Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025)
Published: 24th, September 2025 GMT
A ranar Talata, 1 ga Rabi’ul Thani 1447H, daidai da 23 ga Satumba 2025, Allah Ya yi wa Babban Mai Bayar da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh, rasuwa.
An yi jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh a ranar Talata bayan sallar La’asar, wanda Yarima Mai Jiran Gado, Muhammad bin Salman ya jagoranci manyan malamai da jami’an gwamnati da dubban mutane.
Haka kuma, an yi masa Salatul Gaib a Masallacin Ka’aba da ke Makkah da kuma Masallacin Annabi Muhammad (SAW), da kuma sauran daukacin masallatan da ke kasar bisa umarnin masarautar
UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na SaudiyyaSheikh Abdul Aziz ibn Abdullah Al-Sheikh, ya shahara wajen kyakkyawan shugabanci da tasiri a al’umma.
TasowarsaAn haifi Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh a ranar 30 ga watan Nuwamba, 1943, a birnin Makkah, daga shahararriyar zuri’ar Al ash-Sheikh — ’ya’yan gidan malamai da suka gada daga Muhammad bn Abdulwahhab.
Tun yana karami ya haddace Alqur’ani. Yana dan shekara 17 ya rasa ganinsa, kuma ya taso maraya ba tare da iyaye ba. Amma duk da wadannan kalubale, bai ja da baya ba wajen neman ilimi.
Ya yi karatun shari’a a Jami’ar Imam Muhammad bn Sa’ud da ke Riyadh, inda ya kammala a shekarar 1965. Bayan haka ya koyar a makarantu da dama ciki har da Kwalejin Shari’a da kuma Babbar Cibiyar Shari’a ta Kasa da ke Riyadh.
Sheikh Abdulaziz ya yi limancima masallatai da dama, ciki har da Masallacin Dakhnah da Masallacin Abdullah bn Abdul-Latif, sannan daga baya ya zama Babban Limami a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke Riyadh.
A shekarar 1982 kuma, aka nada shi Limami a Masallacin Namirah da ke Arafat, inda ya rika jagorantar hudubar ranar Arafat a lokacin aikin Hajji na tsawon shekaru 33 — daga 1982 zuwa 2014.
A shekarar 1987 aka nada shi mamba na Majalisar Manyan Malamai, daga nan ya zama Mataimakin Babban Mufti a 1995.
Bayan rasuwar Sheikh Abdulaziz bn Baz a 1999, Sarkin Saudiyya Fahd ya nada shi Babban Mufti na kasar Saudiyya, shugaban Majalisar Manyan Malamai, da kuma shugaban Hukumar Binciken Addini da Bayar da Fatawa.
GudummawarsaSheikh Abdulaziz daya ne daga cikin fitattun malamai da suka fi tasiri a duniyar Musulunci na shekaru fiye da 20. Fatawarsa da hudubobinsa sun shafi rayuwar jama’a a Saudiyya da sauran kasashe, inda ya jaddada muhimmancin hadin kan al’ummar Musulmi.
Ya wallafa littattafai da dama, ciki har da tarin fatawoyi da hudubobin Arafat, da kuma shahararren shirin rediyo mai suna “Nur ‘ala al-Darb.”
Duk da haka, wasu daga cikin fatawoyinsa sun jawo ce-ce-ku-ce. Ya taba sukar kungiyar Palasdinawa ta Hamas, inda ya kira ayyukanta na tashin hankali “haram kuma abin kunya ga addini.”
Haka kuma, ya ba da fatawa cewa wasan chess aikin Shaidan ne, kuma ya soki Twitter a matsayin hanyar “sharrin zamani,” kuma ya bayyana cewa Shi’a ba su cikin Musulunci.
Sai dai kuma, ya bayar da fatawa mai muhimmanci a shekarar 2005 inda ya haramta auren dole, sannan a 2018 ya mara baya ga hukuncin da ya bai wa mata damar tuki a Saudiyya.
Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh ya kasance jagora mai natsuwa, mai hikima. Dalibansa da dama sun zama malaman addini, alkalai da masu wa’azi. Hudubobinsa a filin Arafat sun zama abin sauraro ga miliyoyin Musulmai kowace shekara.
Ya rayu da tawali’u da biyayya ga shugabancin kasar, tare da dagewa wajen kare al’adu da koyarwar Musulunci.
Mutuwarsa ta bar babban gibi a Saudiyya da dukkan al’ummar Musulmi, amma gado da koyarwarsa za su ci gaba da zama haske ga al’umma.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp