Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Mukaman Gwamnatin Tinubu inji Shugaban FCC
Published: 20th, October 2025 GMT
Mukaddashin shugaban hukumar daidaiton rabon muƙamai ta Ƙasa (FCC), Hon. Kayode Oladele, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ya samu kashi 56.3 cikin 100 na muƙaman gwamnatin tarayya da aka nada karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yayin da Kudu ke da kashi 43.7 cikin 100.
Oladele ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron bita na kwana guda kan “Ƙarfafa Jagoranci da Gudanarwa Bisa Renewed Hope Agenda.
” Ya ce wannan rabon yana nuna ƙoƙarin gwamnatin Tinubu wajen tabbatar da adalci da daidaiton wakilci kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
A cewarsa, Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma suna da ministoci mafi yawa, mutane 11 kowannensu, yayin da Arewa ta Tsakiya ke da 8, Arewa maso Gabas 7, Kudu maso Kudu 6, da Kudu maso Gabas 5. Bugu da ƙari, Arewa maso Yamma ce ke da yawan muƙaman jagoranci mafi girma (157), sai Arewa ta Tsakiya 139, da Kudu maso Yamma 132.
Ya tabbatar cewa hukumar FCC za ta ci gaba da bibiyar sabbin nade-naɗe don tabbatar da cewa dukkan yankunan ƙasar sun samu wakilci bisa RenewedHope Agenda na Shugaba Tinubu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Grossi: Za a iya warware batun Shirin nukiliyar Iran ne kawai ta hanyar diflomasiyya October 20, 2025 Trump: Shugabanin Hamas ba su da hannu a kisan sojojin Isra’ila 2 a Gaza October 20, 2025 Iran Da Azerbaijan Suna Gudanar Da Atisayen Hadin Guiwa Na Sojojin Ruwa A Tekun Caspian October 20, 2025 Gwamnatin Yamen Tana Tsare Da Ma’aikatan MDD 50 Ta Kuma Kwace Kayakin Aikinsu October 20, 2025 Gwamnatin Colombia Ta Bukaci Bayani Daga Amurka Kan Kashe Wani Dan Kasar A Tekun Carabian October 20, 2025 An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya October 19, 2025 Araqchi: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Nada Janar Christopher Musa Sabon Ministan Tsaro
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.
A wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin ya maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.
Janar Musa, mai shekaru 58, wanda zai cika 59 a ranar 25 ga Disamba, jajirtaccen soja ne da ya jagoranci rundunonin tsaro a matsayin Shugaban Hafsoshin Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025.
An haifi Janar Musa a Sakkwato a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya tafi College of Advanced Studies a Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Kwalejin Horas da matsakaitan Sojoji (NDA) duk dai a wannan shekarar, inda ya samu digiri na daya a fannin kimiyya a 1991.
An daga Janar Musa zuwa matsayin babban Laftanar (Second Lieutenant) a 1991, kuma tun daga lokacin ya yi aiki a manyan mukamai iri-iri. Daga cikin mukamansa akwai: Babban Jami’in Ma’aikata a bangaren Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81;
Kwamandan Bataliya ta 73;
Mataimakin Darakta, Kayayyakin Aiki, Sashen Tsare-tsaren Rundunar Soja;
Wakilin Sojin Kasa a Kwamitin Horaswa na Hedikwatar Soji ta Najeriya.
A 2019, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Babban Jami’in Ma’aikata na Horaswa da Ayyuka a Hedikwatar Cibiyar Sojin Kasa;
Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Lafiya Dole; da kuma Kwamandan Sashe na 3 na Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Yankin Tafkin Chadi (Multinational Joint Task Force).
A 2021, an nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, inda daga baya ya zama Kwamandan Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, kafin daga bisani Shugaba Tinubu ya nada shi Shugaban Hafsoshin Tsaro a 2023.
A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken kwarin gwiwa kan ƙwarewar Janar Musa wajen jagorantar Ma’aikatar Tsaro tare da ƙara inganta tsarin tsaron Najeriya.