Amurka Ta Ce; Harin Isra’ila Kan Birnin Doha Ba Zai Shafi Kawancenta Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ba
Published: 14th, September 2025 GMT
Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza.
Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya haifar da zaman dar-dar na wucin gadi, amma hakan bai canja yanayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba.
Ya ce makasudin ziyarar tasa ita ce fayyace dabarun Isra’ila, inda ya kara da cewa tattaunawa da Isra’ila ya zama dole domin fahimtar tsare-tsare a nan gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tsohon Kwamandan IRGC Ya Ce Boma-Boman HKI Na Zuwa Kanku Idan Kunki Samar da Kawance September 14, 2025 HKI Tana Ci Gaba Da Rusa Dogayen Gine-Gine A Gaza A September 14, 2025 Dubban Mutanen New Zealanda Sun Fito Jerin Gwanon Goyon Bayan Falasdinawa September 14, 2025 Velayati: Taron Malaman Yahudu A Azerbaijan Tsokana Ce Ga Musulmi Shia September 14, 2025 Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Wajen Kawo Karshen Rashin Hankalin Isra’ila. September 13, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Masu Neman Agaji 4 Tare Da Jikkata Da Dama A Gaza. September 13, 2025 Kasar Masar Ta Gano Makircin Isra’ila Na Kashe Shuwagabannin Hamas A Kasar Ta September 13, 2025 Alakar Iran Da Tunusiya Ta Nuna Aniyar Iran Ta Alaka Da Kasashen Musulmi. September 13, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Goyon Bayan Kafa Kasar Falasdinu September 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce: Akwai Yiwuwar Sake Tattaunawa Da Jami’ar Tarayyar Turai September 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Duk Wani Kutse Na Isra’ila A Kudancin Kasar
Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.
A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”
Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.
Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci