Sarkin Zuru ya rasu yana da shekara 81
Published: 17th, August 2025 GMT
Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya.
Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne a daren Asabar a wani asibiti da ke birnin London bayan fama da jinya.
Marigayin ya bar mata hudu da ‘ya’ya bakwai.
A cikin sakon ta’aziyya, Gwamnatin Jihar Kebbi ta bayyana alhinin ta kan rasuwar Sarkin, tare da mika ta’aziyya ga iyalansa, Majalisar Masarautar Zuru, al’ummar Zuru da daukacin Jihar Kebbi.
“Gwamnati na roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi mafaka a Aljannatul Firdaus,” in ji sanarwar.
Za a sanar da cikakken tsarin jana’izarsa daga baya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kebbi
এছাড়াও পড়ুন:
Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda
Babban Sufeton ’Yan Sanda na Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce galibin jama’a ba sa yaba wa kokarin jami’ansu na hana aikata laifi a cikin al’umma, duk da yana daya daga cikin manyan ayyukansu.
Kayode, wanda Mataimakin Babban Sufeto mai kula da sashen sayo kayayyaki na rundunar, A.A. Hamza ya wakilta, ya fadi hakan ne a Abuja ranar Alhamis, yayin taron kaddamar da wani littafi mai suna “Fraud unmasked”, wanda Dr Preal Ogbulu ya wallafa.
Kotun kasar Kanada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci NAJERIYA A YAU: Halin ƙuncin da ’yan fansho ke ciki a NajeriyaA cewarsa, “Duk laifin da aka dakile aikatawa, dole akwai namijin kokarin da aka yi a kan hakan. Kundin tsarin mulki da kuma dokokin’yan sanda ya ba rundunarmu aikin ganowa da kuma hana aikata laifi. Abu mafi muhimmanci ma shi ne hana aikata laifin tun kafin a yi shi, saboda ya fi sauki, ya fi sauri sannan yana rage cutar da mara karfi,”
Ya kuma lura cewa galibi jama’a kan auna nasarorin ayyukan ’yan sanda ne a kan laifukan da suka faru, ba tare da kallon wadanda suka dakile faruwarsu ba.
Babban Sufeton ya ce, “Duk lokacin da muka hana aikata wani laifi, ba a ganin mun yi kokari. Lokacin da kawai ake ganin kokarinmu shi ne bayan aikata laifi, kodayake aikinmu ya wuce iya nan”.
Daga nan sai Kayode ya yaba wa mawallafin littafin kan yadda ya tabo batutuwan binciken kwakwaf da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen hana aikata laifi da kuma hukunta masu aikata shi.
Babban Sufeton ya kuma ce littafin ya yi daidai da kudurorin rundunarsu sannan ya fito da muhimmancin hadin gwiwa wajen dakile aikata laifuka.