Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
Published: 17th, September 2025 GMT
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoSun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.
A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.
Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.
Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.
Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).
Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.
Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.
NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.
Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.
Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.
Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.
Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Najeriya Safarar Ƙwayoyi Saudiyya zargi safarar miyagun
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Gwarzo Ta Karfafa Yaƙi Da Miyagun Kwayoyi Da Shan Magani Ba Bisa Ka’ida Ba
Shugaban karamar hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya yi gargaɗi ga mazauna yankin kan mummunan ɗabi’ar shan magani ba tare da shawarar likita ba, yana mai bayyana hakan a matsayin babban haɗari ga lafiya da ka iya janyo matsalolin da ke barazana ga rai.
Dr. Tsoho ya yi wannan gargaɗi ne yayin da yake ziyarar duba asibitin Gwarzo General Hospital, inda ya gana da marasa lafiya, ya duba yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yabawa ma’aikatan lafiya bisa jajircewarsu wajen kula da jama’a.
Ya nuna damuwa cewa, yawancin matsalolin lafiya da ake fuskanta a cikin al’umma na faruwa ne sakamakon amfani ko wuce gona da iri wajen shan magunguna ba tare da shawarwarin ƙwararru ba.
Ya shawarci jama’a da su nemi shawarar likitoci da masu magunguna kafin su sha kowanne irin magani.
Shugaban karamar hukumar ya yi kira ga mazauna yankin da su rika ziyarar asibiti mafi kusa da zarar sun ji wata alamar rashin lafiya don samun kulawa cikin lokaci.
Ya tabbatar da cewa akwai likitoci da nas-nas ƙwararru a cibiyoyin lafiya na yankin da za su samar da ingantacciya kulawa.
Yayin da yake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta harkokin lafiya a dukkan yankuna, Dr. Tsoho ya ce hukumar tana aiki don samar da isassun magunguna, kayan aiki na zamani da kuma horaswa ga ma’aikatan lafiya.
Baya ga batun lafiya, shugaban ya kuma yi kira ga jama’a da su kasance masu lura da tsaro, tare da yin gaggawar kai rahoton duk wani motsi ko mutum da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin daukar mataki cikin lokaci.
Daga Khadijah Aliyu