‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta
Published: 20th, October 2025 GMT
“Rundunar ‘yansandan sashi ‘C’, Asaba, karkashin jagorancin CSP Ogbe Emmanuel, sun samu nasarar tare wata mota ɗauke da alburusai da aka nufi jihar Edo da su.
“A yayin da jami’an suke gudanar da binciken motoci na yau da kullum a kan babbar gadar Asaba, jami’an sun yi nasarar tare wata mota kirar ‘Toyota Hiace Hummer Bus’ mai lamba NGK 16 XB, wacce wani Ozoemenam Sylvanus ke tukawa.
“Yadda Direban, ke amsa tambayoyi cikin rashin nutsuwa, ya jawo jami’an suka fahimci cewa, ba shi da gaskiya inda suka gudanar da bincike sosai a kan motar, inda aka gano alburusai 400 da aka ɓoye a cikin motar.
“Wanda ake zargin da farko ya yi karyar cewa makullai ne aciki, amma sai aka ga alburusai bayan bude jakar, nan take aka kama shi, tare da haramtattun kayan da ya ɗauko.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Nijeriya Na Dab Da Fita Daga Halin Kuncin Talauci – Shettima October 17, 2025
Labarai Yadda ‘Yan Bindiga Ke Zafafa Hare-hare A Jihohin Arewa Maso Yamma October 17, 2025
Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025