Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-10-16@09:47:36 GMT

Ana Aikin Tsaftace Unguwar Kwankwasiyya Mataki Na biyu

Published: 16th, October 2025 GMT

Ana Aikin Tsaftace Unguwar Kwankwasiyya Mataki Na biyu

Hukumar kula da gidaje ta jihar Kano ta fara wani gagarumin aikin tsaftar muhalli kashi na biyu a birnin Kwankwasiyya, inda ta kara azama wajen gina tsaftataccen muhalli, lafiya da kuma dorewar muhalli a birane.

 

Da yake jawabi yayin aikin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Engr. Isyaku Umar Kwa, ya bayyana cewa kashi na biyu ya mayar da hankali ne kan inganta harkar sharar gida, da inganta tsarin tattara shara, da kuma kawata wuraren jama’a a fadin birnin na Kwankwasiyya.

 

A cewarsa, aikin na da nufin tabbatar da tsaftar tituna, wuraren shakatawa, da wuraren jama’a tare da inganta alkinta muhalli.

 

Engr. Kwa ya bayyana cewa an tsara wannan shiri ne domin karfafawa mazauna garuruwan Kwankwasiyya da Bandirawo da Amana kwarin guiwa da su taka rawar gani wajen kiyaye tsafta a tsakanin al’ummarsu.

 

Ya kuma kara jaddada cewa shirin zai taimaka wajen rage cututtuka masu alaka da tsaftar muhalli ta hanyar sarrafa sharar gida da inganta ayyukan tsafta.

 

Mukaddashin Manajan Daraktan ya kuma bayyana cewa, aikin tsaftar muhalli ya yi daidai da tsarin sabunta biranen gwamnatin jihar, wanda ya ba da fifiko ga ci gaba da farfado da manyan biranen uku na Kwankwasiyya da Bandirawo da kuma Amana.

 

Ya tuna cewa Birnin Kwankwasiyya, wani bangare ne na aikin raya birane da aka fara a zamanin gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, an tsara shi ne domin magance matsalolin da suka hada da karancin gidaje, da rage cinkoson birane da dorewar muhalli.

 

A karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, an sake yin kokarin farfado da wadannan garuruwa, da warware batutuwan da suka hada da biyan kudaden fansho, da tabbatar da gudanar da ingantaccen albarkatun kasa.

 

Engr. Kwa ya kara da cewa ayyukan tsaftar muhallin da ake ci gaba da yi sune muhimman matakai na cimma wadannan manufofin raya birane da inganta rayuwa da tabbatar da dorewar muhalli a fadin sabbin biranen Kano.

 

Rel/Khadijah Aliyu

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwankwasiyya tsaftar muhalli

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin  Gargadi A Kasa Baki Daya .

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ASUU ta ƙasa da ke Jami’ar Abuja, inda ya zargi gwamnatin tarayya da rashin gaskiya wajen tattaunawa kan buƙatun ƙungiyar. Don haka sun fara yajin aiki daga yau na gargadi na tsawon mako biyu.

Ana ta bangaren Gwamnatin tarayya ta gargadi ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) da ta guji shiga yajin aiki, tana mai jaddada cewa dokar “babu aiki, babu albashi” tana nan daram. Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, tare da ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmed, sun bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya fitar a ranar Lahadi.

Ministocin sun tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa mai ma’ana da ASUU domin warware duk wasu matsaloli da ke addabar tsarin jami’o’i a Nijeriya.

Sun bayyana cewa gwamnati ta nuna gaskiya da hakuri a tattaunawarta da kungiyar, inda ta riga ta amince da mafi yawan bukatun ASUU, ciki har da karin wani kaso na alawus kin koyarwa da inganta yanayin aiki na malamai.

.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Aragchi: HKI Ba Zata Mutunta Tsaida Wuta A Gaza Ba October 13, 2025 Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza October 13, 2025 Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh October 13, 2025 An Fara Musayar Fursinoni Tsakanun Hamas Da HKI A Safiyar Yau Litini October 13, 2025 Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal October 13, 2025 Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Bayyana October 13, 2025 Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Kula Da GIdajen Gyaran Hali A Zamfara Ta Neman Shigarda Fursunoni Tsarin Inshorar Lafiya Na NHIS
  • Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 
  • Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan
  • Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu
  • Jihar Kano Na Aikin Gyaran Cibiyoyin Lafiya Da Za Su Yi Gogayya Da Na Ƙasashen Duniya
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Cewa: Sake Gina Gaza Zai Ci Dala Biliyan 70
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Aikin Titin Abuja–Kaduna–Kano Shekara Mai Zuwa
  • Kungiyar (ASUU) Ta Sanar Da Shiga Yajin Aikin  Gargadi A Kasa Baki Daya .
  • Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang