Matasa sun yi zanga-zanga kan yunwa a Adamawa
Published: 18th, October 2025 GMT
Wasu gungun matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Yola da ke Jihar Adamawa, don jan hankalin gwamnati kan ƙaruwar talauci da yunwa.
Masu zanga-zangar sun bin manyan tituna, inda suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar da su ɗauki matakan rage wahala, rashin aikin yi da matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.
Shugaban Ƙungiyar MOTION na Jihar Adamawa, Mista Musa Andrew, ya ce zanga-zangar ta zama dole ne saboda halin matsin tattalin arziƙi da ke ƙara taɓarɓarewa.
“Mun fito ne don mu yi magana kan rashin adalci da wahala, ga yunwa na ƙaruwa,” in ji shi.
“Yawancin ’yan Najeriya suna kwanciya ba tare da cin abinci ba, yara kuma suna zuwa makaranta ba tare da sun ci abinci ba. Rayuwa ta yi tsada sosai.”
Ya kuma bayyana damuwa kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara musamman a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
“Mun gaji da rashin tsaro a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar nan. Yawancin matasanmu, sojoji da ’yan sanda suna rasa rayukansu a kullum,” in ji shi.
Andrew, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakai don tabbatar da daidaiton rabon albarkatun ƙasa tare da gyara tsarin fansho wanda ya ce yana cike da cin hanci.
“’Yan sanda suna yin ritaya suna komawa gida da kashi 40 cikin 100 na fanshonsu, sauran kuma ana wawurewa. Ba za mu lamunci wannan zalunci ba,” a cewarsa.
Ya kuma nemi a bai wa matasa dama su shiga harkae shugabanci.
“Yawancin shugabanninmu sun fara shugabanci tun suna da shekaru 20, amma yanzu sun ƙi bai wa matasa dama. Shugabanci ba gado ba ne,” in ji shi.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, Hajiya Blessing Musa, ta koka kan tsadar rayuwa, inda ta ce a yanzu magidanta da dama ba sa iya sayan kayan abinci.
“Yunwa tana kashe mu. Farashin kayan abinci ya yi tsada sosai, kuma ba mu da kuɗin saye,” in ji ta.
“Wani mutum ya roƙe ni na sayi shinkafa kan Naira 1,400 amma ba zan iya saya ba. Sama da kashi 70 cikin 100 na ’yan Najeriya suna rayuwa cikin talauci.
“Ba za mu iya tura ’ya’yanmu makarantu masu kyau ba, saboda na gwamnati ba sa aiki yadda ya kamata.”
Ta roƙi gwamnati ta ɗauki matakai don rage talauci, sauƙaƙa farashin abinci da kuma inganta makarantun gwamnati.
Mista Dennis Babangida, wani jagoran matasa, ya bayyana cewa yunwa ta yi ƙamari a Arewa kuma abun damuwa ce.
Ya nemi gwamnati ta tallafa wa manoma da kuma ƙirƙiro ayyukan yi domin rage talauci.
“Farashin taki ya yi tsada sosai, manoma ba sa iya saya. Idan gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma da kuma samar da ayyukan yi, hakan zai rage talauci da yunwa,” in ji Babangida.
Ya kuma gargaɗi gwamnati cewa idan ta ci gaba da yin shiru, matsalar yunwa na iya haddasa rikice-rikice a tsakanin jama’a.
“Jama’a suna jin yunwa kuma suna jin haushi. Gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki kafin lamarin ya fi haka muni,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa Gwamnatin tarayya yunwa zanga zangar gwamnati ta
এছাড়াও পড়ুন:
Zanga-Zangar Miliyoyi A Yemen Ta Jaddada Alkawari Ga Shahidai Da Ci Gaba Da Goyon Bayan Al’ummar Falasdinu
Zanga-zangar miliyoyin mutane a birnin Sana’a na sabunta alkawarin da aka yi wa shahidai tare da tabbatar da shirin tallafawa Falasdinu
Babban birnin kasar Yemen, Sana’a, ya halarci wani tattaki na miliyoyin mutane a yau Juma’a mai taken “Shekaru biyu na bayar da gudummawa… da aminci ga jinin shahidai”, tare da tabbatar da gwagwarmaya na goyon bayan al’ummar Falastinu tare da sabunta alkawarin bin tafarkin shahidai da azama.
Daruruwan jama’a a dandalin Al-Sabeen a lokacin tattakin bayar da amana ya kunshi zurfafa fahimtar al’amuran al’umma. Sun yi nuni da cewa al’ummar Yemen duk da killacewar wuce gona da iri, amma suna nan a fagagen alfahari da daukaka, da tsayin daka kan tafarkinsu na imani da jihadi.
Daruruwan mutane daga cikin miliyoyin ne suka daga tutocin kasar Yemen da na Falasdinu, da kuma hotunan Shahidan gwagwarmaya misalign Manjo Janar Mohammed Al-Ghamari da shugabannin shahidan da suka hau kan hanyar Qudus. Sun kuma rera taken da ke tabbatar da shirye-shiryensu na tunkarar makiya yahudawan sahayoniyya idan har suka dawo da kai farmaki kan Gaza da al’ummar Falastinu ta hanyar karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Sun nuna alfahari da girmamawa ga irin gagarumin sadaukarwar da aka bayar na goyon bayan al’ummar Falastinu da ‘yan uwansu a Gaza tun bayan kaddamar da harin “Ambaliyar Al-Aqsa” da kuma girmama shahidan da suka tashi tsaye wajen kare kasarsu da martabarsu da mutuncinsu da kuma tsarkakar Musulunci.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Yemen Ta Sanar Da Nadin Sabon Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Kasar October 17, 2025 Iran Tayi kira Da A Warware Rikici Tsakanin Afghnistan Da Pakistan Ta Hanyar Diplomasiya October 17, 2025 Hizbullah: Amurka ِDa Isra’ila Ba za Su Iya Yin Nasarar Akanmu ba. October 17, 2025 Majalisar Dattawa Ta Amince Da Amupitan A Matsayin sabon Shugaban INEC October 17, 2025 Shugaban Kasar Sudan Yana Ziyarar Aiki A Kasar Masar October 17, 2025 Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Hrin Wuce Gona Da Iri Na HKI October 17, 2025 WSJ: Amurka Tana Tara Rundunonin Yaki A Zagayen Kasar Venezuela October 17, 2025 Shugabannin Kasashen Amurka Da Rasha Za Su Hadu A Kasar Hungary October 17, 2025 Larijani ya isar da sakon Ayatullah Khamenei ga Putin a ziyarar da ya kai Rasha October 17, 2025 Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina October 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci