JIBWIS FCT Ta Yi Taron Yaye Iyaye Mata Da Suka Kammala Koyon Sana’o’i
Published: 18th, October 2025 GMT
Shi ma a nasa jawabin yayin gudanar da taron, shugaban kwamitin Alhaji Abdullahi Abdulmalik Digi, ya ce, a shekaru hudu da ya yi yana jagorancin kwamitin sun yi abin da yakamata su yi, inda ya ce, a Azumin bara an dauki yara marayu 2000 da aka raba musu abinci da suka hada da buhunan shinkafa da kuma kayan Sallah da za su dinka, mata aka raba musu shadda mata kuma atamfofi inda jimillar kudin da aka kashe ya zama Naira miliyan 64.
Bayan wannan an kashe Naira milin 26 wajen biya wa yara 520 kudin makaranta, inda kowane yaro ake biya masa Naira dubu 50 a kananan hukumomi shida na FCT Abuja.
Sannan an kashe Naira miliyan 3 wajen taimakawa wasu da suka yi wa kwamitin hidima da suka rasu da kuma wadanda a yanzu ba su da lafiya, inda aka aika wa kowannensu Naira dubu hamsin-hamsin har gida.
Ya kara da cewa a wannan taro kuma, mata ne iyayen marayu su 120 aka koyawa sana’o’i, inda aka dauki kusana makonni uku ana koyar da su domin su samu ikon rike marayun da aka mutu aka bar musu. A wannan aiki na koyarwa an kashe Naira miliyan 4.675, a wurin sayen kayan aikin koyar da su da kuma zirga-zirga. Kananan hukumomin guda shida su ma sun kawo ta su gudunmawar ta Naira miliyan 2.4, suka idan an kammala basu horon kowacce a ba ta Naira 20,000 su rike kamar jari, jimillar kudin da kashe a wannan ba da horo na sati uku, ya kama Naira miliyan 7.75.
Jimillar abin da kwamitin ya kashe tun daga watan Azumin bara tun daga miliyan 66.2 kawo yanzu, an kashe Naira miliyan dari da dubu dariyu da saba’in da biyar N1.275 a shekarar bana kadai
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: an kashe Naira Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja
“Wannan mummunan lamari da ya faru a ranar 11 ga Oktoba, 2025, a Wawa Cantonment, Jihar Neja, ya haifar da yanayi mai cike da tashin hankali, inda mazauna sansanin suka shiga cikin mamaki kan yadda irin wannan abin takaici zai iya faruwa,” in ji wani bangare na sanarwar.
A cewar rundunar sojoji, an gano gawarwakin Lance Corporal Femi da matarsa a cikin gidansu dake gini na 15, daki mai lamba 24, Corporals and Below Kuarters, a cikin sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa sojan yana kan aiki a lokacin kuma ya nemi izini daga babban jami’i domin ya kula da wasu harkokin kansa kafin ya dawo aiki.
“Rundunar Sojin Nijeriya tana matukar bakin ciki kan wannan lamari, sannan tana taya iyalan, abokan aiki, da abokan marigayin jimami kan wannan babban rashi.
“Rundunar soji kuma tana addu’ar Allah ya jikansu cikin salama,” in ji Nwachukwu.
An ajiye gawarwakin marigayin, sannan an fara gudanar da cikakken bincike don gano dalilan da suka haifar da wannan abin takaici.
“Brigadier Janar Ezra Barkins, kwamandan 22 Armoured Brigade, ya tabbatar wa jama’a cewa sakamakon binciken zai kasance a bayyane kuma za a duba shi sosai, tare da daukar matakan da suka dace don hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA