Gaza Ta Bukaci A Binciki Isra’ila Kan Sace Sassan Jiki A Gawarwakin Falasdinawa
Published: 18th, October 2025 GMT
Hukumomi a Gaza sun zargi sojojin Isra’ila da satar sassan jikin gawarwakin Falasdinawa tare da kira a binciki wannan “mummunan laifi.”
Darektan ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza Ismail Thawabta, ya fada a ranar Jumma’a cewa sojojin “mamaya na Isra’ila sun mika musu gawarwaki 120 ta hannun kungiyar agaji ta Red Cross a cikin kwanaki ukun da suka gabata, amma mafi yawan sun zo cikin mummunan yanayi, suna nuna alamun kisa da kuma azabtarwa.
Thawabta ya ce akwai alamun shakewa da alamar igiya a wuyansu, lamarin da ke nuni da kisa da gangan.”
“Sassan gawarwakin mutane da yawa sun bace, ciki har da idanu, da sauran gabobin,” in ji Thawabta, wanda ya ce ya tabbatar da cewa sojojin Isra’ila “sun sace sassan jikin mutane yayin da suke rike da gawarwakin,” yana mai cewa hakan “laifi ne.”
Jami’in na Falasdinawa ya bukaci kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su gaggauta kafa wani kwamitin bincike na kasa da kasa don binciken lamarin.
A halin yanzu dai Isra’ila na rike da gawarwakin fursunonin Falasdinawa 735, ciki har da yara 67, in ji kungiyar fafutikar kwato gawarwakin Shahidan Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Bukaci A Kafa Kotun Kasa Da Kasa Kan Gawarwarkin Da Isra’ila Ta Dawo Mata Da Su. October 18, 2025 Madagascar : An rantsar Da Michael Randrianirina A Matsayin Shugaban Kasar October 18, 2025 Iran Ta yi Tir Da Harin da Isra’ila Ta kai Kudancin Kasar labanon. October 18, 2025 Majalisar Dattawa Za Ta Gana Da Ministan Ilimi Kan Batun Yajin Aikin Asuu. October 18, 2025 Gaza ta bukaci a binciki Isra’ila kan sace sassan jiki a gawarwakin falasdinawa October 18, 2025 Madagaska : An rantsar da Kanar Randrianirina a matsayin shugaban kasa October 18, 2025 Al-Houthi: Matsin lamba bai hana Iran ci gaba da goyon bayan Falasdinu ba October 18, 2025 Marzieh Jafari Ta Dauki Lambar Yabo Ta Horar Da Mata Wasan Kwallon Kafa Ta Nahiyar Asia October 18, 2025 Iran: Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Yarjeniyar JCPOA Ya Kawo Karshe A Yau October 18, 2025 Iran: Kauyuka 3 Sun Shiga Cikin Wuraren Bude Ido Na Duniya October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Washington Post: Shirin Trump Na Kai Sojojin Gaza Yana Fuskantar Matsala
Jaridar Washington Post ta buga rahoto akan Shirin Donald Trump na aikewa da sojoji zuwa Gaza, tare da cewa tana fuskantar matsala, domin har yanzu ana Magana akan yadda za a raba ‘yan gwgawarmaya da makamansu.
Jaridar ta ci gaba da cewa; Da akwai damuwa a cikin manyan biranen kasashen duniya danagne da yiyuwar a bukaci sojojin da za a aika su yi amfani da karfi akan Falasdinawa.
A ranar 17 ga watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDD ya fitar da kuduri na amincewa da Shirin da Trump yake da shi akan abinda ya kira zaman lafiya a Gaza.
Kasar Indonesia ta yi alkawalin aikewa da sojojin da za su kai 20,000 domin aikin tabbatar da zaman lafiya. Sai dai kuma kasar tana bukatar ganin an rage yawan aikin da sojojin za su yi.
Ita ma kasar Azerbaijan wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza, tana yin bitar abinda ya kamata su yi.
Sai dai har yanzu babu wata kasar larabawa wacce ta yi alkawalin aikewa da sojoji zuwa Gaza a karkashin Shirin an Trump.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MDD: Kasar Somaliya Tana Fuskantar Mawuyacin Yanayi Saboda Fari November 30, 2025 An Yi Ganawa A Tsakanin Ministocin Harkokin Wajen Turkiya November 30, 2025 Iran ta bayyana halin da Falasdinawa ke ciki da rauni mufi da aka wa dan adam a doron kasa November 30, 2025 An yi gangami a fadin duniya a zagayowar ranar Falasdinu November 30, 2025 Cinikin Kasashen Waje na Iran Ya Zarce Dala Biliyan 76.5 November 30, 2025 Najeriya : Sojoji sun kubutar da yan mata 12 da mayakan ISWAP November 30, 2025 An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru November 30, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mika Sunaye Sabbin Jakadun Kasar su 32 Ga Majalisa Domin Tantancewa November 30, 2025 Hizbullah Ta Bukaci Shugaban Cocin Katolika Na Duniya Yayi Tir Da Hare-haren Isra’ila November 30, 2025 Iran: Kalaman Da Trump Yayi Na Rufe Sararin Samaniyar Kasar Venuzuwela Ya Sabama Doka. November 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci