Araqchi ya isa Saudiyya don halartar taron gaggawa na OIC a kan Gaza
Published: 25th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi.
A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude a wannan Litinin bisa bukatar da Iran da kuma wasu kasashe gabatar na yin hakan.
A yayin taron na kwanaki biyu, mahalarta taron za su tattauna kan matsalolin jin kai a zirin Gaza, da yiwuwar kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palastinu, da kuma gurfanar da ‘yan sahayoniya masu laifi a gaban kotu.
Kungiyar ta OIC ta ce taron zai mayar da hankali ne kan zaluncin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza da nufin samun daidaiton baki da daukar matsaya guda kan martanin kasashe mambobi na kungiyar OIC.
Taron na Jeddah ya zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin mamaye birnin Gaza, tare da kara tsananta matakai da suke jefa al’ummar Gaza a cikin yunwa wadda kan yi sanadin mutuwar mutane a kowace rana.
Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran yana shirin ganawa da wasu takwarorinsa na kasashen musulmi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Zama Mai Biyayya Ga Amurka Ba August 24, 2025 An Gudanar Da Tarukan Makoki Shahadar Imam Ridha (AS) A Hubbarensa Da Ke Mashhad August 24, 2025 Aragchi: Batun ‘Isra’ila Babba” Mafarki ne Kuma Barazana Ce Ga Zaman Lafiya A Duniya August 24, 2025 Dakarun IRGC A Inan Iran Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Gwamnatin Iran August 24, 2025 Juyayin Shahadar Jagoran Shiriya Na Iyalan Gidan Manzon Allah Imam Ali Arridha {a.s} A Mash’had Sun Kai 3,500,000 August 24, 2025 Ma’aikatar Shari’a Ta Sojojin Kasar Iran Ta Ce; Dakarun ‘IRGC’ Barkono Ne A Idanun Makiya August 24, 2025 Makami Mai Linzamin Iran Kirar Qasim Basir Mafarkin Ban Tsoro Ne Ga Tsarin Tsaron Makiya August 24, 2025 Al’ummar Birnin Chicago Na Amurka Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa August 24, 2025 Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Bayyana Kakaba Yauwa A Gaza Da Laifin Yaki August 24, 2025 Ministan Tsaron Iran: Ba Mu Yi Amfani Da Manyann Makamanmu A Yaki Da Isra’ila Ba August 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu
Isra’ila ta kai hare-hare da dama a safiyar Alhamis kan yankunan gabashin Khan Younis, a kudancin Zirin wanda ke nuna yadda isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
A cewar kafofin watsa labaran Falasdinawa, sama da hare-hare 10 a jere Isra’ila ta kai.
Bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna makamai masu linzami na dira akan wuraren zama a gabashin birnin.
A lokaci guda, tankunan yaki na Isra’ila da motocin sulke sun yi ruwan bama-bamai a yankunan zama a gabashin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun kuma lalata gidaje da dama a gabashin birnin Gaza. Kasa da awa daya bayan haka, sojojin gwamnatin sun sake kai hari kan gidajen fararen hula a wannan yanki.
Hakazalika, sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hari kan yankunan arewa maso gabashin Khan Younis, da kuma unguwannin Ma’an, Sheikh Nasser, da Joura al-Lout a kudancin birnin.
Wannan mummunan harin sama ya biyo bayan wani mummunan harin bam da ya kashe mutane sama da 109, ciki har da akalla yara 52, a fadin yankin Falasdinawa da yaki ya daidaita.
Hamas ta zargi gwamnatin Sahyoniya da karya yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kungiyar ta yi kira ga bangaroron da suka shiga tsakani a yarjejeniyar tsagaita wutar, wato Masar, Qatar, Turkiyya da Amurka, da su dauki mataki nan take don matsa lamba ga gwamnatin isra’ila.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Adadin Falasdinawan Da Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Sun Haura 100 October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci