Gwamnan Katsina Ya Bukaci Al’umma Su Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Kawar Da Matsalar Tsaro
Published: 18th, October 2025 GMT
Gwamna Radda ya jaddada cewa hukumomin tsaro kadai ba za su iya fada da ‘yan ta’adda ba, sai dai da gudummuwar ‘yan kasa. Ya yi kira ga ‘yan Nijeria da su zama masu sanya ido da kai rahotanni cikin gaggawa da bayar da ingantattun bayanai ga jami’an tsaro.
Ya yaba wa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu bisa inganta tsaro da maido da martabar tattalin arzikin kasar nan.
এছাড়াও পড়ুন:
Taron Malamai Ya Nemi Haɗin Kai Domin Magance Rashin Tsaro, Talauci Da Rarrabuwa A Arewa
Manyan malamai, shugabanni na addini, gargajiya da siyasa daga sassan Arewacin Najeriya sun hallara a Kaduna domin Taron Musamman na Malaman Arewa (Special Northern Ulamah Summit), wanda ya mayar da hankali kan nemo mafita ta dindindin ga matsalolin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ke addabar yankin.
Taron ya tattauna kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin malamai, amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ta dace, da kuma ƙarfafa hulɗa tsakanin shugabannin addini, gargajiya da na siyasa domin dawo da zaman lafiya da daidaito a al’umma.
Da yake jawabi, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na Uku, wanda Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya wakilta, ya kira malamai da shugabanni su haɗa kai wajen yaki da rashin tsaro, talauci da rarrabuwa. Ya gargaɗi malamai da al’umma da su guji amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ƙarya da haifar da fitina.
Sarkin Musulmi ya jaddada cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata ne kawai idan aka samu haɗin kai na gaskiya tsakanin sassa daban-daban na al’umma bisa koyarwar addinin Musulunci.
A jawabinsu na haɗin gwiwa, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi sun bayyana cewa son kai, rarrabuwa, da matsin tattalin arziki na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo rashin tsaro a Arewa. Sun ce lokaci ya yi da shugabannin addini, gargajiya da siyasa za su buɗe tattaunawa mai fa’ida tare da yin aiki tare domin kawo ƙarshen rikice-rikice da koma bayan tattalin arziki.
Haka kuma, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar na Jihar Zamfara, Sanata Shehu Buba na Jihar Bauchi, da Honourable Alhassan Ado Doguwa na Jihar Kano, sun yaba da wannan taro suna mai cewa lokaci yayi da za a ɗauki mataki na haɗin kai domin ceto yankin Arewa daga ƙalubale.
Sanata Yari ya ce rashin tsaro na ci gaba da ƙaruwa ne saboda rashin daidaito da ƙarancin damar tattalin arziki, yayin da Sanata Buba ya jaddada muhimmancin ƙarfafa matasa da aiwatar da gyare-gyaren zamantakewa bisa ka’idojin Musulunci.
Honourable Doguwa, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Majalisar Wakilai na Arewa (Northern Caucus), ya tabbatar da goyon bayan majalisa ga sakamakon taron, tare da alkawarin haɗa hannu da hukumomi da shugabanni domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a yankin.
A ƙarshen taron, mahalarta sun amince da kafa Cibiyar Jagorancin Addinin Musulunci ta Ƙasa (National Islamic Leadership Forum), domin haɗa malamai, shugabanni da masu tsara manufofi a ƙarƙashin dandalin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.
COV: Shettima Abdullahi