Leadership News Hausa:
2025-10-18@16:35:23 GMT

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Published: 18th, October 2025 GMT

Lewandowski Ba Zai Buga Wasan El Classico Ba

Dan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ba zai buga wasan hamayya tsakanin FC Barcelona da Real Madrid wanda ake yi wa take da El Classico ba bayan da zakarun na Sifaniya suka gano cewa yana fama da rauni a kafarsa ta hagu, dan wasan mai shekaru 37 ya samu rauni ne a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Poland ta buga da kasar Lithuania ranar Lahadi.

Lewandowski yana da tsagewar tsoka a cikin femoris na cinyarsa ta hagu,” in ji Barcelona a cikin wata sanarwa, yayin da kafofin yana labarai na Sifaniya suka ruwaito cewa zai iya yin jinyar makonni hudu zuwa shida, Barcelona za ta kara da Real Madrid wadda ke jagorantar gasar La Liga a wasan Clasico a Santiago Bernabéu a ranar 26 ga Oktoba, yayin da kuma dan wasan ba zai buga wasannin gasar cin kofin zakarun Turai da za ta yi da Olympiakos da Club Brugge da sauran wasannin ba.

Mai tsaron gida Joan Garcia da dan wasa Dani Olmo suma ba za su buga wasan na El Classico tare da Real Madrid ba, amma matashin dan wasan gefe Lamine Yamal ya dawo atisaye ranar Litinin bayan ya fara murmurewa daga raunin da ya samu, an tura dan wasan Barca Ferran Torres gida daga sansanin ‘yan wasan kasar Sifaniya saboda rashin jin dadin jiki, amma kungiyar ta tabbatar a ranar Litinin cewa bai samu rauni ba,

Torres ya jagoranci Barca a lokuta daban-daban a kakar wasa ta bana, yayin da Lewandowski ya kan yi wasa a matsayin wanda zai maye gurbinsa daga benci.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa October 16, 2025 Wasanni Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc  October 15, 2025 Wasanni Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Benin A Uyo October 14, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu Murnar Ranar Haihuwa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu murnar zagayowar ranar haihuwarsa, inda ya bayyana shi a matsayin ma’aikaci mai tawali’u, mai aminci, kuma mai kishin kasa wanda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban kasa abin a yaba ne.

 

Shugaban ya yaba wa Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma kuma shugaban kwamitin majalisar dattijai kan asusun gwamnati bisa “kishin sa na gaskiya, rikon amana, tsarin kasafin kudi, da dokoki masu tasiri da ke magana kan makomar kasarmu.”

 

Da yake karin haske kan tarihin Sanata Wadada a Majalisar Dokoki ta kasa, Shugaba Tinubu ya lura cewa “a cikin shekaru biyu kacal a Majalisar Dattawa, kun bambanta kanku a cikin doka, wakilci, da kuma kulawa a matsayin daya daga cikin masu basirar majalisa, mai taka rawa, kuma abin koyi ga matasa masu tasowa.”

 

Shugaban ya bi sahun al’ummar Nasarawa ta Yamma, ‘yan uwa, abokan arziki, da abokan zaman Sanatan wajen taya shi murna, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa karfin gwiwa, da hikima da kuma koshin lafiya domin ya ci gaba da yi wa kasa hidima.

 

Bello Wakili

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iwobi Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Firimiya
  • Marzieh Jafari  Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa A Nahiyar Asia
  • Tsohon Ɗan Wasan Dambe, Ricky Hatton Ya Rataye Kansa
  • An kama ɓarayi da motocin da aka sace a Gombe
  • Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Sanata Ahmed Wadada Aliyu Murnar Ranar Haihuwa
  • Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadi
  • Majalisar Dattawa za ta tantance Amupitan a ranar Alhamis
  • Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc