Saudiyya ta zaftare wa Najeriya guraban Aikin Hajji da sama da kujeru 28,000
Published: 17th, October 2025 GMT
Kasar Saudiyya ta rage yawan guraben kujerun aikin hajjin da take ware wa Najeriya daga 95,000 zuwa 66,910 daga shekarar 2026.
Aminiya ta ruwaito cewa a baya Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku tana samun guraben na 95,000 a yayin Aikin Hajjin.
’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 8 a harin kwanton ɓauna a Zamfara An ceto mutane 3 da aka yi garkuwa da kama wasu a BauchiA cewar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), wannan sauyi ya biyo bayan gazawar Najeriya wajen cika guraben da aka ware mata a hajjin shekarun 2024 da 2025.
Wata sanarwa da, Mataimakiyar Darakta a Sashen Yaɗa Labarai ta hukumar, Fatima Sanda Usara, ta sanya wa hannu, ta ce hakan na nufin za a sake fasalin yadda za a raba guraben zuwa jihohi, bisa la’akari da yawan alhazan da kowace jiha ta kai a hajjin 2025.
“Shafin Aikin Hajji na Saudiyya ya nuna cewa guraben da aka ware wa Najeriya a hajjin 2026 sun kai 66,910. Wannan na nufin cewa duk da an ware gurabe 95,000 ga Najeriya, adadin da za su iya tafiya hajji a 2026 bai wuce 66,910 ba. An ce an rage guraben ne saboda rashin cikakken amfani da su a shekarar da ta gabata,” in ji sanarwar.
Bayanin na zuwa ne bayan wani taro tsakanin NAHCON da wakilan jihohi domin tattaunawa kan farashin kujerar Aikin Hajji da wasu muhimman batutuwa.
Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Prince Anofiu Elegushi, ya ce za a sake duba rabon guraben da aka yi a baya bisa la’akari da yadda kowace jiha ta yi amfani da gurabenta a hajjin 2025.
A jawabinsa na buɗe taron, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yi kira da a haɗa kai domin tabbatar da nasarar shirya hajjin 2026.
Ya kuma jaddada buƙatar shugabannin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi su ɗauki batun binciken lafiyar alhazai da muhimmanci, duba da yadda Saudiyya ita ma ke ɗaukar lamarin da matuƙar muhimmanci.
A yayin taron, NAHCON ta ce tana ci gaba da tattaunawa da hukumomi domin rage wasu kuɗaɗe kamar na jigilar kaya, don rage yawan kuɗin da ke kan masu niyyar zuwa hajji.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Saudiyya
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Kama Mutum 105, Sun Ƙwato Ƙwayoyi Sama Da 5,000 A Jigawa
‘Yansanda sun kuma samu kuɗi Naira 92,460 da wasu abubuwan maye kamar giya da sauransu.
“Wannan samame sakon gargaɗi ne ga duk masu hannu a fataucin miyagun ƙwayoyi,” in ji SP Adam.
“Yaƙinmu da fataucin miyagun ƙwayoyi yana ci gaba, kuma muna kira ga jama’a su riƙa sanar da mu duk wani abin da suka gani na zargi.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA