An tsara fara sauraron ƙarar a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2025, a gaban Mai Shari’a Yusuf Ubale.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja October 17, 2025 Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Masu Manyan Laifuka: Ta Bar Baya Da Ƙura October 17, 2025 Manyan Labarai Shugaban Ƙasa Zai Sake Nazari Kan Mutanen Da Aka Yi Wa Afuwa October 16, 2025.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano

Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano.

Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a.

’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika

Wannan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Lahadi.

Ya ce sojin ƙasa tare da haɗin guiwar sojin sama da ’yan sanda sun garzaya wajen, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da abin ya shafa.

Sai dai Zubairu, ya ce ’yan bindigar sun riga sun kashe wata mata mai shekaru 60 kafin sojoji su isa yankin.

Ya ƙara da cewa bayan harin farko da suka kai, sojojin sun bi sahun ’yan bindigar zuwa yankin Rimaye, inda suka yi musu luguden wuta, wanda hakan ya tilasta musu barin mutanen da suka sace.

Sai dai har yanzu ba a gano inda mutane huɗu da suka sace suke ba.

Bayanai sun nuna cewar bayan ’yan bindigar sun tsere, sun nufi Ƙaramar Hukumar Kankia da ke Jihar Katsina, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bibiyarsu.

Kwamandan rundunar, ya yaba da jarumtar  sojojin, ya roƙi jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihin bayanai a kan lokaci domin kawar da ’yan bindiga a jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocin Majalisar Dattawa
  • An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna
  • Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Kasafin Kudin 2026 Na Kimanin Triliyan Daya
  • Wani Dan Adawa Da Gwamnatin Paul Biya Ya Mutu A Gidan Yari A Kasar Kamaru
  • An kama ’yan bindiga 4 a Kano
  • MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar
  • Gwamnatin Kano Ta Kara Jaddada Dokar Haramcin Yin Haya da Babur a Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi 
  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano