Rashin tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewa
Published: 18th, October 2025 GMT
Aƙalla makarantun gwamnati 188 ne aka rufe sakamakon mtsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya. Binciken da wakilanmu suka gudanar ya nuna cewa, an rufe makarantu da dama a yankin saboda hare-haren da ’yan bindiga suke kai wa ƙauyukan da kuma yadda wasu makarantun ke zama a matsugunin mutanen da rashin tsaro ya raba da muhallansu.
Wakilanmu sun gano aƙalla an rufe makarantu 55 a Jihar Binuwai, 52 a Jihar Katsina, 39 a Jihar Zamfara, 30 a Jihar Neja, 6 a Jihar Sakkwato da kuma 6 a Kaduna, baya ga makaratu 52 da 55 da aka rufe a jihohin Katsina da Benuwai. Wannan adadi na iya zama sama da haka, saboda ba za a iya isa ga wasu wuraren ba.
Daga cikin makarantu 39 da aka rufe a Zamfara, 20 na firamare ne, yayin da 19 na sakandare ne. A Neja an rufe firamare 18, sakandare 1 da kuma makarantun makiyaya 11. An rufe makarantun sakandire uku, kwalejojin fasaha 2 da makarantar firamare 1 a Jihar Sakkwato.
Hakan na faruwa ne, duk da wani rahoto ya nuna cewa, wasu daga cikin jihohin ne ke da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.
Ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4 Bakatsine ya ƙera motar yaƙi Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan AmurkaA rahoton binciken ICIR ya ce, Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da yara ba sa zuwa makaranta a duniya, inda aka ƙiyasta tsakanin miliyan 10 zuwa 20, a cewar rahoton Hukumar Kula da Ƙananan Yara ta UNICEF na shekarar 2024.
Tsarin ilimin ƙasar musamman yana fuskantar matsala mai ban tsoro, inda yara miliyan 10.2 na shekarun shiga makarantar firamare da kuma wasu miliyan 8.1 na ƙananan makarantun sakandare ba sa zuwa makaranta.
Alƙaluman da Hukumar Kula da Harkokin Ilimi ta ƙasa (NMPI) ta fitar, ya nuna cewa, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta ya kai miliyan 1.4 a Katsina, wanda ya kai kashi 45.9 na yawan mutanen da suka kai lokaci zuwa makaranta a jihar.
Jihar Kebbi na da kashi 67.6 bisa 100 na al’ummarta masu zuwa makaranta, inda sama da yara miliyan 1.06 ke yin karatu a wajen aji.
Sakwato tana da yara miliyan 1.25 da ba sa zuwa makaranta. Wannan na nufin Katsina da Sakwato da Kebbi ne ke jagorantar yawan yaran da ba su zuwa makaranta a Nijeriya.
A cewar ƙididdiga, Katsina na da makarantun firamare 3,375 a shekarar 2018/2019.
Makarantun gwamnati da dama a faɗin jihohin Sakwato da Zamfara da Katsina da Neja da Kaduna da Kebbi da Benuwai
Da Kwara sun kasance a rufe tsawon shekaru, wasu na tsawon watanni ko makonni, bayan rufe su. Sakamakon hare-haren ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da Ansaru da Lakurawa da Mahmuda da ‘yan ta’adda.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, hare-haren ya tilasta wa dubban yara barin makaranta, inda wasu ajujuwa suka zama matsuguni na ’yan gudun hijira da sansanin jami’an tsaro. Yayin da wasu ɗaliban aka mayar da su garuruwa, inda aka haɗe su da makarantun da ake da su, wasu kuma sun daina karatu.
Hakan dai ya zo ne kamar yadda masana ilimi suka yi gargaɗin cewa, tsawaita rufe makarantun karkara, zai ƙara jahilci da talauci.
Sakkwato: An rufe makarantu 6A Jihar Sakkwato, manyan makarantun kwana da suka haɗa da Kwalejin Fasaha ta Gwamnatin Tarayya da ke Wurno da makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke Raɓah da Makarantar Sakandaren Kimiyyar Mata ta Gwamnati da Illela da makarantar Olusegun Obasanjo Technical College da ke Bafarawa da kuma Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Adamu Mu’azu da ke Goronyo sun kasance a rufe shekaru da dama, bayan da gwamnatin tsohon Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ta rufe.
A Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, mazauna ƙauyukan da suka rasa matsugunansu, yanzu sun mamaye gine-ginen makarantu da daddare, kuma suna barin su da rana domin yin karatu. A unguwar Manawa da ke Ƙaramar Hukumar Isa, makarantar firamare ɗaya tilo ta shiga hannun ’yan bindiga da ke amfani da ita wajen hutawa kamar yadda Aminiya ta gano.
“Wannan babban rauni ne ga makomar ’ya’yanmu, dole ne gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki na gaggawa don maido da tsaro da mayar da yaran makaranta”, in ji wani tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Goronyo, Alhaji Zakari Shinaka.
“Akwai makarantu da yawa a Sabon Birni da suka daina aiki, saboda ɗaukacin al’ummomin da ’yan bindiga suka raba da muhallansu,” in ji wani mazaunin garin da ya buƙaci a sakaya sunansa.
Ya ƙara da cewa, “Waɗanda suka rasa matsuguninsu a yanzu suna zama a hedikwatar ƙaramar hukumar, sun mamaye gine-ginen makarantu da daddare.
Yunƙurin tuntuɓar kwamishinan ilimi da makarantun sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala, bai samu ba, yayin da sauran jami’an gwamnati suka ƙi cewa komai.
Zamfara: An rufe makarantu 39A Jihar Zamfara makarantu da dama sun kasance a rufe sama da shekaru shida a ƙananan hukumomin da ke fama da ’yan bindiga, kamar Anka da Tsafe da Ƙaura Namoda. Kaɗan ne kawai a cikin garin Anka ke aiki a ƙarƙashin kariyar sojoji.
Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da Makarantar Firamare ta Kawaye da Makarantar Dawangiye da Makarantar Firamare ta Tubuki da Makarantar Firamare ta Tungar Ku da Makarantar Firamare ta Duza da Makarantar Firamare ta Tungar Mata da Makarantar Firamare ta Tamani da Makarantar Firamare ta Makakari da Makarantar Firamare ta Sunke.
Sauran sun haɗa da: Makaramtar Sabon Birni GDSS da Makarantar Firamare ta Sabon Birni Jar Kuka da Makarantar Firamare ta Abare da Makarantar Firamare ta Duhuwa da Makarantar Firamare ta Mayanchi da Makarantar Firamare ta Fangaltama da Makarantar Firamare ta Dareta.
Wani mazaunin garin Anka, mai suna Malam Hassan Isa ya ce, “yaranmu da yawa sun daina zuwa makaranta a wannan yanki, tun shekaru bakwai da suka gabata. Kaɗan ne daga cikinsu, aka mayar da su wasu makarantun da ke garuruwan da ke da zaman lafiya. Muna cikin wani mawuyacin hali.
A garin Tsafe dai yanzu sojoji sun mamaye makarantu irin su GSS Danjibga da GSS Yankuzo da Makarantar Firamare ta Makera da GSS Wanzamai da Makarantar Firamare ta Sugawa.
Wani mazaunin garin Tsafe, Ali Yusuf Mai Goro ya shaida wa Aminiya cewa, an mayar da wasu makarantun da abin ya shafa masaukin jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da ’yan sandan tafi da gidanka.
“Sojoji sun ƙwace Makarantun Danjibga da Yankuzo da Wamzamai, amma an bar na Makera da Sungawa, babu komai tsawon wannan lokaci. Yaranmu musamman ɗaliban firamare sun daina zuwa makaranta, yayin da ’yan sakandire kaɗan ne suka samu damar ci gaba da karatunsu a wasu wurare”, Inji shi.
Wani mazaunin garin Ɗan Isa, Muhammad Shehu Mai Taya ya ce, an rufe makarantun firamare biyu da makarantun sakandare 12 da ke gundumar tun a shekara ta 2023.
Ya ce, yaran yankin sun bar makarantu saboda ’yan fashi. “A duk faɗin yankin Ɗan Isa, babu wata makarantar firamare ko sakandare a halin yanzu. Babban abin da ke damun mu, ba makaranta ba ce, zaman lafiya, domin idan babu shi, ba za mu iya yin komai ba. Zaman lafiya shi ne gaba da komai, don haka yaranmu sun daina zuwa makaranta, domin kare lafiyarsu,” in ji shi.
An rufe makarantu da dama a KatsinaJihar Katsina ma ta sami wannan matsala ta rufewar makarantu. A wani bincike na shekarar 2024 da Cibiyar Oɗford Policy Management, wadda Hukumar Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ke tallafawa, ya nuna cewa, an rufe makarantu 52 a ƙananan hukumomin Batsari da Faskari da Ƙanƙara. A cikin waɗannan makarantu guda 9 kawai aka buɗe. A tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025 a ƙalla an sace ɗalibai 330 da malamai 14. Sannan an kashe 5 a waɗannan ƙananan hukumomi.
Lamarin da ya fi ɗaukar hankali shi ne sace ɗaliban Kankara na shekarar 2020, inda aka yi garkuwa da ɗalibai sama da 200.
Aminiya ta ruwaito, wata makaranta da ke Marabar Ɗan Ali da ke Ƙaramar Hukumar Danmusa ta koma sansanin sojoji, lamarin da ya tilasta wa ɗaliban ko dai su koma makarantar ƙauye da ke maƙwabtaka da su karatu a cikin wani gida mara rufi, wanda bai kammala ba ko kuma su bar karatun gaba ɗaya.
Kwanan nan Gwamna Dikko Radda ya yarda cewa, rashin tsaro ya gurgunta makarantu da kasuwanni da filayen noma a ƙananan hukumomi 8 da suka haɗa da Jibiya da Danmusa da Safana da Sabuwa.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da wani shiri na wata 18 da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ɗauki nauyin yaƙi da tashe-tashen hankula da magance rikice-rikice, gwamnan ya ce, gwamnatinsa na bin hanyar tattaunawa domin daƙile matsalar rashin tsaro. Ya ƙara da cewa, yarjejeniyar zaman lafiya da al’umma suka yi ta haifar da sakamako a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari da Danmusa da Kurfi, yayin da ake ci gaba da tattaunawa a Ƙanƙara da Safana.
An rufe Makarantu 30 a NejaA Jihar Neja, an rufe makarantu kamar Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara, inda aka sace ɗalibai da ma’aikata 27 a shekarar 2021, inda aka mayar da ita zuwa sansanin soji.
Sauran Makarantun da abin ya shafa sun haɗa da Cibiyar Bunƙasa Ilimi ta Malamai da ke Dandaudu a Ƙaramar Hukumar Munya da Mamman Kontagora Technical College da ke Pandogari a Ƙaramar Hukumar Rafi.
A duk faɗin ƙananan hukumomin Rafi, Shiroro da Mariga da ke jihar sama da makarantu 20 ne babu kowa a cikinsu, ciki har da Makarantar Central Firamare da ke Allawa da Makarantar Firamare ta Gurmana da Makarantar Firamare Kwaki a Allawa da makarantu uku sun kasance babu kowa tun 2024 lokacin da sojoji suka janye.
Malamai sun ce wasu lokuta yara kan shafe makonni uku zuwa biyar a gida a duk lokacin da aka ga ’yan fashi a yankunan da ke kewaye da yankin.
Gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago ya yi alƙawarin mayar da makarantun marasa galihu zuwa “makarantar mega” da ke Minna da sauran shiyyoyin tsaro, amma har yanzu shirin bai fara ba.
Mazauna yankin sun ce, ’yan bindiga sun tilasta rufe makarantu 11 na makiyaya a Ƙaramar Hukumar Rafi, yayin da akasarin ɗaliban sun daina karatu.
A Ƙaramar hukumar Shiroro, Makarantar Central Primary da ke Allawa da Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Allawa da Makarantar Firamare ta Model da ke Allawa da Makarantar Firamare da ke Gyaramiya da Makarantar Firamare da ke Samunaka da Makarantar Firamare ta Gurmana da Makarantar Firamare ta UBE da ke Plalali da Makarantar Firamare ta Bassa da Makarantar Firamare ta Kwaki da Makarantar Firamare ta Chukuba da Makarantar Firamare da ke Rumace.
A Ƙaramar Hukumar Mariga, makarantun da aka tilasta wa rufewa saboda matsalar rashin tsaro sun haɗa da Makaranntar Central Primary da ke Ragada da Makarantar L.E.A Primary da ke Kadago-Gari da Makarantar L. E. A Primary da ke Faransi da Makarantar Central Primary Mazame-Gari da Makarantar L.E.A Primary da ke Masawaci da dai sauransu.
“Duk waɗannan makarantu an rufe su na tsawon lokaci, saboda fargabar ’yan fashi a cikin makarantun da aka jera, Makarantar Primary Ragada da sauran makarantun firamare da ke Ukari aka buɗe kuma ko a makarantun biyu ba a samu kwanciyar hankali ba, domin duk lokacin da ’yan fashi suka zagaye yankinmu, sai su shafe makonni uku zuwa biyar ba tare da halartar ajujuwa ba”, kamar yadda ɗaya daga cikin malaman ya shaida wa Aminiya.
Da aka tuntuɓi Darakta Mai Kula da Jarrabawa a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja, Asabe Abdullahi ta ce, ana buƙatar umarni daga babban sakatare kafin yin magana kan lamarin.
Kaduna: Garuruwa sun tashi an bar makarantuA Ƙaramar Hukumar Kajuru, ƙauyuka irin su Karimai da Cibiya sun zama ba kowa, inda a ƙalla makarantu shida suka zama kufai. A ƙananan hukumomin Chikun da Birnin Gwari, an mayar da ɗaliban makarantun da aka yi watsi da su zuwa garuruwa kamar Udawa, inda aka matse wasu a ajujuwa da yawa.
Wani Shugaban matasan Yuhana Kufana, ya ce akwai ƙauyuka kamar Karimai da Cibiya a gundumar Maro da ke Kajuru inda aka daina zuwa makaranta, saboda mazauna waɗannan garuruwan duk sun yi gudun hijira, saboda matsalar rashin tsaro.
Ya ce, “duk da haka duk makarantun da ke mallakin gwamnati ne, kusan makarantu 6 a wannan gundumar ba sa aiki, saboda iyaye da iyalan da suka taɓa zama a yankunan duk sun yi gudun hijira, yawancin mazauna garin sun yi ƙaura zuwa garin Mararaban Kajuru da garin Kufana don zama. A yankin Kujeni ma makarantun babu kowa, saboda mazauna yankin sun yi gudun hijira. Hakan yana nufin duk inda iyayen suka koma, yaransu ba za su iya komawa makaranta ba.
“Sai dai har ya zuwa yanzu ba mu san abin da ke faruwa da malaman da aka tura makarantun da aka yi watsi da su ba, ko hukumomin ilimi sun mayar da su wasu makarantun ba mu sani ba. Yana da kyau a lura cewa, gwamnatin jihar ba ta sanar da rufe waɗannan makarantu a hukumance ba saboda rashin tsaro.
Amma tunda ba a bar ɗalibaiA cikin al’umma ba, makarantun sun zama ba su aiki, gwamnati ba ta ce ta rufe su ba, amma gaskiyar magana ita ce ba a bar mazauna ƙauyukan ba, makarantun ba su aiki. Wannan shi ne halin da muke fuskanta a halin yanzu’’.
Wani Shugaban al’umma a garin Udawa da ke Ƙaramar Hukumar Chikun, Imam Muhammadu Udawa ya ce, akwai makarantun LEA a Labi da Anguwar Yako da Manini da Gwarso da Mil Biyu da Hayin Mato, waɗanda duk ƙauyukan da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari, waɗanda yanzu haka mazauna garin sun koma garin Udawa tare da ’ya’yansu, domin ci gaba da karatunsu.
A cewarsa, yawancin ƙauyukan sun kasance ba kowa a shekarun baya, saboda rashin tsaro. Kuma tun daga lokacin, makarantun da ke cikin waɗannan al’ummomin sun kasance babu kowa. Ya ce, yawancin ɗaliban sun warwatsu a sauran al’umma.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kaduna, Ahmed Maiyaki bai amsa kiran waya ba ko kuma amsa sakon tes da WhatsApp da Aminiya ta aika a layin wayarsa, don jin ta bakinsa.
Kebbi: Tsoro bayan sace ɗalibai a Birnin YauriA Jihar Kebbi ta Kudu, musamman Danko Wasagu har yanzu makarantu a rufe suke, tun bayan sace dalibai 96 da aka yi a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri a shekarar 2021.
Iyaye yanzu sun fi son saka yara a makarantun da ke kusa da garuruwa. “Dole ne mu dakatar da su daga makaranta na tsawon wata takwas, ya fi aminci fiye da barin su, su faɗa hannun ‘yan fashi,” in ji Yahaya Abdullahi, wani uban yara uku a kusa da Rijau.
Kabiru Diri, wani manomi a yankin Kanya da ke jihar ya ce, an hana ’ya’yansu da dama shiga makarantunsu.
Ya ci gaba da cewa, “ba da daɗewa aka mayar da wasu daga cikinsu zuwa makarantu a yankunan Mahuta da sauran
Al’ummomi a Masarautar Zuru, har ma wasu iyayen sun kai ’ya’yansu makaranta a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
An rufe makarantu 55 a BenuwaiA Jihar Benuwai makarantu sun rushe a ƙananan hukumomi 11 da suka haɗa da Guma da Logo da Agatu da Kwande da Gwer West. Yawancin ajujuwa yanzu suna karɓar iyalan da suka yi gudun hijira ne.
A Makarantar Firamare ta RCM, Agagbe, yara suna amfani da sararin makarantar ne tare da ’yan gudun hijira, yayin da a Logo LGA, yara suna zaune ba komai, yayin da azuzuwa ke rufe.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Amnesty International ta ce, an lalata ko kuma rufe makarantu 55 a Benuwai a shekarar 2024 kaɗai, tare da kashe a ƙalla mutane 540 cikin wata biyu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, an katse ilmantarwa a yawancin ƙananan hukumomi 23 da ke fama da hare-haren a jihar.
Ƙananan hukumomin da suka fi fama da matsalar sun haɗa da Guma da Logo da Agatu da Kwande da Gwer West da Apa da Gwer East da Ukum da KatsinaAla da Otukpo da kuma Makurɗi, inda akasarin makarantu ko dai an rufe su ko kuma iyalan da suka rasa matsugunansu suka karɓe su.
A Makarantar Firamare ta NKST da ke Anyin a Ƙaramar Hukumar Logo, an dakatar da koyarwa bayan da mazauna ƙauyukan sun mamaye ajujuwa, yayin da a Gwer West da Guma, mafi yawan ƙananan hukumomin ba su da makarantun da suke aiki a yanzu, saboda mazauna yankin sun tsere, wasu ’yan bindiga sun mamaye yankunansu.
Misali, Makarantar Firamare ta RCM da ke Agagbe ta kasance makaranta ɗaya tilo da ta rage a gundumar Mbaakpa ta Gwer West duk da cewa a yanzu tana kokawa wajen aiki tare da ‘yan gudun hijirar da ke mamaye rabin kayan aikinta.
Wata ‘yar shekara tara, mai suna Ukeryima Emmanuella, wadda ta gudu daga ƙauyen
Tse Adekule da ke unguwar Mbachohon tare da iyayenta ta ce: “ya kamata gwamnati ta nemo wurin da ’yan gudun hijira za su zauna, domin makarantarmu tana aiki yadda ya kamata.”
Hakazalika, Orhena Terkuma ɗan shekara 12, wanda ya bar garin Tse Kpar da ke gundumar Sengeɓ ya ce, yana son ci gaba da karatunsa, amma ya kasa, ganin an rufe makarantarsu ta Mbahungwa tsawon lokaci.
Yayin da har yanzu ma’aikatar ilimi ta jihar ba ta ce uffan ba, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar ta ce, tana aiki tare da Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da Tarayyar Turai (EU) da sauran abokan haɗin gwiwa, don nemo mafita mai ɗorewa.
Duk da cewa ba a samu matsala ba, jihar Kwara ta samu tartsatsi a Ƙaramar Hukumar Patigi, inda aka rufe makarantu kamar Makarantar Firamare ta Nyamikpan LGEA bayan hareharen baya-bayan nan. Halartar wasu makarantun da aka sake buɗewa ya ragu. Hakan dai na faruwa ne, duk da cewa gwamnati ba ta sanar da rufe wata makaranta ba.
A garin Matokun da ke Ƙaramar Hukumar Patigi, mazauna yankin sun bayyana yadda iyaye, suka yi gaggawar janye ’ya’yansu daga makarantu sakamakon harin baya-bayan nan. Makarantun da aka koma bayan hutun, an tilasta su rufewa da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Talata, bayan samun bayanai kan sababbin hare-hare.
Yayin da akasarin makarantu a cikin garin a buɗe suke, tsoro da rashin tabbas sun rage fitowar jama’a sosai. A Makarantar Firamare ta Nyamikpan LGEA da ke kan titin Ilorin a cikin garin Patigi, an rufe ƙofofin ne a lokacin da wakilinmu ya ziyarci wajen, inda aka ga yara kaɗan ne suka dawo gida.
Wani malami ya ce, yawan halartar makarantu a yankin ya ragu zuwa kusan kashi 30 cikin 100.
“Makarantar Firamare da ke Matokun ce abin ya fi shafa, inda iyaye suka cire ’ya’yansu suna tsoron barin su, har ma da mu da muke koyarwa.
An harbe ɗaya daga cikin ɗalibaina a lokacin harin, kuma yana kwance a asibiti. Ta yaya za mu je aji da irin wannan fargaba”, in ji wani malami mai suna Matthew Ahmed da ya tattauna da Aminiya.
Wani mazaunin garin da ya bayyana sunansa da Abubakar ya ce, “Yaranmu suna zaune a gida babu abin da suke yi, abin yana da zafi sosai, domin a wannan lokacin ne ya kamata a koyar da su”.
Kwamishinan Ilimi na manyan makarantu na jihar, Lawal Olohungbe ya ce, gwamnati na duba darussan rediyo ga yaran da lamarin ya shafa.
Ya ce, gwamnati ta yi la’akari da koyon ta intanet, amma da sauri ta gane cewa rashin hanyoyin sadarwa a yankunan karkara zai taƙaita tasirinsa.
“Kamar yadda yake da kyau a yi koyarwa ta intanet, yawancin yankunan da ke cikin Kwara ta Arewa da sauran al’ummomin da abin ya shafa, suna da matsalolin sadarwa. Wannan ya kawo mu ga zaɓi na biyu, wanda shi ne azuzuwan rediyo, inda kawai muke ba da sanarwar ba wa yara damar shiga gidan rediyo na wasu sa’o’i. Gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta wannan yanayin, “inji shi.
‘Barazanar talauci da aikata laifuka’Michael Banda na ofishin UNICEF da ke Kano ya jadada mummunar illar rashin tsaro ga ilimi, inda ya yi nuni da hauhawar rashin zuwa makaranta a tsakanin ɗalibai da raguwar amincewar al’umma kan harkar ilimi. Ya ce, rikicin ya sanya yara cikin ruɗani.
“Kowace shekara, rashin makaranta na iya jefa miliyoyin yara cikin wani yanayi na tashin hankali da talauci”, in ji shi.
Aliyu Abdullahi, malamin makaranta ne, inda ya ce matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa na magance matsalar rashin tsaro ba, za a yi watsi da ilimin boko.
“Gaskiyar magana ita ce, yara da matasan da ba su da damar zuwa makaranta, za su bar takwarorinsu da ke zaune a wurare masu aminci, za mu iya gane ɓarnar da aka yi a cikin shekaru ashirin masu zuwa ko kuma nan ba da jimawa,” in ji shi.
Wani masani kan harkokin tsaro, Lamin Ismail Daba ya ce, “yawancin yaran da aka hana su shiga makarantu za su kai ga aikata laifuka, musamman mazan da za su shiga ƙungiyoyin ‘yan fashi da sauran laifuka dabandaban. A ɗaya ɓangaren kuma, ‘yan matan na iya yin karuwanci” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen shawo kan lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga gudun hijira Makaranta makarantu Rashin Tsaro Tsaro da ke Allawa da Makarantar da Makarantar Firamare ta Makarantar Firamare da ke A Makarantar Firamare ta makarantar firamare da da ke Ƙaramar Hukumar da makarantar firamare matsalar rashin tsaro Makarantar Sakandaren makarantar Sakandaren ba sa zuwa makaranta daina zuwa makaranta wani mazaunin garin Wani mazaunin garin a Ƙaramar Hukumar mazauna yankin sun A Ƙaramar Hukumar Makarantun da aka an rufe makarantu An rufe makarantu makarantun da aka makarantun da ke yan gudun hijira da abin ya shafa zuwa makaranta a da suka haɗa da yi gudun hijira wasu makarantun a makarantun da Hukumar Kula da firamare da ke Primary da ke da makarantun aka mayar da da makarantu sun haɗa da ya nuna cewa makarantu da makarantu a makarantu A Gwamnati da ta Gwamnati kamar yadda yan bindiga gwamnati da a makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara
Aƙalla jami’an tsaro takwas, ciki har da ɗan sanda guda ɗaya da masu tsaron al’umma bakwai, sun rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da aka kai musu a hanyar Gusau–Funtua da ke Jihar Zamfara a ranar Alhamis.
Lamarin ya faru ne a lokacin da gamayyar jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da ’yan sanda da mambobin rundunar tsaro ta jihar Zamfara ke amsa kiran gaggawa daga kauyen Tungawa da ke ƙaramar hukumar Tsafe.
An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a Bauchi Majalisar Dattawa ta amince da Amupitan Shugaban INEC“Maganar da nake yanzu haka, an kwashe gawarwakin jami’an da suka mutu zuwa Gusau domin jana’iza,” in ji wani shaida da aka bayyana sunansa da Tsafe.
Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe, Hon. Garba Fanchan, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Ya bayyana harin a matsayin “mugunta da rashin imani,” yana mai tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar matakan gaggawa don dakile matsalar tsaro da ke ƙaruwa a yankin.
Gwamnan jihar, Dauda Lawal, shi ma ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan mamatan.
A cikin wata sanarwa ranar Alhamis, gwamnan ya jajanta wa hukumomin tsaro tare da addu’ar Allah ya gafarta wa jami’an da suka rasa rayukansu.
“Waɗannan jaruman sun mutu ne a yayin da suke bakin aiki don kare al’ummarmu. Allah ya gafarta musu, ya sa sun huta,” in ji Gwamna Lawal.
Hanyar Gusau–Funtua na ƙara zama wurin da ake yawan kai hare-hare, inda rahotanni ke nuna cewa kusan kowace rana ’yan bindiga na kai farmaki ga matafiya a hanyar.
Hukumomi sun sha alwashin ƙara daukar matakai domin dawo da zaman lafiya a hanyar da kuma tabbatar da lafiyar matafiya.