MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza
Published: 19th, October 2025 GMT
Hukumar samar da abinci ta MDD ta bukaci a bude duk wasu hanyoyi domin shigar da abinci a Zirin Gaza, saboda yadda magance matsalar yunwa a Zirin zai dauki lokaci.
Kakakin WFP Abeer Etefa ta shaidawa manema labarai a Geneva cewa, za a dauki lokaci kafin a rage yunwa.
“Yanayi a Gaza yana da matukar wahala kuma har yanzu muna da nisa daga cimma wannan burin,” in ji ta.
A cewar WFP, bukatar gaggawa ta ta’allaka ne ga “bude mashigar kan iyaka guda biyar” zuwa cikin yankin “domin a wadata Gaza da abinci da kuma samar da wuraren rarrabawa cikin gaggawa,”.
Shirin WFP, “shi ne kara yawan taimakon da za a kai ga mutane miliyan 1.6 a cikin Gaza cikin watanni uku masu zuwa,” in ji Madam Etefa
A ranar Alhamis din da ta gabata ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Sa’ar ya sanar da cewa wata kila a bude mashigar Rafah tsakanin zirin Gaza da Masar ranar Lahadi.
Majalisar Dinkin Duniya da manyan kungiyoyi masu zaman kansu na yin kira da a bude wannan mashigar, yayin da zirin Gaza ke fuskantar mummunar matsalar jin kai sama da shekaru biyu na yakin da aka fara a watan Oktoban shekarar 2023.
A cikin watan Agusta, kwararrun abokan hulda na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar a hukumance cewa ana fama da yunwa a zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan(a) 158 October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Al-Hassan (a) 157 October 19, 2025 KissoshinRayuwa : Sirar Imam Al-Hassan(a) 156 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 155 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 154 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 153 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 152 October 19, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 151 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.
Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, musamman hare-haren ’yan bindiga, da ‘yan ta’adda, da masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci a yankuna daban-daban.
Ko wadanne irin kalubale ne ke gaban sabon ministan tsaron yayin da yake shirin kama aiki a ma’aikatar tsaro bayan majalisa ta tabbatar da shi?
NAJERIYA A YAU: Matsalar Kansar Mama Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan