Hukumar Alhazai ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Maniyyatan Aikin Hajjin 2026 Su Fara Biyan Kudaden Ajiya
Published: 11th, August 2025 GMT
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta shawarci maniyyata aikin Hajjin shekarar 2026 da su fara shirin biyan kudaden ajiya.
Kiran ya biyo bayan taron da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta gudanar tare da hukumomin Alhazai na jihohi, inda aka bayar da shawarar ajiyar naira miliyan 8 da rabi ga masu niyyar zuwa aikin Hajji, kafin a sanar da hakikanin kudin aikin Hajjin shekarar 2026.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya shawarci wadanda ba su da fasfo da su gaggauta zuwa Hukumar Shige da Fice ta Kasa domin yin nasu, yana mai cewa shi ne ake amfani da shi wajen hada takardun tafiya.
Najeriya ta sake samun kujeru 95,000 daga Masarautar Saudiyya domin aikin Hajjin 2026, ana kuma sa ran jihar Kaduna za ta sake samun yawan kujerun da aka saba bata.
Yunusa Mohammed ya kuma bayyana cewa hukumar za ta sanar da maniyyata lokacin da za a fara yin rajista a Jihar Kaduna.
Safiyah Abdulkadir
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Sabbin Mataimaka Na Musamman A Karamar Hukumar Auyo
An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo.
Alhaji Binyaminu Kafur ya sake tabbatar da kudirin majalisar wajen yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da kayayyaki more rayuwa, don tabbatar da ganin kowa ya amfana da mulkin dimokuraɗiyya.
Ya yi kira ga jama’a da kada su gaji wajen yin addu’a domin samun nasarar shugabanni wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu.
Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Umar Jura ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa zabar mutanen da suka dace don yin aiki a lokacin mulkinsa.
Ya yi kira ga waɗanda aka naɗa da su bada haɗin kai tare da yin aiki tukuru don nuna amincewar da aka nuna gare su.
A madadin waɗanda aka naɗa, Malam Yakubu Muhammad Auyo da tsohon shugaban rikon ƙwarya Mika’ila Auyo sun gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa amincewa da su don yin wannan aiki.
Haka kuma sha alwashin haɗin kai domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Usman Muhammad Zaria