Wani mutum ya ƙona tsohuwar budurwarsa a Oyo
Published: 17th, October 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo, ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruƙ da ake zargin ya bankawa tsohuwar masoyiyarsa wuta bayan da dangantakar su ta yi tsami.
Majiyar PUNCH Metro ta samu labarin a ranar Alhamis cewa, lamarin ya faru ne a barikin sojoji da ke Ibadan babban birnin jihar.
Jami’an tsaro sun kama ’yan bindiga 2, sun ƙone sansaninsu a Kogi Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert MacaulayWani ƙwararre a fagen yaƙi da ’yan tada ƙayar baya, Zagazola Makama wanda ya bayyana yadda lamarin ya faru a shafinsa na sada zumunta na X, ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa shi da budurwar sun yi rantsuwar cewa ba za su rabu ba.
Sai dai rahoton ya bayyana cewa, wanda ake zargin ya fusata ne bayan da dangantakar ta soyayya da ke tsakaninsu biyun ta lalace.
Lamarin da ya fusata saurayin wanda ake zargin ya zuba wa budurwar man fetur kafin ya banka mata wuta.
Bayan faruwar lamarin, jami’an soji da ke barikin sun ceto matar inda aka garzaya da ita zuwa asibiti kafin su kama wanda ake zargin.
Makama ya rubuta cewa, “Wacce aka kashen mai suna Omolola Hassan, an bada rahoton wanda ake zargin ya zuba mata man fetur sannan kuma ya ƙona ta, wanda aka ce ya fusata ne saboda taɓarɓarewar alaƙarsu.
“A cewar shaidu, jami’an soji da ke barikin sun yi gaggawar shiga tsakani tare da kashe wutar kafin a garzaya da budurwar zuwa asibitin Yawiri da ke Akobo don yi mata magani.
“Wanda ake zargin, wanda ya yi iƙirarin cewa dukkansu sun yi rantsuwar cewa ba za su rabu ba, a halin yanzu yana tsare.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda wanda ake zargin ya da ake zargin ya
এছাড়াও পড়ুন:
Uwar Gidan Shugaban Sin Ta Ziyarci Wajen Nune-nunen Karfafawa Mata Gwiwa A Bangaren Fasahohin Zamani
A nata bangare, Sima Bahous ta yabawa ci gaban da Sin ta samu wajen cike gibin fasahohi tsakanin jinsi, da ingiza ci gaban harkokin mata ta kowanne bangare da kare hakkoki da muradun mata.
Ta kuma yi kira ga kasa da kasa su hada hannu tare wajen karfafa gwiwar mata da ‘yan mata su samu ci gaba a zamanin amfani da fasahohi. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA