Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Kafa Dokar Wuraren Tsaro A Makarantu
Published: 17th, October 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta fara aiki kan dokar da za ta kafa wuraren tsaro (safe spaces) a makarantu domin karfafa ilimin yara mata a jihar.
Shugaban Kwamitin Ilimi, Honarabul Mahmud Lawal, ya bayyana hakan a babban taro kan Ilimin Yara Mata da aka gudanar a Zariya, wanda Cibiyar Kula da Ilimin Yara Mata (CGE) ta shirya don tunawa da Ranar Yara Mata ta Duniya ta 2025.
Ya ce dokar, mai taken “Dokar Wuraren Tsaro a Jihar Kaduna, 2025,” za ta kare ‘yan mata daga cin zarafi, hana wariya, da samar da tsarin horaswa da rahoto a makarantu.
Daraktar CGE, Hajiya Habiba Mohammed, ta ce taron na da nufin kara karfafa ‘yan mata a matsayin shugabannin da za su kawo sauyi, musamman a lokacin rikice-rikice da suke fuskantar kalubale irin su aure da wuri da barin makaranta.
Ta ce cibiyarsu na ganin ilimi a matsayin makamin da zai bai wa ‘yan mata damar canza al’umma, kuma dokar majalisar za ta taimaka wajen tabbatar da shirye-shiryen su a makarantu.
A jawabinsa a wurin taron, Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Farfesa Adamu Ahmed, ya yaba da taken taron, yana mai cewa ya dace da kalubalen da ‘yan mata ke fuskanta.
Ya ce daya cikin kowanne ‘yan mata hudu a yankin na yin aure kafin shekaru 18, kuma har yanzu ba su da daidaiton damar ilimi kamar maza.
Farfesa Ahmed ya bayyana cewa ABU na kara yawan ‘yan mata da take karɓa, inda suka kai kashi 42 cikin 100, tare da kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki su kara zuba jari a ilimin ‘yan mata.
Ibrahim Suleiman
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yara Mata
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Cire Darasin Lissafi Zai Taimakawa Dalibai Shiga Jami’a
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cire darasin Lissafi daga jerin wajibcin da ake buƙata domin samun shiga manyan makarantu ya samu karɓuwa daga wasu ɓangarori na dalibai da malamai. Wasu dalibai sun nuna farin ciki da wannan mataki, suna ganin zai sauƙaƙa musu damar samun shiga jami’a da sauran manyan makarantu ba tare da shan wahalar lissafi ba.
Sai dai wasu masana sun bayyana cewa, duk da wannan sauƙin, ya kamata a yi taka-tsantsan saboda lissafi na taka muhimmiyar rawa wajen gina tunani da fahimtar ilimin fasaha, kimiyya da injiniya. Wannan ya sa ake tambaya ko cire lissafi daga wajabcin shiga manyan makarantu ba zai iya rage ingancin dalibai a nan gaba ba.
NAJERIYA A YAU: Shin Babu Wata Hanyar Magance Matsalolin ASUU Ne Sai Yajin Aiki? DAGA LARABA: Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan