Aminiya:
2025-11-27@19:41:33 GMT

Tinubu ya umarci NAHCON ta ƙara rage kuɗin aikin Hajjin 2026

Published: 7th, October 2025 GMT

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026 nan take, kuma ta fitar da sabon farashin cikin kwana biyu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumar ta sanar da rafin kimanin N200,000 a kan farashin da maniyyata suka biya a bara.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya isar da umarnin shugaban kasa yayin wani taro da ya yi da shugabanni da mambobin hukumar NAHCON a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Litinin.

Shettima ya buƙaci a samu hadin kai tsakanin jami’an jihohi da na tarayya, ciki har da gwamnoni, wajen fitar sabon farashin da ya dace da yanayin tattalin arzikin ƙasar.

An fara bincikar Ganduje kan zargin karkatar da N4bn BBNaija S10: Ban san yadda zan kashe N150m da na lashe ba — Imisi Eniola

Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su gaggauta biyan kuɗaɗen da suka dace zuwa Babban Bankin Najeriya (CBN) domin tabbatar da cika tsare-tsare da kuma gudanar da aikin Hajjin cikin lumana.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya ce an gudanar da taron ne domin kammala shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, musamman batun farashin kujera.

Ya ce manufar gwamnati ita ce rage wa maniyyata kuɗin tafiya, la’akari da sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa a yanzu.

Hadejia ya ce, “Tattalin arziki yana ƙara samun daidaito, kuma darajar naira tana ƙaruwa sakamakon gyare-gyaren da gwamnati ke yi. Idan maniyyata sun biya tsakanin Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 a bara saboda tsadar Dala, yanzu da naira ta ƙara daraja, ya kamata a rage farashin.”

Ya ce an umarci NAHCON ta yi amfani da ainihin farashin canji na yanzu, yana mai cewa idan hakan ta tabbata, za a samu gagarumin sauƙin kuɗin aikin Hajji.

Shi ma Sakatare na NAHCON, Dakta Mustapha Mohammad, ya ce wannan umarni na shugaban ƙasa zai ƙara yawan maniyyata aikin Hajjin bana.

“Wannan ci gaba ne mai kyau. Rage kuɗin zai taimaka wa Musulmi da dama su samu damar yin wannan rukuni na addini. Za mu yi aiki tuƙuru tsakanin yau da gobe domin rage kuɗin zuwa matakin da kowa zai iya biya,” in ji shi.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi kuma Mataimakin Shugaban Ƙungiyar shugabannin Hukumomin Alhazai na jihohi da Abuja, Alhaji Faruk Aliyu Yaro, ya bayyana farin cikinsa da umarnin shugaban ƙasa.

“Mun yi matuƙar farin ciki da wannan mataki na shugaban ƙasa da mataimakinsa. Wannan zai taimaka wajen rage kuɗin aikin Hajji, kuma muna gode wa Allah da gwamnati,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: maniyyata rage kuɗin

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.

Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.

Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.

Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.

Ƙarin bayani na tafe…

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Jihar Jigawa Za Ta Rufe Karbar Kudaden Aikin Hajjin 2026 Ranar 24 Ga Watan Disamba
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS