An Fara Kidayar Kuri’un Zabukan Kananan Hukumomi 16 Da Aka Yi A Libya
Published: 19th, October 2025 GMT
Hukumar zaben kasar Libya ta sanar da cewa bayan da aka rufe kada kuri’u a mazabun da aka yi zaben a jiya Asabar, an fara kidayar kuri’u.
Sanarwar ta kuma tabbaatr da cewa wadanda su ka kada kuri’un sun kai kaso 68% na jumillar wadanda su ka yi rijista,kuma an gudanar da zaben ba tare da wata matsala ba.
Fira minista Abdul Hamid Debaibah wanda yake jagorantar gwamnatin da kasashen yammacin turai su ka amince da ita a birnin Tripoli, ya yi kyakkyawan yabo akan yadda zaben ya gudana.
Ya kuma kara da cewa, zaben da aka yi ya tabbatar wa da duniya cewa al’ummar Libya za su iya tafiyar da tsarin demokradiyya.
An yi zaben ne dai na kananan hukumomi bayan da aka rika dage shi a baya saboda dalilai na tsaro.
A ranar 20 ga watan nan Okto ba ne za a yi zaben a sauran yankunan da su ka rage.
Har yanzu kasar ta Libya tana da rabuwar kawuna saboda hukumomi biyu da take da su a gabashi da kuma yammacin kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Arakci: Iran Da Kasashen China Da Rasha Suna Shirin Kawo Karshen Takunkuman Turai October 19, 2025 Miliyoyin Mutanen Amurka Sun Yi Zanga-zanagr Nuna Kin Jinin Donald Trump October 19, 2025 Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi October 19, 2025 Sojojin HKI Sun Shiga Cikin Yankin Qunaidhara Na Kasar Syria October 19, 2025 Gaza: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Wuta October 19, 2025 Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila kan keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta October 19, 2025 An gudanar da zanga-zanga a sassa da dama na Amurka October 19, 2025 MDD : “Zai dauki lokaci” kafin a rage yunwa a Gaza October 19, 2025 ICC ta ki amincewa da daukaka karar Isra’ila October 19, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159 October 19, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta soke bada mafaka ga ‘yan kasashen Afirka 10
Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10.
Wannan matakin, ya zo ne bayan harin da aka kai a Washington kwanan nan, kuma ya shafi kasashe 19, da suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, a cewar wata sanarwa da Hukumar Kula da ‘Yan Kasa da Shige da Fice ta Amurka (USCIS) ta fitar.
Sauran kasashen su ne Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.
Sanarwar ta umarci ma’aikatan hukumar da su “rike duk fom din bukatar Zaman Mafaka, ba tare da la’akari da kasar da bakon yake ba, har sai an sake duba shi.”
Matakin ya shafi ‘yan kasashe 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”
Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.
Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar Ta Sanar Da Tattaunawa Da Amurka Don Shirya Sake Gina Gaza December 3, 2025 Isra’ila Ta Hana Motocin Agaji 6000 Shiga Gaza Duk Da Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta December 3, 2025 Kasar Qatar Ta Gargadi Isra’ila Game Da ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza December 3, 2025 Sharhi: HKI tana fama da karancin sojoji a dukkan rassan sojojin kasar December 2, 2025 Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufa December 2, 2025 Shugaban Kasar Najeriya Ya Nada Janar Chiristopher Musa ( Ritaya) A Matsayin Ministan Tsaro December 2, 2025 Nigeria Ta Bai Wa Dan Takarar Shugabancin Kasar Guine Bissau Mafakar Siyasa December 2, 2025 Palasdinu: Sojojin “Isra’ila” 3 Su Ka Jikkata Sanadiyyar Taka Su Da Mota December 2, 2025 Hamas Ta Caccaki Isra’ila Game Da Hana Shigar Da Kayayyakin Agaji A Yankin Gaza December 2, 2025 Ministan Tsaron Najeriya Ya Mika Takardar Ajiye Aiki Ga Shugaban Kasa Ahmad Tinubu. December 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci