Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga makarantun horar da ‘yan jam’iyya da su taka rawar gani wajen kyankyashe hazikai, tare da gabatar da shawarwari ga JKS.

 

Xi, wanda shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kiran ne cikin wani umarni da ya gabatar ga makarantun koyar da jagoranci na ‘ya’yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin.

(Mai fassara: Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5.

An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja

Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda.

Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa.

Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto ofishin ’yan sanda, inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.

Kakakin rundunar jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya shi.

Ya ce an kama Onwe da Chinyere Ugochukwu a ranar Juma’a a unguwar Azugwu, Ƙaramar Hukumar Abakaliki, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Matar Onwe, Philomena, ta ce ta yi mamaki matuƙa cewa mijinta ya sayar da jaririn nasu.

Ta bayyana cewa tun bayan haihuwarta, Onwe, ya ce zai kai jaririn wajen ’yar uwarsa domin ta sa masa albarka, sai dai daga baya aka gano cewa ya sayar da shi.

Ta ce, “Yaronmu bai wuce kwanaki biyar da haihuwa ba, amma mijina ya sayar da shi.

“Ban taɓa tunanin zai yi haka ba. Ina roƙon jama’a da masu hannu da shuni su taimaka min a wannan hali da na tsinci kaina.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana
  • Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
  • Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi
  • Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta
  • Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar.
  • Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
  • Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho
  • Putin: Natanyahu Yan Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba