HausaTv:
2025-10-19@10:48:01 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154

Published: 19th, October 2025 GMT

154-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar Khudubar Imam Hassan Al-mujtaba (a) ya gabatar da khudubarsa ta farko bayan shahadar mahaifinsa Amirulmuminina (a) a masallacinsa da ke Kufa. Mun ji cewa a bangaren khudubarsa ta farko yayi magana kan darajar mahaifinsa Imam Ali (a) da sabikan a cikin addinin musulunci, wadanda suka hada da saida ransa don kare ran manzon All..(s) da kuma jihadi a kan tafarkin All..kuma tare da manzon All..(s). Jibirilu da Mika’ilu suna dama da hagunsa. Sannan ya yi maganar cewa mahaifinsa ya yi shahada a cikin dare mai daraja, daren da Allah ta’ala ya dauke annabi Isa dan Maryamu daga doron kasa zuwa sama, sannan darenda wasiyin annabi Musa (a) Yusha’u dan Nun ya yi wafta shi ma. Sannan mun bayyana cewa wasu malaman shi’a suna ganin daren 21 na watan Ramadan ita ce daren lailatul kadiri, wanda Allah yayi maganarsa a cikin Al-kur’ani mai girma.

Sannan yayi kuka ya zubar da hawayensa, haka ma wadanda suke cikin masallaci suka yi koka da kukansa.

Sannan bayan an yi shiru na wani lokaci sai ya fara bangare na biyu na khudubarsa, inda ya bayyana masu matsayinsa da nasabinsa da daukakar da All..yayi masa, saboda su san cewa ya cancanci khalifancin manzon All..(s) kamar yadda mahaifinsa da kaninsa suka cancanta.

Ya ce ga wadanda basu sanci ba, to shi ne Al-Hassan dan Aliyu, shi ne dannabin wannan al-ummar, inda muka bayyana cewa manzon All..(s) yana kiransa da kaninsa Hussain (a) yayansa, ya ce shi ne fitila mai haskakawa, dan wanda yake kira zuwa ga All.. da izininsa. Y ace yana daga cikin wadanda mala’ika jibirilu yake sauka ya tashi a gidansu, yana daga cikin wadanda All..ya tsarkaka daga daudar zunubi tsarkakawa, yana daga cikin wadanda Allah Ta’ala ya wajabta sonsu ga musulmi.

Bai haka sai aka fara yi masa bai’a. Ubaidullahi dan Abbas ya tashi daga cikin mutane bayan khudubar Imam (a) yana cewa : Ya ku mutane ! Wannan shi ne dan Annabinku kuma wasiyyin limaminku ku tashi ku yi masa bai’a.

Daga nan sai mutane suka daga murya a cikin masallaci suna bayyana biyayyarsu a gare shi, suka kuma bayyana yardarsu da shugabancinsa. Da kuma cancantarsa da khalifanci. Daga nan suka yo kan Imam suna son yi masa bai’a.

Wanda ya fara yi masa bai’a shi ne shugaba kuma gwarzo Qais dan Sa’ad al-ansari, kafin yayi bai’ar sai yana bayyana shirinsa na hamasar yaki, sai ya cewa Imam(a) shimfida hannunka in yi maka mubaya’a kan littafin Allah da sunnar annabinsa da kuma yakar wadanda suka saba maka, sai kafin ya bashi hannu, ya ce masa

{Kan littafin Allah da sunnar Annabinsa, don sun zo da duk wani sharadi} saboda yakar makiyansa yana hannun Imam ne, kuma bisa littafin Allah da sunnan manzon Allah (s) suke yaki ko sulhu, kuma Imam ne yake da zabin daya daga cikinsu. Idan wani yana son ya bayyana masa a ina ya dauko shi a littafin All..ko sunnar manzon All..(s). sannan ya bashi hannunsa ya yi musafaha da shi.

Daga nan duk jama’ar da ta zo zata yi masa bai’a sai ya fada masu cewa

{Zaku yi mani bai’a ne bisa ji da bi, kuma zaku yiki wanda nay aka, zaku zauna lafiya da wanda na zauna da shi lafiya}, a lokacinda suka ji wannan sharadin sai suka dakatar da bai’ar, sai Imam kuma ya dauke hannunsa daga garesu. Sai suka yi tururuwa zuwa ga kaninsa Imam Hussain(a), suna cewa ka shimfida hannunka mu yi maka mubaya’a irin wanda muka yiwa babanka da kuma yaki da wadanda suka saba maka batattu mutanen sham. Wasu malaman tarihi daga ciki harda Ibnu Kutaiba a cikin littafinsa Al-Imama wassiyasa, suna cewa, sai Imam Hussain(a) ya maidasu, yana cewa

{Allah ya tsareni in karbi bai’arku matukar Al-Hassan yana nan da ransa}. Bayanda Imam Hussain (a) ya maida su, sai suka koma suka yiwa Imam Al-Hassan mubaya’a basa so.

Wannan ba gaskiya bane, saboda yana nufin Imam Hassan (a)  tun farko yana nufin sulhu da mutanen sham, amma abinda zai zo nan gaba zai tabbatar mana da cewa, ba haka bane. Imam yana da nufin yakar mu’awiya dan Abusufyan har sai ya mika kai.

Kuma ko da hakan gaskiya ne, to sai dai da khawarijawa, wadanda suke neman tada hankali,  da samarda damuwa a cikin musulmi. Don su sun jirkirta bai’arsu zuwa wani lokaci. Wannan ya nuna shakkun da khawarijawa suke da a cikin lamarin sabon limaminsu.

Sai kuma shi’ar Iyalan gidan manzon All..(s) suna kan bakarku na biyayya ga wasiyyan manzon All..(s) kuma basa wani taraddu kan cewa su suka fi cancanta da jagoranci da kuma khalifanci kamar yadda All..ya zabesu da shi.

Don haka dangan da wannan Imam (a) yana kan bakansa na cewa abinda ake bukata shi biyayya da da’a gareshi, amma yakar wadanda suka yi masa tawaye, khawarijawa ne ko mutanen sham zabi na hannunsa.

Har’ila yau wasu malaman tarihi suna ganin ai bai kamata Imam Al-Hassan (a) ya karshi khalifanci bayan shahadar babansa ba, saboda daular musulunci a  lokacin tana cikin tashe-tashen hankula wadanda Mu’awiya da Abusfyan ya tayar da kuma Khawarijawa. A ganin bai kamata ya karbi khalifancin ba. Dan amsa wannan tambayar Alhujjatu Ali-yasin ya ce.

01-Idan har ya zama wajibi ne mutane a cikin addini su yi bai’a ga limami wanda aka nada shi, to kuwa ba zai yu ga limamin da aka nadar ya ki karban bai’arsu ba. Don idan akwai mataimaka, ya zama waji ga liman ya karbi jagorancin wadanda Allah ya dora masa shugabancinsu. Don haka a yayinda akwai magoya baya a ciki da wajen kufa, ba zai halatta ga Imam(a) ya ki karban bai’arsu ba.

02-Kada mu takaita kallommu zuwa ga rayuwar duniya kasai, shugabancin iyalan gidan manzon Allah (s) a addinin musulunci Allah da manzonsa (a) sun rika ya kammala shi tun manzon Allah (s) yana da ransa.

Ko tare da bai’a ko babu bai’a a wajen Allah Imam Al-Hassan (a) shi ne shugaba bayan mahaifinsa, mutane sun bi shi ko sun ki binsa. Sannan mutane ne suke bukatarsa don ya kasance shugabansu, ba shi yake bukatarsu ba, amma idan sharuddan jagorancin sun cika a nan bai da zabi na jinkiri ko da na wani lokaci ne.

03-Sannan da ya jinkita kamar yadda masu sukansa(s) suke so, ya jira sai mu’awiya dan Abu sufyan ya zo ya rufesu da yaki a Kufa basu da shugaba? Ko kuma sai wasu musibun sun kara bayyana? Da haka ya faru da sai al-ummar musulmi ta fada cikin wasu Karin matsaloli wadanda ba za’a taba warwaresu ba.

Daga nan sai sauran garuruwa da suke karkashin ikon Amirul muminina (a) kafin shahadarsa suka fara aiko masa bai’ar mutanensu. Kasar Iraki ga daya da sauran wurare duk sun aiko masa da bai’arsu.

A Basra, Imam Hassan(a) ya tabbatar da Zayar dan Abihi a kan walin Basra da wasu yankuna a kasar Farisa.

A kufa kadai mutane dubu 42 sun masa bai’a , kan ji da biyayya, haka ma a Mada’in da dukkan mutanen Iraki sun masa bai’a. Mutanen Hijaz da Yemen sun masa bai’a . ba wadanda basu yi masa bai’a ba sai mu’awiya a sham da kuma masar Inda Amru dan Asi yake wali daga wajen Mu’awiya.

A lokacin da Al-amura suka tabbata a gareshi, ya nannada mukamai daban daban, ya karawa mayakansa dirhami dari dari a al-bashinsu, kamar yadda babansa yayi a yakin Jamal. Da haka kuma ya mallaki zukatansu da kuma takubbansu.

Ibnu Kathir yace: ya yayi haka sai suka so shi fiye da mahaifinsa.  Ya yi khudaba a cikinsu ya kara jaddada masu kan cewa shugabancinsa shi ne shirin Allah na shugabancin al-ummar musulmi, saboda All..ya takaita shugabanci a cikin iyalan gidan manzon All..(s).

Ya gargadesu dangane da sauraron farfagandar mu’awiya dan Abusufyan, ya kuma kira su zuwa nuna turjiya kan fasadin da banu umayya karkashin jagorancin Mu’awiya a cikin al-ummar musulmi.

Sannan akwai kura-kurai wadanda malaman tarihi suka yi saboda rashin zurfafawa cikin biske da gano gaskiyan abinda ya faru dangane da bai’ar Imam Al-Hassan (a).

Daga cikin Mas’udi yana cewa ‘ an yi wa Imam Hassan (a) bai’a ne bayan wafatin mahaifisa da kwanaki  biyu}. Wannan ba haka bane, musamman idan mun dubi mafi yawan littafan tarihi, wadanda suka tabbatar da cewa an masa bai’a , wayewar garin da ya yiwa babansa jana’iza.

Sannan Faridul Wajdi ya ce, an yiwa Imam Al-Hassan (a) bai’a kafin wafatin mahaifinsa, bayan bai’ar ne ya yi wafati. Wannan shi ma ba hakabane, saboda mafi yawan malaman tarihin sun bayyan cewa hakan ya kasance ne bayan wafati da kuma jana’izarsa(S).

Sai kuma Khuduri, wanda ya ce shi’ar Ali(a) a Irakine kawai suka yi masa bai’a a Iraki da gewayensa. Wannan ma ba gaskiya bane saboda dukkan kasashen da suke karshen ikon mahaifinsa sun masa bai’a sai wadanda suke karkashin ikon Mu’awiya.

Sai taha Hussain, wanda  ce Imam Al-Hassan (a) bai gabatar da kansa don bukatar a yi masa bai’a ba. Sai ya yi jawabi ne, mutane suka yi kuka, sannan Abaidullah dan Abbas ya kira mutane su yi masa bai’a. Wannan ma ba haka yake ba, musamman idan mun dubi bangare na biyu na khudubarsa, inda yake bayyana nasabarsa, da tsarkin gidansu, da kuma wajabta sunsu ga dukkan musulmi.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: ar Imam Al Hassan malaman tarihi wadanda suka kamar yadda Mu awiya da

এছাড়াও পড়ুন:

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153

153-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littana wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa, na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-Mujtaba(a) dan Fatimah diyar manzon All..(s) da muke kawo muku. Mun yi maganar yadda, addinin musulunci ya himmatu da shugabanci, saboda haka ne ya ciki addini da shi kamar yadda ya zo a cikin aya da 3 na suratul Ma’ida.

Sannan mun ji yadda Amirulmumina (a) yayi wasiyya ga dansa Imam Hassan (a) da kuma kaninsa Imam Alhussain (a) a bayansa. Mun bayyana cewa manzon All..(s) tare da umurnin All..ya bayyana cewa khalifofi a bayansa 12 har duniya ta nade na farkonsu Ali(a) sannan yayansa Alhassan da Alhussain daga nan sai yayan Alhussain 9.

Amirul muminina (a) ya yi ishara kan wannan batun a cikin khudubobinsa da dama, inda yake ishara da wadan nan limamai daga iyalan gidan manzon All..(s).

Kamar inda yake cewa {Su ne rayuwar ilmi, da mutuwar jahilci, hakurunsu ne zai sanar da ku ilminsu, da kuma zahirinsu daga badini, yin shirinsu kuma daga hikimar maganasu, basa sabawa gaskiya kuma basa sabani a cikinta, kuma sune ginshakan musulunci, kuma sune mafaka da kuma kariya ga musulmi.

Da su ne gaskiya yake koma inda ya dace da shi, sannan bata yake kaucewa daga inda yake, harshen karye yake yankewa daga tushensa, sun rike addini rikon kareshi da kuma aikata shi, bar ikon ji da sani da kuma fada kawai ba, lalle masu fadar ilmi suna da yawa, amma masu kiyaye ilmin a aikace kadan ne}

Har’ila yau dangane da su manzon All..(s) yana cewa {Wannan addinin ba zai gushe a tsaye kamar yadda yake ba har zuwa ranar kiyama, idan har shuwagabannin 12 ne zasu zama khalifofib, dukkaninsu kuraishawa ne}. A wani hadisi yana ce {Al-Hassan da Alhusain limamai ne sun tashi ko sun zauna}, ma’a sun tashe sun yi yaki ko sun yi sulhu.

Da wasu hadisai da dama dangane da su. Don haka bayan kammala jana’izar Mahaifinsa, da zartar da hukuncin kisasi kan ibnu Muljam, Imam Hassan (a) a ranar 21 ga watan Ramadan ya je masallacin mahaifinsa A kufa, ya hau kann mimbari, sannan sahabban mahaifinsa da wasu sahabban manzon All..(s) da sauran mutanen kufa suka cika masallacin, sannan ya fara khudubarsa ta farko inda yake cewa {Hakika an dauki ran mutum a cikin wannan daren, wanda magaba basu kama kafarsa a ayyuka ba, kuma na baya ba zasu kama kafarsa ba a ayyukan alkhairi, hakika ya kasance yana jihadi tare da manzon All..(S) inda yake kareshi da ransa, manzon All..(s) ya kasance yana aika shi tare da tutarsa, sai mala’ika jibrilu yana kare shi daga damarsa sannan mika’ilu yana kare shi daga hagunsa, ba zai dawo ba sai All…ya yi bashi nasara ta hannunsa.

Hakika yayi wafati a cikin daren da aka dauke Isa dan Maryam(s) (a) daga doron kasa zuwa sama, yayi wafati a daren da Yushau dan nun wasiyin anna musa(a) yayu wafati, bai bar kudade ba sai dirhami 700 wanda ya rage daga cikin albashinsa, yana son ya sayawa iyalansa khidimi da su, ya umurceni da in maida su cikin baitul mali} daga nan ya tuna da mahaifinsa, sai yayi kuka hawaye suka zuba daga idanunsa}.

Daga nan sai dukkan wadanda suke cikin masallacin suka yi kuka da kukansa(a), daga baya sai an yi shi a cikin masallacin, saboda bakin ciki da Rashin Amirul muminina (a), daga nan sai Imam Al-Hassan (a) ya sake tada maganarsa, inda yake cewa

{Ya ku mutane! Wanda ya sanni ya sanni, wanda kuma bai sanni ba, to nine Al-Hassan dan Aliyin, nine dan Annabi (s), nine dan wasiyi, nina dan mai bada Bushara mai gargadi, nine dan mai kira zuwa ga All..da izininsa, nine dan fitila mai haske, ina daga cikin iyalan gida wadanda mala’ika Jibrilu yake sauka yay a tashi daga wajemmu, kuma ina daga cikin Ahlulbaiti wadanda All..ya tafiyar da dauka daga garesu ya tsarkakesu tsarkakewa, kuma ina daga cikin iyalan gidanda All….ya wajabta sonsu a kan duk musulmi, All..mai girma da daukaka ya fadawa annabinsa(s) {Ka ce, Ban tamyeku wata lada a kansa ka, sai so ga dangina na kusa, kuma ga wanda ya aikata mai kyau} kuma aikata mai kyau shi ne sommu Ahlul baiti}

Wannan shi shi khudubar Imam Al-Hassan dan Ali (a) na farko bayan shahadar mahaifinsa Aliyu dan Abitalib (a) kuma ga bayanin wasu daga cikin abubuwan da ya kawo a cikin khudubarsa (s).

Da farko ya bayyanawa mutane matsayin mahaifinsa Imam Ali (a) a musulunci, musamman jihadinsa tare da manzon All..(s), a lokacinda manzon All..(s) yake bashi tuta ya je yaki, ta manya-manyan mala’ikun All..suna tare da shi, kuma sune Jibiru da Mika’il, wannan shi sirrin nasarar da Aliyu dan abitalib ya samu a kan mushirikai a yake yaken da manzon All..(s) yayi a duk tsawon rayuwarsa. Don babu wani yaki wanda manzon All..(s) yayi a rayuwarsa face Aliyu na tare da shi kuma shi ne mai rike da tutar yakin, sai yakin tabuka, wanda ba’a ma yi shi ba.

A manya-manyan yake-yaken wadanda manzon All..(s) ya yi da mushrikai, Aliyu dan Abitalib shi ne kwarzon yakin. A badar shi ya kashe fiye da rabin mushrikan da aka kashe, a uhud bai gudu ba kamar yadda da dama suka gudu, saboda haka ne aka ji masa Rauni kimanik 8 a jikinsa, manzon All..(s) ma an ji masa rauni a wannan yaki. Aliyu shi ne gwarzon yakin Ahzab inda ya kashe amru dan Abduwud, shi ne gwazon Khaibara, inda ya kashe Marhab ya sami nasara a kan yahudawan khaibara. She ne gwarzon Hunain, bai gudu ba, kamar yadda wasu suka gudu, sannan shi yay a kare manzon All..(s) daga mayakan Hunain, ya kuma sami nasara a kansu.

Aliyu(a) ya sami nasarori a dukkan inda manzon All..(s) ya tura shi yaki, yakin zatussalasil, yake yake da dama a Yemen da sauransu.

Sanna a yakin tabuka bai fita da shi ba saboda, akwai makircin da ake son a yiwa addinin musulunci, wanda ya kadai zai iya magance shi.

Har’ila yau ya bayyana yadda mahaifinsa Amirulmuminin (a) yake kare banzan All..da ransa, kama daga daren hijira, inda ya seda ransa ya kwanta a shimfidan manzon All..(s) bayan ya san mushrikan Makka sun yanke shawarar kashe a wannan daren. Sanna a yakin Uhudu, shi da wasu  mutane kadan ne suka kare manzon All..daga mushrikai.

Sannan Imam Al-Hassan (a) ya ca na farko da na karshe basu kama kafarsa a aikin alkhairi ba, don haka wanda ya kasance haka to kuwa shi ne mafi girma da daukaka. Idan ana maganar masu matsayi irinsa a cikin wasiyan annabawa da bayin All..da aka yi ko za’a yisu nan gaba, ba wanda zai kama kafarsa. A hadisi manzon All..(s) yana cewa Aliyu (a) shi ne siddiki mafi girma.

02-Imam ya bayyana darajan daren da mahaifinsa ya koma ga mahalicinsa, wato shi ne daren da aka yi mirazi da Isa dan Maryam (a), har ila yau shi ne darenda wasiyyin annan Musa (a) Yusha’u dan Nun ya bar duniya shi ma. Wasu malaman shi’a suna daukar daren 21 ga watan Ramadan shi ne daren lailatul Kadiri wanda Alkur’ani mai girma yayi maganarsa. Kuma wasu hadisan manzon All..(s) suka suka bayyana cewa daren yana cikin darare 10 na karshen watan.

Don haka a wannan daren mai albarka ne wasiyyin manzon All..(s) ya koma ga Ubangijinsa mai girma da daukaka.

03-ya bayyana zuhudun mahaifinsa Imam Ali (a), gudun duniya ta sa shi ya kaurace mata, don haka bai bai kome da duniya ba, sai dirhami 700 wadanda suka rage daga cikin albashinsa, wadanda kuma da yar ayu zai sayawa iyalansa kuyanga ko bawa wanda zai taimaka masu a ayyukansu na yau da kullum.

Dukiyar al-umma masu yawa suna shiga hannunsa, amma baya karkata zuwa wannan duniyar kamar yadda wasu shuwagabannin a zamaninsa suka karkata zuwa gareta. Yayi haka don yarda da amincewar abinda All..ya yi masa alkawari a lahira. Sannan a lokacinda ya ga zai bar duniya ya umuce shi, wato Al-Hassan (a) ya maidasu cikin kudaden jama’a, wato Baitul Mali.

04-daga karshe Imam Al-Hassan a cikin khudubarsa ta farko bayana shahadar mahaifinsa, ya fadawa mutane, waye shi. Menen matsayinsi a cikin wannan al-umma da musulmi, inda ya bayyana cewa, shi Alhassan dan Ali, dan kuma annabin wannan al-ummar, tunda mahaifiyarsa diyar manzon All…(s), a nan hadisai da dama sun zo daga manzon All..(s) yana cewa Alhassan da Alhusain yayansa ne.

Kuma inda yake cewa All..ya Sanya zurriyar ko wani annabi daga tsutsunsa, amma ya Sanya zurriyyarsa a tsotson Ali(s). Imam Ali (a) kansa, yakan fadi cewa, Alhassan da Alhusain yayan manzon All..ne, sannan sauran yayansa kuma, yayansa ne. Sannan ya bayyana cewa yana daga cikin wadanda mala’ika jibrilu yake sauka ya tashi a gidansu, yana daga cikin wadanda All..ya tsarkakesu daga sabo, kamar yadda ya zo a cikin alkur’ani, kuma yana daga cikin wadanda All..ya wajabta sonsu a cikin alkur’ani mai girma.

Don haka duk wanda ya ji wannan, shi akwai wanda ya shi Daraja da daukaka da cancantar zama shugaba irinsa?. Don haka Imam Alhassan (a) ne yafi cancanta da kuma dacewa da shugabancin Al-ummar kasansa tunda ba wani dan annabi ko jikan annabi da yak e dan doron kasa a lokacin sai shi da kaninsa Al-hussain (a).

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150 October 19, 2025 Wata Kotun A Murka Ta Haramtawa HKI Kafa Na’urorin Leken Asiri A Wayoyi Masu WattsApp October 19, 2025 Sojojin Najeriya: Rahotanni Dangane Da Juyin Mulki Wa Shugaba Tinubu Ba Gaskiya Bane October 19, 2025 Hamas Ta Gabatar Da Sunayen Kwararrun Da Zasu Gudanar Da Harkokin Gaza October 19, 2025 Doha: Pakistan da Afghanistan sun amince da tsagaita bude wuta a tsakaninsu October 19, 2025 Isra’ila ta ce mashigar Rafah za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai abin da hali ya yi October 19, 2025 Araqchi: Kuduri Mai Lamba 2231 Ya Zo Karshe October 18, 2025 Kasashen Iran, Rasha, Da China Sun Jaddada Rashin Halaccin Dawo Da Tsohon Takunkumi Kan Iran October 18, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157
  • KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 150