Aminiya:
2025-10-18@10:48:40 GMT

Yadda ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4

Published: 18th, October 2025 GMT

Bayanai sun nuna ma’aurata 136 sun rasa rayukansu a sakamakon rikici a tsakaninsu a cikin shekaru huɗu da suka gabata a sassan Najeriya.

Alƙaluman da muka tattara daga rahotannin manyan jaridun Najeriya sun nuna yanayin rikicin ma’aurata a ɗauƙacin shiyyoyin shida da ke faɗin Najeriya.

Rahotannin sun nuna matsalolin da suke haifar da hakan a tsakanin ma’aurata da ake zaton zamannsu zai kasance mutu-ka-raba, sun haɗa da zargin cin amanar aure, rikicin abinci, rikici kan waya da sauransu.

Wannan al’amari ya rutsa da mata da maza, masu matsayi daban-daban daga shekarar 2021 zuwa 2025, kuma da alamar ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka Dantawaye ya zama sabon kwamishinan ’yan sandan Abuja

Alƙaluman sun nuna matan aure ne waɗanda suka fi rasa rayukansu a irin wannan yanayi, inda aka kashe mata 96 cikin 136, wanda kusan ninki ukun adadin mazaje 39 da aka kashe.

Akwai kuma wasu miji da mata da suka yi mutuwar, dai wata amaryar da aka kashe ana daf da ɗaurin aurenta.

Ina matsalar ta fi muni?

Bayanan da muka tattara n ma’aurata 134 da aka kashe a Najeriya daga 2011 zuwa 2015 sun nuna matsalar ta fi muni a Jihar Legas, inda aka kashe mutum 17, dukkansu mata in bada mutum ɗaya, wanda ke nuna yadda abin ya fi ritsawa da mata.

A matsayi na biyu wajen munin matsalar akwai jihohi uku — Adamawa da Edo da Ogu — waɗanda a kowannenau aka kashe mutane 10.

Da haka Jihar Adamawa ta zama inda matsalar ta fi muni a yankin Arewa maso Gabas da ma ɗauƙacin Arewa, kamar yadda Legas — wadda Ogun ke bi mata — ta yi fintinkau a Kudu maso Yamma, ɗauƙacin Shiyyar Kudu da ma faɗin Najeriya.

A Shiyyar Kudu maso Kudu kuma abin ya fi muni a Jihar Edo, Ind aka rasa rayuka 10 a tsawon shekaru huɗu da suka gabata. Musabbabin kisan ma’aurata Binciken ya lura akwai kamanceceniya a dalilan kashe-kashe a tsakanin ma’aurata. Waɗannan dalilai, musamman a jihohin da abin ya fi muni, sun haɗa da zafin kishi da matsin tattalin arziki da kuma tashin hankali.

Masu ɗaukar hankali daga cikin abubuwan da suka faru a Legas sun haɗa da yadda wani magidanci ya cinna wa matarsa wuta, da wani wanda ya kashe matarsa saboda ta ƙi yin girki, sai ta ukun da aka kashe kan ƙin biyan bashi. Akwai kuma wadda mijinta ya cizge iskar Oksijin da take shaƙar numfashi da shi a gadon asibiti.

A Jihar Adamawa, inda abin ya fi muni a Arewa, manyan dalilan da aka gano su ne rikici tsakanin ma’aurata. Daga cikin akwai wani magidanci da aya kashe matarsa saboda ta ƙi kwanciyar aure da shi, da wata wadda mijinta ya kashe ta saboda ta zarge da cin amanar aure. Akwai kuma wadda mijinta ya kashe ta saboda ta ɗauki wayarsa.

Waɗannan abubuwan sun nuna yanayin raunin alaƙa tsakanin ma’aurata inda wani lokaci abin da bai kai ya kawo ba yake rikiɗewa zuwa tashin hankali a tsakaninsu.

A Jihar Edo, inda abin ya fi muna Kudu maso Kudu, dalilan wannan ɗanyen aiki sun haɗa da tashin hankali, rashin kwanciyar aure da rikicin kuɗi — wani abin mamaki shi ne yadda wani ya kashe matarsa saboda “ta ƙi ranta mishi N2,000.”

A Jihar Ogun, inda nan ma aka kashe mutum 10, dalilan sun haɗa da cin amanar aure da kuma rikici kan dukiyar iyali.

Sauran jihohi da aka fi samun matsalar su haɗa da Anambra (9 cases), Delta (7) da Ondo (7) — dukkanau a Shiyyar Kudu, a birane da ya yankunan karkara.

Duk da cewa alƙaluman yankin Arewa ba su da yawa sosai, masu sharhi sun bayyana cewa ba lallai ne alƙaluman sun nuna haƙuƙanin abin da ke a zahiri ba, saboda yawanci a Arewa iyalai kan sasanta rikici a tsakaninsu ba tare da kai rahoto ga ’yan sanda ko ’yan jarida ba. Ra’ayin Malami

Rabaran Amos (ba sunansa na gaske ba) daga Cocin Anglican St Matthias, Ushafa, ya bayyana cewa waɗannan kashe-kashen ba kwatsam suka faru ba haka kawai, illa sakamakon lalacewar dangantaka na tsawon lokaci.

“Kisan ma’aurata ba ya faruwa da gaggawa. A cikin kowanne tashin hankali akwai tarihin bacin rai, riƙo, girman kai da watsi,” in ji shi.

Ya ce rashin iya magana da fahimta na daga cikin manyan dalilan rikici. Ma’aurata da dama ba sa tattaunawa don fahimtar juna, sai don yin rinjaye.

“Wasu ma’aurata na ɗaukar gardama a matsayin gasa. Idan fushi ya ƙaru, zuciya ta ƙi yafiya, sai tashin hankali ya biyo baya.”

Rabaran Amos ya danganta matsin tattalin arziki da ƙaruwar rikici a gidajen aure. Ya ce Rashin aiki da tsadar rayuwa na rage haƙuri da kwanciyar hankali.

“Talauci ba ya haddasa kisa kai tsaye, amma yana ƙara tsanani ga duk wata matsala.”

Ya ce rashin amana da zargin zina na rushe dangantaka, inda gida ke iya biyowa baya. Kishi, fushi da giya na haddasa kisa.

Ya ƙara da cewa wasu maza na ɗaukar dukan mata a matsayin alamar iko.

“Wasu maza na ganin cewa duka alamar shugabanci ne; wasu mata kuma na mayar da martani da ƙin yarda. Idan ƙauna ta koma gasa, an manta da manufar aure — zama tare da fahimta.”

Ya ja hankalin ma’aurata da su nemi taimako da wuri: “Shiru a yanayin tashin hankali ba tsoron Allah ba ne. Duk wani kisa yana farawa da sakana zuciya. Idan ba a tumɓuke ta ba, sai ta girma ta zama masifa. Dole ne mu gina gida da yafiya, haƙuri, addu’a da girmama juna,”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Cin amanar aure Ma aurata tsakanin ma aurata da abin ya fi sun haɗa da

এছাড়াও পড়ুন:

Kaso 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF

Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya bayyana cewa kashi 16 cikin 100 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu mai tsafta a gidajensu.

Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Chisom Adimorah ce, ta bayyana haka a ranar Laraba yayin bikin Ranar Wanke Hannu ta Duniya ta 2025, wanda Ma’aikatar Ruwa da Tsaftar Muhalli ta Tarayya ta shirya.

DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose

Adimorah, ta nuna damuwarta kan wannan matsala, inda ta ce duk mutane biyar cikin shida a Najeriya ba su da waje  da za su iya wanke hannunsu yadda ya kamata.

Ta yi kira ga gwamnati, ƙungiyoyi, kamfanoni da kuma ’yan ƙasa su haɗa kai wajen inganta tsaftar hannu a ƙasar.

Ta kuma tabbatar da cewa UNICEF za ta ci gaba da taimaka wa Najeriya wajen inganta manufofin tsaftace muhalli domin su dace da sabbin ƙa’idojin WHO da UNICEF kan tsaftar hannu.

Ministan Ruwa da Tsaftar Muhalli, Injiniya Joseph Utsev, ya bayyana muhimmancin wanke hannu wajen kare lafiyar jama’a, inda ya ce “wanke hannu na ceton rai tare da kariya daga barazana.”

Utsev, ya ƙara da cewa ‘Taswirar Najeriya ta Tsaftar Hannu’ wadda aka ƙaddamar a shekarar 2022, ita ce har yanzu ke jagorantar ƙoƙarin wayar da kan jama’a kan wanke hannu a faɗin ƙasar nan.

Ya jaddada cewa dole ne a fara koyar da wanke hannu tun daga makarantar firamare domin yara su saba da wannan ɗabi’a tun suna ƙanana.

A nasa jawabin, Aghogho Gbetsere, wanda ya wakilci Ministan Muhalli, ya shawarci ’yan Najeriya su riƙa wanke hannunsu a kai a kai, inda ya ce hakan na iya rage hatsarin kamuwa da cututtukan gudawa da kashi 50 da kuma cututtukan da suka shafi numfashi da kashi 25.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aurata 136 sun kashe juna a shekara 4
  • Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka
  • Akwai Bukatar Al’umma Ta San Aikin Da Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu (TETFUND) Ya Yi  – Masari
  • Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Za Ta Kafa Dokar Wuraren Tsaro A Makarantu
  • Ranar Abinci Ta Duniya: NAWIA Ta Tallafawa Mata 114  Da Kayan Aikin Gona A Zamfara
  • Kashi 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF
  • Kaso 16 na ’yan Najeriya ne kawai ke da wajen wanke hannu — UNICEF
  • An Kashe Mutum 13 A Wasu Sabbin Hare-Hare A Ƙauyukan Filato
  • 2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa