, al-amarin yana nan kamar yadda suka kasance, da na san cewa kai ne mafi sanin al-amuran shugabanci, kuma ka fi dacewa da shugabancin wannan al-ummar, kuma ka fi kyautata shugabanci, ka fi iya kaidi wa makiya, ka fi iya tara haraji, da na mika maka shugabanci bayan mahaifinka. Sannan mahaifinka ya yi makirci wa Uthman har aka kashe shi yana matsayin wanda aka zalunta, sai Allah ya nemeshi da jininsa, wanda Allah ya neme shi da wani abu ba zai kubuce masa ba, sannan ya kwacewa al-umma al-amarin shugabancinta, ya rarraba hadin kanta, sai wadanda suke dai-dai da shi a matsayi a cikin wadanda suke da sabika a shiga musulunci, da yin jihadi, da kuma dadewa a cikin musulunci, suka saba masa, yayi iddi’a’ii kan cewa sun kwance bai’arsa, ya yakesu ya kuma zubar da jinni, ya kuma halatta huruminsu, sannan ya zo mana yana iddi’a ‘iin bai’arsa a kammu, amma yana son ya mulke mu ne a dole, mun yakeshi ya yake mu.         )

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna

Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu.

Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da yamma, inda aka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Lamarin ya tayar da hankula a ƙauyukan da ke kewaye, inda iyalai da dama suka kwana cikin fargaba.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikin waɗanda aka sace matasa ne da suka tafi gona domin yin roron wake lokacin da aka afka musu.

NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Shi ’Yan ta’adda sun kashe ɗan sanda a gidan DPO a Jigawa

Ya ce: “An fara kai hari ne ga mutane 15, wasu sun tsere, wasu kuma aka sake su ba tare da sharaɗi ba. Amma har yanzu mutum 11 suna hannun ’yan bindiga, kuma sun buƙaci a biya su kuɗin fansa na naira miliyan biyar,” in ji shi.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa a ranar Talata, ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazavar Jama’a/Sanga, Hon. Daniel Amos, ya bayyana satar mutanen a matsayin mugunta da rashin tausayi, tare da yin Allah-wadai da kai hari kan talakawa masu aikin halaliya.

“Muna buƙatar kara tsaurara tsaro, yin amfani da dabarun bayanan sirri, da ɗaukar matakan gaggawa da haɗin gwiwa domin kwantar da hankalin jama’a da kuma ceto waxa0nda aka sace,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
  • Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta
  • Sharhi:’HKI tana fama da karancin sojojin a dukkan rassan sojojin kasar’.
  • Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe 
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 165
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan 164
  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno
  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi