Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Yanzu haka ana gudanar da taron bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayin duniya ta Majalisar Dinkin Duniya, karo na 30, wato “COP 30” a takaice, a birnin Belem na kasar Brazil, inda a ranar Juma’a 14 ga wata aka kira wani taro a gefe mai taken “Dabarun Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya”, don bayar da fasahohin Sin a fannin daidaita al’amura a kokarin sabawa da sauyin yanayi.

A wajen taron, shugaban tawagar kasar Sin a taron COP30, kana mataimakin ministan muhallin halittu na kasar, Li Gao, ya ce sauyin yanayin duniya wani babban kalubale ne da daukacin bil Adama ke fuskantarsa, inda a nata bangare, kasar Sin ta tsaya kan mai da hankali kan dukkan bangarorin dakatar da sauyin yanayi, da kokarin sabawa da shi. Kana kasar tana gudanar da gwaje-gwaje a biranenta 39 ta fuskar daidaita tsare-tsare don sabawa da sauyin yanayin duniya. Ban da haka, jami’in ya ce, kasar Sin na son karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashe, a kokarin tinkarar sauyin yanayi, da inganta fannin sabawa da sauyin yanayin duniya a kasashe daban daban.

Duk dai a wajen taron, Francesco Corvaro, wakilin kasar Italiya mai kula da batun sauyin yanayi, ya yi yabo ga kasar Sin bisa nasarorin da ta samu a kokarin sabawa da sauyin yanayin duniya, inda ya ce ci gaban da kasar Sin ta samu ya nuna makomar aikin tinkarar sauyin yanayi a duniya, kuma yana sa ran ganin Sin ta zama tamkar wata gada mai hada dukkan bangarorin kasashe masu tasowa da masu sukuni, ta yadda za a tabbatar da hadin gwiwar daukacin bil Adama a kokarin tinkarar sauyin yanayin duniya. (Bello Wang)

ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Matakin Amurka Na Ingiza Daftarin Tsawaita Aikin Tawagar UNISFA  November 15, 2025 Daga Birnin Sin Za A Wallafa Makalar Xi Game Da Gina Sabbin Ginshikan Samar Da Ci Gaban Kasa Masu Inganci November 15, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Sanya Hannu Kan Yarjejeniyoyin Cinikayya Na Biliyoyin Kudi Yayin Baje Kolin CHTF Na Kasar Sin
  • Shugaban Nukiliyar Iran Yace Amurka Da Israila Sun Shiga Sabon Mataki Mai Hadari
  • ’Yan bindiga 5 Sun shiga hannun ’yan sanda a Kebbi
  • DRC: An Kulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Tsakanin Gwamnati Da Kungiyar M23
  • Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30
  • NNPP Tana Da Ƙwarin Gwiwar Riƙe Kano Da Lashe Jihohin Arewa A Zaɓen 2027 – Ajuji
  • Meke Kawo Yanke Hukunce-hukunce Masu Karo Da Juna Daga Kotuna?
  • Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo
  • An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka
  • Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya