NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyan ‘Ya’yan Su
Published: 25th, August 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye.
A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincabe sukayi wa iyaye yawa.
Daya daga cikin manyan sauyin da aka samu sun hada da aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda hakan a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawan da ‘ya’ya suke samu.
NAJERIYA A YAU: Ayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su a nan gaba DAGA LARABA: Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mataShirin Najeriya A Yau zai yi Nazari ne kan irin kalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyan ‘ya’yan su.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: iyaye Tarbiyya yara
এছাড়াও পড়ুন:
Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.
Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura IsaTrump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”
A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.
“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”
Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.
“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.
Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.