Shagaya ya ce: “Wadannan hanyoyin da bankuna ke amfani da su wajen zaluntar kwastomomi na fiye da kima suna shafar ‘yan kasuwa, masu karamin karfi, dalibai da kuma kungiyoyin da ke cikin mawuyacin hali a wannan yanayin tattalin arziki mai tsanani. Idan ba a gudanar da bincike da daukar mataki cikin gaggawa ba, wannan matsala za ta ci gaba da rage amincewar jama’a ga tsarin banki tare da lalata kokarin shigar da jama’a cikin tsarin hada-hadar kudi.

Bayan amincewa da kudurin, Majalisar Wakilai ta umurci CBN da ta wallafa jerin caje-cajen da aka amince da su cikin sauki, tare da kakabawa bankunan da suka saba dokoki hukunci mai tsanani.

‘Yan majalisar sun kuma bukaci babban banki ya kafa wata hanyar karbar koke-koke wacce za ta kasance mai saukin amfani da inganci ga kwastomomi da abin ya shafa daga cajin da ba bisa ka’ida ba ko masu yawa.

Haka kuma, Majalisar ta umurci Hukumar Kula da Gasar Kasuwa da Kare Hakkin Masu Amfani (FCCPC) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da kamfe na wayar da kan jama’a a fadin kasa don ilmantar da ‘yan Nijeria game da hakkokinsu dangane da cajin banki.

An ba kwamitocin da ke kula da Dokokin Banki da Hukumomin Banki aikin gudanar da cikakken bincike tare da mika rahoto cikin makonni hudu don daukar mataki na gaba a majalisa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tawagar Bankin Duniya Ta Gana Da Gwamnan Katsina Kan Mayar Da ‘Yan Gudun Hijira Muhallinsu October 17, 2025 Labarai Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja October 17, 2025 Rahotonni Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya October 17, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotun ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike

Kotun Babban Majistare da ke Yaba ta bayar da umarnin a tono gawarwakin mutane 10 da gobara ta kashe a ginin Afriland Towers da ke Legas a ranar 16 ga Satumba, 2025, domin a gudanar da bincike a kansu.

Alkalin kotun, Mai shari’a Atinuke Adetunji ce ta bayar da umarnin a ranar Talata bayan ta samu labarin cewa an riga da binne wasu daga cikin waɗanda gobarar ta ritsa da su.

“Mai ƙorafi ya rubuta wa Gwamnatin Jihar Legas don neman izinin tono gawarwakin waɗanda suka mutu, sannan a gudanar da bincike a kansu,” in ji Mai Shari’a Adetunji.

Wannan umarni ya biyo bayan wata wasiƙa daga ofishin babban lauya Femi Falana da aka aike wa Babban Mai Kula da Gawarwaki na Jihar Legas, Mai Shari’a Mojisola Dada, a ranar 29 ga watan Satumba, 2025.

Femi Falana (SAN), ta hannun ofishinsa, ya shigar da ƙorafi ga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Legas, yana neman a gudanar da binciken gawarwaki don gano musabbabin mutuwar da kuma tabbatar da adalci.

A zaman farko na shari’ar, Mai Shari’a Adetunji ta umurci dukkan ɓangarorin da suka halarta da su gabatar da takardun da suka dace kafin zaman kotun na gaba.

Kotun ta kuma gayyaci hukumomi da kamfanoni da suka haɗa da bankin UBA da Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Ma’aikatar Kashe Gobara, Afriland Towers, United Capital, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Hukumar Tsaro ta Jihar Legas, da sauran masu ruwa da tsaki.

Adetunji ta ƙara da umartar mai ƙorafi da ya tuntubi iyalan waɗanda suka mutu don gano waɗanda ke da niyyar a tono gawar ’yan uwansu domin a gudanar da binciken gawarwaki.

Ta kuma nemi shaidun gani da ido da su bayyana don bayar da bayani kan abin da ya faru.

Lauya Yahaya Atata daga ofishin Falana ya shaida wa kotu cewa zaman na ranar an shirya shi ne don haɗa dukkan masu ruwa da tsaki da kuma fayyace yadda za a gudanar da binciken gawarwaki.

Sai dai alkalin ta lura cewa lauyoyin ba su shirya sosai ba, kuma ta jaddada cewa binciken ba zai ci gaba ba sai an gabatar da dukkan takardun da ake bukata.

Wani lauya mai wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu, A. O. Mema, ya shaida wa kotu cewa abokinsa, Peter Ifaranmaye, wanda shi ne manaja a Hukumar Tara Haraji ta Tarayya, an riga da binne shi.

Bayan wannan bayani, alkali Adetunji ta jaddada cewa yin binciken gawarwaki yana da matuƙar muhimmanci.

“Binciken gawarwaki muhimmin abu ne. Ba za mu iya gudanar da bincike ba sai an yi bincike don a gano hakikanin abin da ya faru,” in ji ta.

Kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba, 2025.

Gobarar ta tashi ne a ginin Afriland Towers, wani katafaren ginin kasuwanci da ke titin Broad a unguwar Legas Island, a ranar 16 ga watan Satumba, inda ta kashe akalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.

Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da sassafe, kuma ta bazu cikin ginin da sauri kafin hukumomin kasha gobara su samu damar shawo kanta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro
  • Fitar Da Kudi Ta Haramtacciyar Hanya Na Kara Dagula Matsalar Tattalin Arziki – IMF
  • Hukumar Gidan Yarin Kano Ta Tabbatar Da Dauke Abduljabbar Zuwa Abuja
  • ’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe
  • Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay
  • Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia
  • Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis
  • Kotu ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike
  • Kotun ta umarci a tono gawarwakin wadanda gobara ta kashe a Legas don yin bincike