Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150
Published: 19th, October 2025 GMT
150-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda Abdurrahman dan Muljamul Muradi la’anenne ya sare Amirul muminina (a) a kansa a lokacinda yake sallah a cikin masallacinsa a Kufa.
Kafin haka, a hajjin shekarar da ta gabata ce, Khawarijawa suka gudanar da taron bayan aikin Hajji na shekara ta 39 bayan hijira suka tsaida kashe shuwagabannin musulmi wadanda suke jayayya a kan shugabanci a kan al-ummar Musulmi. Suka kuma yanke shawarar kashe Amirul muminina (a) da Mu’awiya da kuma Amru dan Asi.
Abdurrahman dan muljamil Muradi ne ya dauki alhakin kashe Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a), inda suka Sanya safiyar 19 ga watan Ramadan na shekara mai kamawa.
Almuradi ya shigo kufa a lokacinda lokacin aiwatar da shirinsu, ya kusa ya sauka a wajen diyar Amminsa Qatam, wacce kuma yake son aurenta, inda ta fada masa cewa ba zai auretba sai da sadakin da ta ambata, daga cikin har da kashe Imam Ali(a), saboda kissan mahaifinta da dan’uwanta a yakin Nehrawan.
Dan muljam ya buye mata kan cewa kashe shi (a) ne ya kawota kuma. Amma sai ta zuka shi, har ya amince da kashe Imam Ali (a) a matsayin bangare na sadakin aurenta.
A bangaren Imam Ali (a) kuma, a lokacinda masu tsaronsa suka fahinci cewa khawarijawa suna barazana ga rayuwarsa, sai suka bukace ya basu izinin kara masu tsaronsa amma ya ki amincewa, yana cewa All..ne ke kare shi, kuma a lokacinda ajalinsa ya zo zai dauke wannan kariyar, ta yanda ba wanda zai kare shi daga mutuwa.
Sannan a daren musibar ya kwana bai yi barci sosai ba, yana da zagayawa a tsakiyar gida yana Kallon sama yad ubi taurari, sai ya ce: Ban yi karya ba ba’a yi mani karya ba, itace daren da aka yi mani alkawari. Yana cikin wannan halin har lokacinda sahur ya yi, sai ya yi alwala, ya kama hanyar fita gida zuwa masallaci, sai dansa Imam Alhassan (a) ya fitarsa, sai ya fito a firgishe, ya tambaye shi abinda yasa zai fita ziwa waje a lokacin. Sai ya fada masa marfarkin da yayi kuma mafarkin ya hana shi barci. Ya fada masa, yadda ya ga mala’ika Jibrilu ya sauka kan dutsen Abukubais ya dauki duwatsu be ya je kan Ka’aba sai ya bugasu da juna suka zama gari, sai ya watsa garin a iska, babu gida a Makka da Madina face wannan garin ya shiga. Da yambayeshi fassarar mafarkin sai ya cewa: Idan mafarkin ya zama gaskiya, to za’a kashe babanka, kuma ba wani gida da zai rage a Makka da madina sai sun yi Bakinciki da kisana.
Da haka ya wuce masallaci, ya tada mutane masu barci a cikinsa don su yi addu’oi kafin gari ya waye. Mai littafin Istiw’ab ya bayyana cewa, Imam Alhassan (a) ya fito tare da shi, zuwa Masallaci, Sai ya data mutane sannan ya zo ya fara sallah, a wannan halin ne Abdurrahman dan Muljamul Muradi ya sareshi a kansa a kan goshinsa, har sai da takobinsa mai guba ya shiga cikin kwakwalwasa. A nan ne ya daga murya yana cewa {Na rantse da Ubangijin Ka’aba! na rabauta}.
Gaskiya ne Imam(a) ya rabauta, wani rabo ne yafi irin rabonsa? Hakaki an sare shi a lokacinda yake ganawa da Ubangijinsa, labbansa suna ambaton All..a cikin salla a kuma cikin masallaci dakin All… Gaskiya ne Imam (a) ya rabauta, wani rabo ne yafi irin rabonsa? Saboda a duk tsawon tarihin bil’adama, za’a ci gaba da gwama gaskiya da adalci da sunansa.
Bayan sautinsa (a) ya kai ko ina, sai mutane suka yi fitowa daga ko ina, zuwa masallaci. Daga cikin har da ‘ya’yansa (a). Ja’adatu dan Hubairah Almakhazumi, mahaifiyarsa Ummu Hani diyar Abutalib (a), yar’uwan Amirul muminin (a) ne ya fara zuwa kansa, ya sami kawunsa na rike da kansa yana cewa: {dan bayahude ne ya kashe ni, Abdurrahman dan Muljam, kada ya kubuce maku}.
Nan da nan suka taru a kansa suna kokarin tayi shi ya bada sallar asubaha, amma ya kasa. A lokacinda idonsa ya fada kan Imam Hassan (a) sai ya ce masa ya bada sallah. Imam (a) ya yi sallar a zaune, jina na kwarara da kansa. A lokacinda Imam Hassan (a) ya kamala sallah sai ya dauki kan babansa ya ajiye a kan cinyarsa sannan ya tambaye shi: Wa yayi haka da kai? {dan ba yahude, Abdrurrahman dan Muljam} sai yace: ta iya ya tafi?
Sai Imam (a) yace: Kada kowa ya je nemansa, zai bullo maku da wannan kofar} sai ya nuna kofar kinda. Sai mutane suka shagaltu da nemansa ta kofar sai ga shi gashi ana cewa an kamashi ta kofar. Aka daure hannunsa. aka kawo shi gaban Imam Alhassan (a) sai yace masa:
{Ya kai la’anenne! Ka kashe Amirul muminina kuma shugaban musulmi, wannan shi ne sakamakonka a gareshi bayan ya saukar da kai ya kusanto da kai, kai kuma da wannan zaka saka masa?}.
A wata ruwayar an bayyana cewa mutane sun gamu da shi a kofar Kinda suna da jifansa da duwatsu don su kama shi, har zuwa lokacinda Mughira dan Naufal dan Haritha dan Abdulmuttalib ya kama shi ya daga, ya buga shi da kasa sannan suka daure hannayensa suka kawo shi gaban Imam Alhassan (a). Akwai wasu ruwayoyin dangane da kama shi.
Sai ya Imam Al-Hassan ya juya wajen babansa ya na cewa: {Ya babana! Ga wannan makiyin All… makiyinka, dan Muljam, All..ya bamu iko a kansa.}.
Sai Imam (a) ya bude Idanunsa, ya kalle shi yana cewa {Lalle ka zo da mummunan abu, kuma al-amari babba, shin bana tausaya maka?, kuma ina gabatar da kai kan wasu a kyauta? Me yasa zaka saka mani da wannan sakamakon?} sai ya juya wajen Imam Alhassan (a) yana cewa {Ya da na! Ka tausayawa fursinanka, ka rahamce shi ka yi masa jinkai} Sai Imam (a) ya ce masa: {Ya baba! Wannan la’anen nen ya kashe ka, ya kuma jefa musiba a kammu, sannan kana umurtammu da tausaya masa?} .
Sai Amirul muminina (a) ya amsa masa da cewa
{Ya da na! Mu Ahlul Baitin Jinkai da rahama ne, (don haka) ka ciyar da shi daga abinda kake ci, ka shayar da shi daga abinda kake sha, idan kuma na mutu! To’ ka yi masa kisasi da kashe shi, kada ka yi muthla da mutumin, don lalle ni, na ji kakanka manzon All..(s) yana cewa, na gargadeku da yin Muthlah, ko da da kare mai cizo, idan kuma na rayu ni nafi sanin abinda zan yi da shi, kuma ni nafi cancantar Afwa, kuma mu Ahlul Baiti, bama karawa wanda ya cutar da mu sai Afwa da karamci.}
Sai Imam (a) ya bada umurni a kai shi gida, sai aka dauko shi, mutane suna ta kuka suna bin sa zuwa gida. Suna fada da babban murya an kashe limamin shiriya, an kasha limamin shiriya. Sai a cikin gida, yayansa mata da iyalansa suka tarbeshi da kuka,
A lokacinda ala kai shi ga masaukinsa, sai Imam Hassan (a) ya dube shi sannan ya ce masa. {Ya babana! Waye zai kula da mu bayanka? Lalle rashinka a wajemmu, kamar rashimmu ga manzon All..(s) ne}
Sai Imam (a) ya rungume shi, saboda kwantar da hankalinsa, yana cewa
{Ya da na! All..ya kwantar da zuciyarka da baka hakuri!,ya kuma girmama ladarka, da ladar yan’uwanka, gwagwadon rashi na a gareku}
Daga nan sai Imam Hassan (a) ya tara wata jama’a ta likitoci don jinyar mahaifinsa (s). Mafi kwarewa daga cikinsu shi Atheer dan amru Assakuni. Sai Atheer ya bukaci a kawo masa sabuwar jijiyar akuya da zafinsa, sai da aka kawo masa ya shigar da shi a cikin inda aka sareshi har ya shiga can ciki, sannan ya fiyar, ya dan dade kadan. Sai ya fito da shi, sai ya ga cewa nikekken farin kwakwalwansa ya na makale a jikin jijiyar.
Sai Atheer ya kidime, sai ya dubi Imam (a) yace masa, Ya shugaban muminai ka, ka yi wasiyarka, lalle zaka mutu. Sai Imam Hassan (a) ya juya ya dubi mahaifinsa, hawaye na kwarara a kan kumatunsa yana cewa {Baba na! ya karya bayana, ta yaya zan iya kallonka a irin wannan halin? }. Sai Imam ya kale shi yana fada masa a hankali
{Da na! daga yau, babu bakin ciki ko fargaba ga mahaifinka, a yau zan sadu da kakanka Muhammad Zabebbe(a), da kakarka Khadijatul Kubra, da mahaifiyarka Zahra (s) Lalle Hurun eeni suna sauraron gabatowar babanka, daga wannan lokacin, babu wata damuwa gareka, ya da na kada ka yi kuka}
Daga nan sai gubar ta shiga cikin jininsa, sai ya canza launinsa(s) zuwa fatsi fatsi. Ko yellow. Amma yana cikin nutsuwa yana ambaton All..yana kuma tawali’u zuwa gareshi yana kallon sama, yana addu’o’ii yana cewa
{Ya Uabangiji ina rokonka, kasancewa tare da manzanni da wasiyan, da kuma mafi daukakar Aljanna…}..
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Masani Kan Harkokin Tsaro Ya Ce: Makami Mai Linzamin Iran Kirar Ghadir Ya Aike Da Sako Ga Isra’ila October 18, 2025 Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: An Rusa Gaza Gaba Daya October 18, 2025 Joseph Kabila Ya Koma Kasarsa Domin Kalubalantar Hukuncin Kisa Da Aka Yanke Kansa October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Abdurrahman dan
এছাড়াও পড়ুন:
KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156
156-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, yadda Mu’awiya dan abusufyan ya kidemi bayan bayan ya sami labarin cewa an yiwa Imam Hassan bai’a a matsayin Khalifan musulmi a kufa, sannan ya kira taron mashawartansa suka zauna suka kuma fidda wassu al-amura guda biyu don fuskantar Imam Al-Hassan(a). Kuma sune, aika jasusu mai aiko masu labarai sirri daga kasar Iraki, musamman a biranen Kufa da Basra wadanda suka kasance manya-manyan garuruwan a lokacin a kasar Iraki.
Sannan na biyu kuma suna son sayan wasu manya-manyan shugabannin Iraki wadanda suke taimakawa Imam Alhassan (a) don su barshi shikadai, hakan zai tilasta masa ya mika kai ga mu’awiya dan Abusufyan.
Sannan ba tare da bata lokaci ba suka aika mutanen biyu zuwa kasar Iraki, daya a Basra da kuma a Kufa babban birnin daular musulunci karkashin Imam Hassan (a).
A lokacin da wadan nan ma’aikata biyu suka je inda aka turasu suka fara ayyukansu na leken asiri, sai asirinsu ya tonu, Imam Hassan (a) ya tura shurdatul Khamis suka bazu a cikin kufa har sai da suka zakulo jasusun Ma’awiya a cikin birnin suka kawoshi a gaban Imam Alhassan (a) wanda ya bada Umurni a kashe sai aka kashe shi.
Haka ya faru a Basra ma, inda Abdullahi dan Abbas ® ya sa aka nemo shi aka kuma kama shi aka kawo shi a gabansa ya bada umurni aka kasheshi.
Daga sai Imam Hasan (a) ya rubutawa Mu’awiya wasika, inda a ciki ya aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin kufa da Basar, sannan yayi masa barazana da yaki. Sannan ya fada masa cewa ya ji labarin ya nuna jin dadi da shahadar mahaifinsa Imam Ali (a).
Mu’awiya ya tsorata ya kuma mayar masa da amsa kan cewa bai ji dadin kasan mahaifinsa ba, amma yaki ya yi magana kan dan leken asirin da ya aika. Haka ma Ibnu Abbas ya rubutawa Mu’awiya wasika yana aibata shi da cusa dan leken asiri a cikin mutanen Basra. Shi ma mu’awiya ya mayar masa da amsa inda ya bayyana masa cewa Imam Alhassan (a) ya rubuta masa wasika irin tasa, yana aibata shi. Amma bai bayyanawa Ibn Abba kan cewa Imam Al-Hassan (a) yayi masa barazana da yaki.
Bayan haka sai Ibn Abbas ya rubutawa Imam Alhassan wasika inda a cikin yake bashi shawara yake kuma kodaitar da shi kan yakar Mu’awiya da kuma wasu dabarbaru da ya bashi. Ga nassin wasikar kamar yadda take.
:Bayan haka, Lalle musulmi sun mayar maka shugabancinsu bayan Aliyu (a), to zage dantse don yaki, ka yi jihadi da makiyinka, ka kusanto da mutanenka, wadanda suke da raunin Imani ka sayi addininsu don kare kanka daga cutar da kai. Ka kuma dora mutane daga manya-manyan gidaje da daukaka don sai danginsu su bika sannan kan jama’a ta hadu, …..
Ka yi koyi da abinda abinda ya zo daga wajen shuwagabanni adilai, suna cewa karya bata halatta sai a yaki… kuma ka san cewa abinda ya sa mutane suka kauracewa mahaifinka suka koma wajen Mu’awiya shi ne shi mai son daidaita rabo a tsakanin, sai wannan yayi masu nauyi.
Kuma ka san cewa kana yakar wanda ya yaki All..da manzonsa(a) a farkonmusulunci ne, har sai da al-amarin All..ya bayyana ya kuma sami rinjaye. A lokacinda aka kadaita Allah aka shafe shirka addini ya daukaka, sai suka bayyana cewa su masu Imani ne a gaban mutane, suka karanta Alkur’ani suna masu istahza’I da ayoyinsa, suka tsaida sallah suna cikin kasala, suna aikata sauran farillu ba da sonsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci