Jihar Jigawa Za Ta Gina Tashoshin Samar Da Ruwan Sha Masu Amfani Da Hasken Rana
Published: 19th, October 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ware kimanin Naira Miliyan 400 domin gina sabbin tashoshin samar da ruwan sha na hasken rana a kananan hukumomi guda biyar na jihar.
Manajan Darakta na hukumar ruwa ta jihar, Injiniya Zayyanu Rabi’u Kazaure, ne ya bayyana hakan a Dutse.
A cewarsa, an tsara aikin ne domin a gina tashoshin a Hadejia, Ringim, Birnin Kudu, Kafin Hausa da kuma sabon rukunin gidaje na Kazaure.
Injiniya Zayyanu Rabi’u ya bayyana cewa samar da ruwan sha yana daga cikin muhimman shirye-shiryen wannan gwamnatin a jihar.
Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayanta wajen tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta ga al’umma.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
Aƙalla mutum shida ne suka jikkata bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Kangire da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa.
Ishak Ibrahim Fanini, mai taimaka wa shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Muhammad Uba, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankaliA cewarsa, an zargi makiyaya da shigar da dabbobinsu cikin gonakinsu wasu manoma.
Wannan ya haddasa faɗa tsakanin manoma da makiyayan.
Ya ƙara da cewa shugaban Ƙaramar Hukumar ya gudanar da taron sulhu tsakanin ɓangarorin biyu, inda ya gargaɗi su kan tayar da rikici a yankin.
Wannan sabon rikici ya faru makonni kaɗan bayan irin wannan ya auku a watan Oktoba, inda mutane uku suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a Ƙaramar Hukumar Birniwa.
Rikicin manoma da makiyaya ya zama babban matsala a Jigawa da sauran yankunan Arewa.
Masana sun ce wannan rikici na yawan faruwa ne saboda matsalolin muhalli, tsadar rayuwa.
Sun bayyana cewa sauyin yanayi da yaɗuwar hamada a Arewacin Sahel sun tilasta wa makiyaya da dama yin ƙaura don ciyar da dabbobnsu.
Sai dai shigarsu yankunan da ake noma a Jigawa, ya haifar da rikici saboda lalata gonaki.